← Book details Maimoon Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 23 OF 190

Sashe 23

Maimoon Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Rannan muna a gaban chemistry lab muna duba past questions and answers na WAEC sai muka hango Ibrahim da wasu mata su biyu a gaban staff room, Hasiya ce ta taba ni tace "kinga mutumin ki can, ko suwa ya samu kuma" ina dubawa naga mata ne su biyu da kaya a hannun daya, dayar daga gani babbar macece dayar kuma budurwa, budurwar da hijab matar kuma da babban mayafi, sun jima a tsaye suna magana sai naga ya karbi kayan hannun budurwar ya wuce gaba suna binsa a baya suka tafi staff quarters. Har dare ban kuma ganinsa ba kuma ina ta tunanin ko su waye wadan nan? Washe gari da safe sai gashi yazo yace min inzo, muna fita waje sai yace "there is someone here that wants to see you" gaba na ya fadi nace "who?" Yace "my mother" nan da nan naji wani tashin hankali yazo min, he wants me to meet his mother, this is serious. To ni yanzu da wacce fuskar zan je mata? Kuma me zance mata? Nace masa "Ibrahim am sorry, I can't" ya bata fuska yace "why can't you?" Nace "tsoro nake ji" dariya yayi yace "tsoron me kuma? Bata cin mutane, besides tare zamu je, just ku gaisa shikenan" na kalli kayan jikina, uniform ne a wanke a goge, hijab dina ya rufe har bom2 dina, fuskata babu kwalliya, dama ba kwalliyar nake yi ba. Na sake kallonsa har yanzu da dariya a fuskarsa. Yace "you look great, let's go" yana fadin haka ya shige gaba, na bishi a baya kamar wadda kwai ya fashewa a ciki. Direct visitors room muka je, ya dan tsaya yana kallona yace "are u ready" na girgiza kaina alamar no, yayi dariya kawai ya bude kofar da sallama. Nima nayi sallama na shiga. Su biyu ne kamar jiya da babba da karama. Ina kallon babbar nasan ita ta haifi Ibrahim sai dai bata kaishi tsaho ba, karamar kuma sam basa kama dan ta fishi hasken fata sosai, dan da kadan zan nuna mata fari, sai dai ita fuskarta duk kuraje yayin da tawa take tas. Kana ganin maman su Ibrahim kaga typical yaroba woman. Da daurin zanin ta akan riga, da goggoron akan ta. Ibrahim ya zauna a kusa da ita ni kuma na durkusa daga nesa a kasa na gaisheta da turanci. Ta amsa min amma daga gani turancin na isar ta yayi ba. A raina nace oho dai ni ba iya yarabanci nayi ba sai dai mu tsaya daga gaisuwar. Na gaishe da dayar tunda daga ganinta nasan ta girme ni. Ta amsa tana dariya, na dago kai sai naga Ibrahim ne yake hararar ta, ya wani dora kafa daya akan daya. Maman su kuwa idonta yana kaina. Sai da muka dan jima a haka sannan Ibrahim yace "Maimunatu this is my mother, and that girl over there is my sister" da saurin ta tace "his step sister" na dago kai na kalleta sai naga idonta a kansa, bansan dalili ba sai naji hankali na bai kwanta ba da kallon da take masa. Mamansu naji ta fara magana da gurbataccen turancinta "kullum na kira Ibrahim zancen sa Maimunatu tace kaza maimunatu tayi kaza, inna yi masa complain akan baya zuwa mana weekend sai yace ai muna karatu da Maimunatu sun kusa fara exams, kullum zancen kenan, shine nace bara inzo inga maimunatun nan dai da ido na" naja hijab dina na rufe fuskata, inaji tana masa magana da yarabanci, naji dai tace fulani a ciki, sai naji yace "mu fa yaroba ba'a wani kunyar suruka, in zaki bude ido ki bude, dan duk randa kika haihu ita zata yi miki wanka" na kara dunkule wa a guri daya a raina ina cewa kai Ibrahim mai ya kawo zancen haihuwa kuma? Gaba daya suka yi dariya. 'Yar budurwar ce tayi magana tace "let me introduce myself properly, ni step sister dinsa ce, ma'ana babana ne mijin mamansa, sunana Efisowa amma zaki iya kira na Efi, nazo in taya shi assessing sabida nasan ba iya zabe yayi ba. Dama tunda naji mama tace Fulani nace sai nazo nagani da kaina, gashi kuma naga kinyi kankanta da yawa" Ibrahim yace mata "shut off" sannan yayi mata magana da yarabanci itama ta mayar masa, sai maman tayi musu magana duk sukayi shiru. A hankali maman tace min "ina parents dinki?" Nace mata "suna cikin garin abuja" tace "ku 'yan Abuja ne" nace "'yan jigawa ne mu" kawai sai naji matar tayi min, yadda take magana a hankali irin maganar Ibrahim. Efi ce dai hankali na bai kwanta da ita ba, duk na damu ganin ta kasa dauke idonta daga kan Ibrahim. Ibrahim ne yace zai mayar dani class dan muna karatu, Efi ta sake yin magana da yarabanci shi kuma ya sake ce mata shut off maman tayi tsaki tana kallon efi alamar warning. Tunda muka fito bamu yi magana ba sai da muka dan yi nisa sannan yace "how do you like my mother" nace "she is OK, you look like her but taller" yace "no, she always say da baban mu nake kama" Har nayi tunanin kar in tambayeshi akan efi amma sai zuciya ta ta kasa jurewa, nace "Your sister doesn't like me" yayi dariya yace "yours doesn't like me either" nima nayi dariya sannan nace "but this is different, i feel like there is some tension between you two" yayi shiru bai bani amsa ba, wannan ya tabbatar min da zargina. Nan take naji raina yana kuna. Sai da muka kusa zuwa class sannan yace "koma menene da a tsakanina da efi is over tun tuni, abinda yake tsakanin mu sam bashi da dangantaka da efi. A mincewar mama da baba kawai nake bukata. Please Maimunatu don't screw this thing off. Mama tazo takanas saboda ta ganki, please show her your best behavior yadda in taje zata bawa baba labari shima zai yaba dake, please don't let Efi get in your head, that is exactly what she wants" muna zuwa gaban class din mu nayi shigewa ta ba tare da nace masa komai ba. Har na zauna yana tsaye a gaban class din ya rungume hannayensa fuskarsa da alamar damuwa.

