← Book details Maimoon Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 139 OF 190

Sashe 139

Maimoon Part 1 Complete Hausa Novel · about 3 min read

tana kalle kalle, gabansa yaji ya fadi, she looks so much like Moon, but she isn't Moon. Ya danna horn ta juyo ta kalli inda yake, tana zuwa dai dai window dinsa ta bata rai ganin shine, ya rike kugu tace "what do you want?" Exactly abinda ya gaya mata a office dinsa, bai bata amsa ba ya turo ko fa ya fito, ya jingina da motar ya rungume hannayensa a kirjinsa ya zu ba mata ido. Sai kuma ta kasa kallonsa ta juya tana kallon gefe, sai da ya gama tsare ta da ido sannan yace "na horu haka, ayi min afuwa, nayi kuskure ba zan sake ba" ta juyo tana kallonsa tace "me kayi?" Yace "laifuffuka na ai suna da yawa, na farko I used you to get into Moon's home, na biyu I ignored your calls, na uku I treated you badly a office dina" Ta dan so tayi murmushi amma ta maze tace "shine abinda ya kawo ka? Ai na dauka kazo kaji sakon da Moon ta bani in gaya maka ne. To tunda ka gama fadar abinda zaka fada ni bara in koma gida" yayi sauri ya tari gabanta yace "to ai baki ce kin hakura ba" ta murguda masa baki ta sake yin gaba, sai kuma ta juyo "au ba zaka tambaye ni sakon Moon din ba" ya girgiza kansa yace "just tell me if she is OK" tace "she is more than OK. Amarya ce fa ko ka manta" daga haka tayi komawar ta gida. Ya danyi murmushi yana jin dadi a ransa, at least maimunatu is OK, she loves mijin da ta aura, abinda ya faru ranar ya tabbatar masa da haka, abinda ba shi da tabbaci a kai shine idan shi mijin nata yana son ta kamar yadda take son sa. Ya koma motar sa ya tayar ya koma bakin gate, yana zuwa baba habu ya kawo masa wata 'ya karamar envelope, yace "ka ganta kuwa na gani" ya karba yayi godiya ya saka a aljihun sa ya tafi. Bai bude letter din ba sai da yaje gida ya gama duk abinda zaiyi yayi shirin kwanciya sannan ya dauko takardar ya bude; Dearest Ibrahim I may not be around when you come back. Please give the man who gave you this letter your new phone number and I will call you. I miss you Maimunatu. Ya ajiye takardar ya dafe kansa da hannayensa biyu yana jin garin yana juya masa. Ya tuna yawan zurga zurgar da ya ringa yi zuwa unguwar su maimunatu, amma Allah bai taba bashi ikon karasawa gurin mai gadin su ba, all this while wannan wasikar tana ajjiye, da ace ya karasa gurin mai gadin ya karbi wasikar ya karanta da duk wata karya ta Amira ta kare. Ba Amira ce ta raba shi da Maimunatu ba, Allah ne ya raba su, saboda ya riga ya kaddara cewa babu aure a tsakanin su. Ya jingina kansa a jikin frame din gadon for some time, sannan ya mike zaune ya dauko wayarsa yayi dialing number din Amina, ga mamakin sa sai yaji ta dauka, bata gaishe shi ba tace "what do you want?" Yace "har zan kwanta na tina baki ce kin yafe min ba har yanzu" tace "to sai na fada? Tunda kazo gidan mu kaga na fito ai na hakuran kenan ko" yace "thank you" tace "good night then" yace "wait. In really kin hakura can we be friends then?" Ta danyi shiru sannan tace a hankali "am not Moon" yace "I know" tace "ok, friends then" yace "to kiyi min dariya mana inji sai in yarda mun zama friends din" tace "I don't have dimples" yace "I know".
Chapter 139 · 0% Book details