Sashe 169
Maimoon Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
akan cikin yana yiwa ummee da sultan bayanin komai, sultan sai washe baki yake yi. Sun fi minti talatin suna kallo, sultan wai bai gaji da gani ba, sai da doctor yace "kai da za'a haifa maka a baka a hannunka ba sai kayi ta kalla ba?" Ya rubuta result ya bamu, ya rubuta wani ya bawa ummee. Alhamdulillah komai normal yake tafiya. Daga nan muka koma gida. Washegari doctor Ahmad ya kira sultan wai yana son muje gidan sa mu wuni a can, yana son ya hada ni da matar sa. Matarsa mai kirki sosai, Firdausi, zamuyi kusan sa'anni ni da ita, sai dai ita har tayi 'ya'ya biyu, Amra da Afra, su sultan suka fita suka barmu tare, tare muka hada lunch tana ta yaba methods of cooking dina, bata san cewa da zero nake ba daga baya na koya, muna gama shirya table su sultan suka dawo muka yi lunch tare, nace da doctor Ahmad, "da fatan dai baka gaya masa ba" yace "ai nayi wa ummee alkawari, duk wanda yake so ya sani sai dai ya tambaye ta" nan muka zauna hira akan banbancin al'adun mu da nasu, da yadda zamani yake chanza both al'adun mu da nasu. Ummee ce ta kira ni a waya tace mu dawo gida haka nan, na duba agogo naga 4:30, nayi mamaki cewa da tayi mu dawo da wuri bayan hira tana dadi, Ahmad yace bara su biyo mu kawai dama sun jima basu je gidan ummee sun gaishe ta ba. Muna yin packing na lura da motoci da yawa a gidan, ni dai ina mamaki na kalli sultan ya daga min kafada alamar shima bai sani ba, a palon farko muka ga al rataye balloons pink and blue, a kofar shiga palo na biyu an yi decoration an rubuta 'Welcome to the Gender Reveal Party' mamaki ne ya kamamu, dama Ummee party ta shirya mana? Muna shiga kuwa aka dau tafi da sowa, da 'yan'uwan sultan nan kusan duk wanda yake gari yazo, na kalli Ahmad naga yana mana dariya, wato dashi aka hada baki shi yasa ya gayyace mu gidan sa. Ni dai ba zan iya cewa ga abinda ya faru ba, they are all talking at the same time kuma mostly larabci suke yi, ni dai naga an jamu ni da sultan gefe, aka hada hannayen mu aka daure da pink and blue ribbons, sai kuma naga an turo wani table da katon cake akai, fari tas cake din kamar snow, aka kawo gabanmu aka ajiye, aka kawo mana 'yar karamar wuka fara aka saka mana a hannayen da aka daure, ina kallon zahra tana recording da wayarta, suka fara chanting 'cut the cake, cut the cake' sultan ya kalleni yace "are you ready?" Na juya na kalli ummee, ta gyada min kai, na kalli sultan nace "yes" nan aka dauki tafi da sowa, suna chanting "pink means girl, blue means boy" wato in muka yanka cikin cake din muka ga pink to girl ce, in kuma muka ga blue to boy ne, na kalli sultan naga sai zuba murmushi yake, dadi ya ishe shi, gani ga ummeensa ga 'yan uwansa duka kuma muna sonsa, ga kuma cikin jikina, dan haka bai damu ba ko mace ce ko namiji ba, nima sai naji ban damu ba, fatana Allah ya bani mai albarka. Muka dauki wukar a tare muka yanka cake din, tun kafin mu karasa yanka wa na ga blue, muna gama yankawa kuma aka dauki ihun "it is a boy" ni dai dariya kawai nake yi, na kalli sultan naga shima dariyar yake yi, ya kalle ni yace "Congratulations My Love, you won" yayi kissing dina a cheeks sannan yayi min a goshi, sai kuma ya rungume ni a jikinsa ya rada min "I Love You" a cikin kunne na, nima nace masa "I love you more". Nigeria Ibrahim; Satinsa biyu a Ibadan ya dawo abuja, a zaman da yayi a ibadan ya kuma kulla dangantakarsa da ubangiji kuma ya kara kulla wa da mama da sauran 'yan uwansa, dan takanas ya fita yawon zumunci, kusan duk 'yan uwansa da suke ibadan, barim mama da baba da kuma babansa mahaifi babu gurin wadanda baije ba, kuma duk inda yaje sai ya kai musu goma ta arziki. Yana dawowa Abuja kuwa ya karawa employees dinsa albashi, wadanda ya kora ya kira su suka dawo bakin aikin su. Shi kansa yaji chanji a jikinsa, dan yanzu fresh yake jin kansa, zuciyarsa da take a kuntace a da yanzu tas yake jinta. Ya nemi masu aikin construction suka zo sukayi masa renovating gidansa aka kara dakuna, aka fitar wa da mama part dinta, da nashi part din shi da Amina, daga baya kuma akayi dan karamin BQ saboda kannensa maza. Har furnitures sai da ya zuba da komai sannan ya koma ibadan, nan fa mama ta saka rigima ita ba zata koma gidan sa ba, sai da ya hada da gaya wa 'yan'uwanta da yasan tana jin maganar su sannan ta yarda ta biyo shi, ita da maimunatu da kannen Ibrahim maza su biyo, matan dama duk sunyi aure suna gidajen mazajen su, mazan