Bayan na zauna sai nayi tunanin ban kyauta wa Ibrahim ba, kuma gaskiya ya fada cewa this is our chance, ya kamata inyi kokari inyi probing to his mother cewa I am good enough, inna bari kishin Efi ya shiga raina tun yanzu to ina da problem.

Anan zan tsaya inja hankalin 'yammata har ma da matan auren, idan mace ta nuna tana son mijin ki, musamman idan shi mijin ko saurayin baya son ta, don't make an enemy out of her, ki jata a jikin ki kiyi mata kirki sosai, make sure duk sanda saurayin ko mijin yake around kun nuna mata irin soyayyar da kuke yiwa junan ku, ita da kanta zata ji kunya ta ja baya, amma idan kika kama fishi da fada kamar kina tura shi gurinta ne. Ke kuma budurwa da kike neman miji, kar kiga wata da nata kiyi sha'awa kice lallai sai kin raba. In dai har soyayyar tsakani da Allah yake yi mata to ba zasu rabu bafa.

Washe gari da yamma muna kofar library da Amira da wasu kawayen mu sai ga Ibrahim sun taho gurin mu shida Efi, tun daga nesa nake kallon yadda take ta shishshige masa, gaba daya kowa ya tsaya yana kallon su har suka kara so. Kallo daya nayi masa nasan ransa a bace yake. Suna zuwa yayi introducing dinta generally, sannan yace "she said she wants to look around the school" nayi sauri nace "she is welcome" tare da miko mata hannu, ta kalle ni sannan ta kalli Ibrahim kamar me neman izni shi kuma ya dauke kansa ya juya ya tafi, tayi masa magana da yarabanci bai amsa mata ba, ya saka hannayensa a aljihun wandon sa yayi tafiyarsa. Yana tafiya na fara yi mata hira, nayi mata introducing duk friends dina da suke gurin. Amira ko kallon ta bata yi ba. Daga nan nace tazo in showing her around, tun daga classes, labs, kitchen, dining hall duk sai da na kaita, sannan na kaita hostel.
Hafsat tana kwance muka shiga, ta bimu da kallo, sannan tace min da fulatanci "wannan kuma a ina kika samota?" Na amsa mata da turanci "she is Ibrahim's step sister" sannan na kalli Efi nace "this is my Sister, Hafsat" Efi tace "oh my God she is so beautiful, nice to meet you" ta mika wa Hafsat hannu, kirikiri Hafsat ta ki bata hannu tace da fulatanci "ni bazan taba hannunki ba, kurwata kur" nayi dariya, Efi tace "what did she said?" Nace mata cewa tayi "ai kin fita kyau ma" nan da nan ta washe baki tace "thank u" Hafsat ta harare ni. Nan da nan Efi ta fara santin dakin mu, wai wannan ai ko a gida sai haka, ita in tana nan ai ba zata so ayi hutu bama. Nan da nan na chika mata gabanta da kayan chiye2 muka zauna muka yi ta hira, tana bani labarin gidan su. Amma ni bance mata komai ba akan namu gidan. Har akayi sallar magrib muna tare can sai Ibrahim ya kira ta yace ta fito su koma gida, haka kawai sai na samu kaina da jin babu dadi saboda ya kira ta a waya. Na dauko wani set din toiletries na mu na dove na saka mata a keda na bata. Tayi ta mamaki wai ina student har nake kyautar kaya?

Washe gari Ibrahim yace min zasu tafi, na hado sweets da biscuits madu yawa a leda na boye a hijab dina saboda 'yan sa ido, yazo ya kira ni muyi sallama da mama. Ina shiga na gaishe ta, ta amsa min da sakakkiyar fuska sosai tayi min fada akan karatu, naji dadi har raina, na dauko leda ta na bata nace a kaiwa Abdullahi da Abdulrahman, kananan kannen Ibrahim. Taki karba na ajiye mata a gabanta na tafi.
Chapter 23 · 0% Book details