Sashe 151
Maimoon Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Episode Eighty Two : The Light Like I always say and always emphasize, things are not always what they seem. Duk abinda kake zargi, karka yanke hukunci a kansa sai kayi bincike ka tabbatar, duk abinda aka gaya maka akan wani indai har ba kaine da kanka ka gani ba, kar kayi saurin yanke hukunci akai, kayi bincike sosai first. Never and never judge a book by it's cover, in ba haka ba you might spend the rest of your life regretting. How far will you go to save your family? Hakan kuwa akayi. Daga nan sarki Abdallah ya saka akaje dakunan da khairat ta zauna aka kwashe duk kanin kayanta aka rufe dakunan. Gari yana waye wa yasa aka tara masa duk mutanen gidan tun daga kan iyalinsa har bayinsa ya ce ya hane su da ko da ambaton sunan khairat ne a gidan ballantana labarin ta ko wata magana data shafeta. A lokacin da Prince Sadiq ya tashi daga bacci jin kansa yayi fresh, babu abinda yake damunsa, kamar bashi da wata matsala a duniya. Ya danganta hakan da bacci mai nauyi daya samu. Yayi wankansa ya shirya ya tafi gurin mahaifinsa, ya tarar dashi yana cin breakfast, ya gaishe shi ya zauna gefe, mahaifin nasa kallonsa kawai yake yana studying dinsa, sannan yace "Sadiq yau baza a fita gurin abokanai ba ne?" Sadiq ya dan shafa kansa yace "Ranka ya dade yau gida zan zauna, sam yau bana son hayaniya" sarki abdallah yaji babu dadi har cikin ransa. Sadiq ne za'a ce masa ya fita gurin abokanai yace shi ya zashi ba? Sadiq din da kullum in yana gari gidan a cike yake da mutane saboda shi? Bayan ya baro mahaifin nasa ne ya tafi cikin gida gurin yaya, yana shiga palon ta yaga wani yaro yana ta kuka a hannun baba gaji, kallo daya ya yiwa yaron yaji wani irin tsanarsa a ransa, ji yake kamar ya hada daga baba gajin har yaron yayi musu duka ya kore su daga palon amma ya daure zuciyar sa ya wuce ciki, tunda ya shiga Yaya take kallonsa da mamaki har ya durkusa ya gaishe ta, ba zai iya jure kallon yaron ba dan haka ya mike ya fice, ga mamakin sa sai yaga yaron yana yunkurin zuwa gurin sa dan haka ya kara sauri ya fita in ba haka ba zai iya kwada wa yaron mari. Babu shiri Yaya ra dau mayafinta ta tafi gurin mai martaba, ta tarar har yanzu abinci yake ji ga Nani a kusa dashi, babu kishi a tsakanin Yaya da Nani dan haka a gabanta tayi magana, "Ranka ya dade me akayi wa yaron nan ne?" Ba tare daya kalle ta ba yace "Abinda yafi alkhairi a tare dashi shine abinda nayi masa" hawaye ya fara zuba a idon Yaya tace "Allah ya taimake ka ko dansa fa bai gane ba ya zakace hakan shi yafi alkhairi a rayuwarsa? Wannan ba Sadiq din mu bane ba, wani ne daban ba dan mu ba" bai ce mata komai ba, nani ta tambaye ta ta fada mata abinda ya faru, itama nanin kukan ta fara yi dan duk sun fahimci abinda mijin nasu ya aikata, nani tace "ayi mana afuwa, amma muna ganin wannan ai ba shine mafita ba, a zaunar da yaron ayi masa nasiha, asaka malamai suyi tayi masa adduoin nutsuwa, babu abinda yafi karfin addu'a, a hankali komai zai warware. Amma yanzu ba khairat aka raba shi da ita ba, rayuwarsa aka raba shi da ita gabadaya" sarki Abdallah ya ajiye chokalin hannunsa ya juyo yana kallonsu, a hankali yace "ku tashi ku bani guri" babu musu suka tashi suka bar gurin, ya jingina kansa a jikin kujerar dake bayansa, har yanzu ya kasa tantance cewa abinda yayi dai dai ne ko ba dai dai bane ba, odds din sunyi yawa, Sadiq yana da taurin kai kuma tunda yace sai yaje to sai yaje din ko me za'ayi masa, yes addua tana maganin komai amma tana taking time, sadiq ba zai jira ba. Yanzu addu'ar da zaiyi shine Allah ya karya abin wata rana, bayan komai ya lafa, yadda ko Sadiq yaje Riyadh maganar ta riga ta wuce. A ranar da yamma ya aika aka kira Sadiq, ya mika masa takardu guda uku yace "wata takarda nake so ka rubuta min, kayi copy uku, daya da larabci, daya da turanci daya da hausa" ba musu sadiq ya dauki takardar da biro ya fara rubuta abinda mahaifin nasa yake fada masa kamar haka "Bismillahir rahmanir rahim. Assalamu Alaikum wa rahmatullah. Ni Sadiq Abdallah, na saki matata Khairat Abdallah saki daya, idan ta sami miji tayi aure. Bissalam" yana gamawa yayi sauran copies din ya mika wa baban nasa, sannan yace "takardun menene wannan ranka ya dade?" Sarki Abdallah yace "sample ne na yadda ake rubuta takardar saki, zamu ajiye a fada saboda harkar shari'a" sadiq