kuma an gama secondary school amma babu halin shiga jami'a, 'yar collage din ma ta gagare su. Ai kuwa suna ganin gidan da zasu zauna yanzu sai murna, wahala ta kare dadi yazo kuma, suna zuwa ya nema musu admission a university of Abuja, Allah ya so lokacin sabon dauka ne kuma yana da hanya tunda yana da kudi, dan haka basu samu matsala ba suka samu, maimunatu kuma ya nema mata makaranta me kyau sosai ya saka ta, yayi hiring 'yan aiki saboda kula da gida, baya son mama ta ringa aiki da kanta, amma duk da haka tace a bar mata girki zata ke yi musu da kanta tunda bata saba da zaman banza ba. Ya saka mata DSTV a dakinta saboda in babu kowa ta ringa debe mata kewa. Maimunatu kuwa a part dinsa ya ware mata daki, ya cika mata shi da dukiya duk abinda yasan little girl zata bukata sai da ya saka mata, amma ita duk wannan bai dame ta ba, ita babban burinta shine ta ganshi tare da ita, dan sam kin zama tayi a dakinta sai nashi dakin ta dawo, tare suke kwana ta makalkale shi kamar zai gudu, har ransa yake jin tausayinta, bata san mahaifiyarta ba shi kuma mahaifin nata yayi watsi da ita yana chasing dead dreams dinsa, rannan yana shiryata zai kaita makaranta tace "Daddy please don't take us back to ibadan" ya durkusa a gabanta yana shafa gefen fuskarta yace "I promise you I won't". Dadin gidan yake ji sosai yanzu, amma da har baya so ya dawo gida saboda zaman kadaicin da yake ciki, yanzu kuwa kullum cikin nishadi yake da dariya, bashi da wani sauran problem sai Amina. Sam Amina taki kulashi, tun ranar nan har yau taki daukan wayarsa, yaje gidan yafi sau a kirga amma taku fitowa, direct take cewa a gaya masa ba zata zo ba, yayi messages din ban hakurin har kalamansa sun kare, kullum yana ganinta online a WhatsApp amma maganar duniyar nan in yayi mata ba zata bashi amsa ba, kuma tana karantawa yana gani. Gashi kuma wani irin sabon sonta ne yake kara shigar sa, ita kuma kamar da gayya kullum sai ta chanza DP dinta, sai yayi saving yayi ta kallo, sam yanzu ya daina kanin fuskar moon a fuskarta, har mamaki yake yi ya akayi da yake ganin suna kama, they are totally different, kowacce is special in her own way. Daga baya ya yanke shawarar zai biyo mata ta sama, dan haka yaje gidan ya binciki ranar da zai samu Daddy, ranar kuwa yaje ya aika akayi masa sallama dashi, Daddy ya gane shi dan haka yayi masa iso har palon bakinsa yana tambayarsa ya saukin jiki, Ibrahim kan har ya manta ma da yayi wata jinya, shi yanzu jinyar zuciyarsa ce a gabansa. Nan ya yiwa Daddy bayanin abinda yake tafe dashi, Daddy yayi murna sosai amma kuma sai ya tambashi ko Aminan ce tace masa yazo? Nan fa Ibrahim ya fara shafa kai, daddy yace kar ya damu zai yi magana da Aminar yaji menene amsarta, duk abinda ake ciki zai saka walid ya kira shi a waya ya gaya masa. Ibrahim ya riga yasan amsar da Amina zata bayar dan haka sanda walid ya kira shi ya gaya masa abinda tace bai yi mamaki ba, amma Daddy yace a gaya masa ya cigaba da nemanta, inta chanza ra'ayi shikenan, in bata chanza ba kuma sai dai yayi hakuri dan ba za'a yi mata dole ba. Nan Ibrahim ya kara kaimi gurin rarrashi da ba da hakuri amma shiru kamar an shuka dusa, kuma har a zuciyarsa bai taba tunanin ya hakura ba saboda yana ji a ransa cewa itace matarsa. Ranar wata Friday kawai yana zaune a office sai yaga message, har sai da ya mitstsika idonsa dan yana ganin kamar yaudarar sa idon yake yi, Amina, ya bude ya fara karantawa "if you can, come over tomorrow, someone wants to meet you" da sauri yayi reply, "of cause I can, And I really hope that someone is you". Saturday yana yin sallar la'asar ya cewa mama zai dan fita ya dawo, sai gidan su Amina, suka gaisa da baba habu dan yanzu sun fara sabawa dashi, ya shiga yayi packing ya kira ta a waya, bata dauka ba har ta katse, sai kuma gata ta fito, ta kira wani yaron gidan tayi masa magana sannan ta koma ciki, yaron yazo yayi masa iso zuwa palon su yaya Walid, ya shiga ya zauna yana karewa haduwar gurin kallo, sam yanzu dukiyar gidan bata tsorata shi saboda yasan karamcin jama'ar gidan. Yaji motsi a bakin kofa, yayi sauti ya juya, Amina ce a tsaye da dogon hijab a jikinta tayi sallama ta karaso ciki, murna kamar ta kashe Ibrahim, gani yake kamar bai taba ganin macen da hijab yayi wa kyau irin amina ba. Ya mike yana amsa sallamar ta, sai kuma yaji wata sallamar daban, ya kalli bakin kofar, nan take annurin fuskarsa ya kau, ko a mafarki baya fatan ganin wannan fuskar, me take yi anan,