Sashe 89
Maimoon Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
'Yan # teamibrahim ina jin duk abinda ake yi muku, believe me, i will surely reward your loyalty. Bature yace "he who laugh last....... Washegari da sassafe Sultan ya kira ni yace min ya tafi office, yana da meeting very early, dan haka nima ban tashi da wuri ba, ina jin Mommy kusan shigowarta uku tana dubani, sai kusan karfe 12 na tashi, shima kuma yunwa ce ta tashe ni, nayi wanka na shirya cikin wasu riga da skirt english wears tunda duk kayana sunyi min yawa yanzu, nayi packing gashina a tsakiyar kai na sauko kasa, a kitchen na samu su Mommy already suna aikin abincin lunch, na gaishe da Mommy ta amsa tana kallon kayan da na saka, na jawo kujera na zauna nace "Ma'u ki kawo min taimako, yunwa na ke ji" da sauri Asma'u ta ajiye aikin da take yi ta fara hado min tea, na karba na fara sha sannan ta zubo min farfesun naman ragon da suka gama hadawa ta hado min da bread, na karba ina ci ina santi, Mommy tace "aikin kenan, amma in akace kiyi garki ba zaki yi ba sai dai a girka ciki, ni ban taba ganin macen da bata son girki ba sai ke Moon" Furaira ta karba "kuma gashi gwanin nata gwanin abinci ne ba" a tare muka watsa mata harara ni da Mommy, tayi sauri taja bakinta tayi shiru, can Mommy tace "ke furaira ya akayi kikasan saurayinta ne?" Furaira tace "nima Mommy wallahi a gurin 'yan waje nake ji, shi yake gaya musu" a raina nace "zai aikata" Asma'u tace "kar ki damu mai sunan daada, duk sanda akayi bikin ki gidan ki zan koma inyi ta dafa miki abinci ke da mijin ki" nan itama ta karbi nata rabon hararar daga Mommy" sai da na gama cin abinci na sannan Mommy tace "ku bata suyar friend rice din nan tayi" na fara yarfe hannu ina kallon Mommy kaman zanyi kuka "Mommy wallahi kone wa zanyi, ni kuba ni in yanka muku wani abu, ni zafin wutar ne bana so" asma'u ta biye min "dama wannan jikin naki haka babu tsoka ina zaki iya juya shinkafa? Bara dai in baki ki hada fruit salad" nan na kama murna na zauna dishen a kasa na nade kafa, maryam tace "so take fa ta gudu, ai tana zuwa kitchen zata ce a bata yanka, daga nan zata yanke hannu sai kuma ta tashi ta fita shikenan ba zaki kara ganin taba sai akan dining" duk suka saka dariya, na bata rai nace "ke Maryam har zaki nuna min aiki da wuka? Da likita fa kike magana" daga nan sai na fara basu labarin yaddda muke buda kan mutun mu bude kwakwalwarsa mu yi masa aiki sannan mu mayar mu rufe, ban ankara ba ina ta surutu sai gani nayi ana juye fruit salad din a bowl, har an gama hadawa, na dauko cup aka zuba min na koma gefe na fara sha ina cigaba da labari na. Tsayuwar mota muka ji a waje, Mommy ta kalleni tace "madam ki je ki chanza wadannan kayan na jikin ki, dan wannan tsageran yaron bashi da linzami a gidan nan, har kitchen din nan zai iya shigowa" nace "Mommy kaya na duk sunyi min yawa ne wallahi" tace "to sai ki saka wadanda suka fi wadannan girma ko kuma ki saka dogon hijab" nace "yes Mommy" har zata fita tace "kar ki yadda fa inzo dining in tarar dake da kayan nan sai ranki ya baci" da sauri na mike na riga ta hawa saman. Sai da nayi alwala na saka dogon hijab dina bayi sallah sannan na dan gyara fuskata na sauka kasa, ya Habeeb na tarar a palo, na zauna muka fara hira sai da ga Daddy, ya Walid da Sultan sun dawo, daga gani daga masjid suke. Ko kallon inda Sultan yake banyi ba na gaishe da Daddy, duk da ina jin idanuwansa a kaina. Daddy ya fara yi mana zancen convocation din mu da za'a yi next week, kuma duk tare za'ayi har dasu Faruk. Nan muka kama murna. Saukowar Mommy ce ta katse mana hayaniyar mu, gaba daya muka juya muna kallonta, tasha ado tun daga sama har kasa, tayi kyau sosai dan bazaka kalleta ba kace ta haife ni ma ballantana ya Walid daya doshi 30 years. Tana zuwa ta gaishe da Daddy, su kuma duk suka gaishe ta har Sultan, ta amsa ba tare da ta kalle shi ba, sannan tace "ga abinci nan a dining" ta mike ta tafi, muma duk muka bi bayanta. Muna zama na tashi na fara zubawa kowa abinci, sakara ce da miyar vegetables, fried rice da hadin salad sai farfesun naman rago, sai kuma fruit salad. Kowa farfesu na fara zuba masa sannan kuma sai in tambaye ka me kake so a cikin sakwara da shinkafa sai in zuba maka, amma da nazo kan Sultan ban tambaye shi ba na xuba masa fried rice da salad da yawa amma na ciccire tumatir din cikin salad din, duk abinda nake yi idon kowa akaina yake, ina gamawa yace min "thank you" ban amsa masa ba na koma na zauna. Ya Habeeb ne ya kasa shiru yace "shi Sultan mai yasa ba'a tambaye shi abinda yake so ba? Idan kuma ransa yafi son sakwarar kuma fa?" A hankali nace "baya cin sakwara ai" ya Walid yace "wow, yanzu kai zama kayi kai ta lissafa mata abincin da kake so da wanda baka so?" Daddy yayi gyaran murya duk kowa yayi shiru. Ina lura da Sultan gaba daya a takure yake, kuma nasan ganin Mommy a gurin ne. Daddy ya cigaba da maganar zuwan mu England ita kuma Mommy ta gaya mana cewa in munje zamu taho tare da Hafsat saboda tana son tazo ta haihu a gida, nan muka kara yin wata murnar. Sultan ne ya fara tashi yace wa Daddy zai koma office saboda ya baro aiki sosai a can. Yana tafiya su Daddy da yaya Walid suka fara maganar irin cigaban da company n Sultan yake samu, yaya Habeeb yace "yanzu fa a cikin 'yan watanni har ya fara zancen sayan building din kusa dashi zai kara wasu offices din ya kara expanding din gurin. He is a real hustler. Baya zama sam, baya kuma gajiya da aiki" ni da Mommy kawai jin su muke bamu ce komai ba. Sai da suka gama sannan Mommy tace da ya Habeeb "kai da kake ta celebrating success din wani kai ina taka success din? Tunda aka samar maka aikin nan ka fara ni banga ko hula ka saya wa kanka ba, baka da aiki sai kashewa 'yammata kudi ko? Ka san Allah Habeeb ka fita daga ido na in rufe, kana ganin walid ya sayi filin sa yana kokarin fara gini amma kai ko ajikinka sai ana maganar wani ka iya cewa 'he is a real hustler' bayan kai yanzu da zan duba account dinka babu wani abin kirki a ciki" yadda kokayi maganar ya Habeeb ne saka mu muka yi dariya ni da ya Walid, ta juyo tana hararar ya Walid tace "kai kuma ka iya taya wani murna cewa budurwarsa tasan abinda yake so da wanda baya so amma kai kaki yin budurwar ballantana ka gaya mata kai me kake so din, you are not getting any younger fa, ya kamata kai ma ka san me kake ciki tun kafin hajja ta juyo kanka ta samar maka mata" na rufe bakina ina dariya ganin yadda ya Walid ya bata fuska, ta juyo kaina tace "ke kuma a ina kika samu wannan wayar ta hannun ki?" Cikina ne ya bada kululu, na fara in ina, tace "shine ya baki ko?" Na gyada kai, tace "ce masa akayi ba zamu iya saya miki waya bane ba? Ko kuma ke ce kika roke shi?" Nayi sauri na girgiza kaina tace "to ki tabbatar kin mayar masa da wayarsa, phones din ki suna dakina kije ki dauka, kuma kar ki sake karbar komai nasa" nace "yes Mommy" Daddy yace "saura ni" duk mukayi dariya banda Mommy, yace "to duk kin hada min kan yara kin musu fada ai gwara ki hada dani kawai" Haka rayuwa ta cigaba da tafiyar mana inda Sultan ya dage da aikinsa ni kuma na fara mayar da kiba ta. Kullum haka muke wuni makale a waya duk da cewa zai zo muyi lunch tare, dinner ma haka, kullum da daddare kuma muna tare a palon su ya Walid har sai Mommy ta kira ni ko kuma in su ya Habeeb sun kora ni gida. Ana gobe zamu tafi england aka dauko Amina daga 'yalleman. Tare duk muka tafi England a jirgin Daddy, a gidan Hafsat na sauka naga tayi nauyi sosai, Sultan ma ba kunya cewa yayi acan zai kwana, dole Zayed ya bude masa guest room din waje, ranar kusan raba dare mukayi hira, da zayed da sultan suka zauna hira har sai da muka gaji ni da Hafsat muka tafi muka kwanta muka barsu. Washegari da sassafe muka tashi muka fara shirin tafiya Oxford, wata tsadaddiyar doguwar riga Sultan ya aiko min da ita yace in saka, ai kuwa kamar an gwada ni dan das ta zauna a jiki na, Hafsat ta kalle ni ta tabe baki tace "to ba dole tayi miki dai dai ba tunda yasan size din komai, ni rashin kunyar ku har mamaki take bani, kun wani maze kamar babu abinda ya faru" na bata rai nace "kai Hafsat, ni kam da na sani ban gaya miki maganar nan ba, ni dashi har mun manta ma amma ke kin kasa mantawa, it is in the past, please move on" ta tabe baki tace "shine yace miki ya manta? An gaya miki duk wannan kallon naki da yake na banza ne? To gwara ma ki sani, bai manta ba, dan haka sai kibi a hankali dashi" ni dai ban kuma ce mata komai ba saboda bana so tayi spoiling mood dina for today. Na dora graduation gown akan doguwar rigar muka fita, sam na kasa hada ido da Sultan sai nake ganin kamar maganar da Hafsat ta fada gaskiya ne. Tun daga gidan Hafsat muka fara pictures, a dole na ware