ya danyi dariya yace "sunana na gani shi yasa nayi tambayar" sarki yayi dariyar shima yace "da kai akayi sample din ai, kuma kai ai baka da mata khairat ko kana da ita?" Sadiq ya girgiza kansa yace "I never heard the name". Sarki ji yayi kamar zai yi hawaye dan tausayi. Haka Sadiq ya cigaba da rayuwarsa, kullum yana ganin wannan yaron mostly tare da sarki, kuma ga mamakin sa sai yaji ana nuna kamar dan nasa ne, duk sanda yaji maganar sai yaji wani bakin ciki kamar ya kama yaron ya shake shi ya mutu, to ya akayi ya zama nasa? How comes? Duk sanda yayi wannan tunanin sai yaji kansa gaba daya ya to she ya kasa tuna komai, wannan shi yake kara irritating dinsa a duk lokacin da yaron yayi masa magana ballantana kuma idan yaron ya tambaye shi wacece uwarsa, sai yaji gaba daya kansa ya toshe kwakwalwarsa ta daina aiki, wannan shi yasa kullum yake kara nisanta kansa da yaron. Present days Sarki Sadiq ya share hawayen fuskarsa yana jin matsanancin hausin kansa, duk wannan ya faru ne sanadiyyar taurin kansa da rashin jin maganarsa da kuma kin yiwa iyayensa biyayya a lokacin da suka hana shi auren khairat, amma kuma da akwai rabon sultan a tsakanin su, duk da haka da ace yayi biyayya ga mahaifinsa da mahaifin ya nemi hanyar maslaha cikin sauki ba tare da anyi masa abin da akayi masa ba. Taurin kansa cost him 30 years of his life. Ya tuna da auren da akayi masa, a take wani daci ya taso masa a bakin sa, wannan yarinyar zuwaira ya tsane ta tun tana yarinya, sannan kuma ga abinda tayi, what kind of a father will do what his father did to him? Gashi yanzu ba shi da rai ballantana ya tambaye shi why, amma ai da akwai wacce take da rai kuma yadan da sanin ta akayi komai. Aka hada shi aure da yarinyar da an san da a cikin hayyacin sa yake ko daura masa ita akayi a kafa ba zai tafi da ita ba, gashi yanzu har 'ya'yansu biyu together. Ya mike tsaye ya wake fuskarsa a sink ya dauki towel ya goge, ya sauke ajjiyar zuciya yana kallon reflection dinsa ta mirror, he is back, shekaru basu chanja original sadiq ba, from now everything will be alright. Yana bude kofar dakin mutanen da suke waiting room duk suka tashi tsaye suna kallonsa da mamaki, da yawa daga cikin su basu gane shi ba saboda ko babbar riga babu a jikinsa ballan tana rawani, ya bisu da kallon daya bayan daya har yaxo kan drivern sa, ya mika masa hannu "baki key" da sauri ya miko masa key din, ya fusga da sauri ya fita su kuma suka bishi da ido. It has been a while daya tuka mota amma bai manta yadda akeyi ba, a hankali ya tuka saboda baya son ya jawo hankalin mutane kansa. Direct sabon waje ya zarce ya yi packing ya tafi da sauri dakin Yaya, tana palo a tare da huda da kuma bayinta biyu suna yi mata tausa. Babu sallama ya daga labulen dakin ya tsaya yana kallonta, hatta huda bata gane shiba amma Yaya ba cire manyan kaya ba, ko menene dan nata zaiyi ba zata kasa gane shiba, a hankali ta mike duk da yanayin jikinta na tsufa, ta mike tsaye tana kallonsa kamar yadda shima yake kallonta, duk da baiyi mata magana ba amma tasan menene ya faru, da hannu ta yiwa mutanen gurin alama da su tashi su fita su basu guri. Suna fita yace mata "why?" Cikin nutsuwa tace "bani bace ba, mahaifinka ne, kuma sanda yayi bai shawarce ni ba" sarki ya hadiye daci a bakinsa yace "amma ya gaya miki dalilin da yasa yayi min haka?" Tace "bai gaya min ba amma na sani, yayi ne dan ya kare ka, yayi ne dan ya kare martabar gidan nan, yayi ne dan ya kare martabar kasar nan baki daya" hawaye ne ya fara taruwa a idonsa yace "to aura min zuwaira fa? Wanne irin uba ne shi? Wanne irin uba ne zai aura wa dansa yarinyar da tayi cikin shege? Wannan ma yayi ne saboda ya kare martaba ta ko saboda ya wulakanta martaba ta? Bai san Yaya tazo kusa dashi ba sai kawai saukar mari yaji a fuskarsa, ya rike kuncin yana jin zagi a ransa, cikin tsawa tace " wannan shine babban dalilin daya janyo yayi maka abinda yayi maka, dan bashi da rai hakan ba yana nufin zaka fada masa duk abinda yazo ranka ba. Komai yayi yayi ne to protect his family, you included". Ya fara tunanin yadda auren ya kasance, zuwairah cousin dinsa ce, tun tana yarinya baya son ta, jinin su bai hadu ba, tana da rashin kunya sosai ga shegen munafunci, duk a family shi baya son 'yan gidansu saboda sun zama wake daya mai bata gari, tun daga shigar su ma zuwa yadda suke mu'amala da mutane zaka gane cewa ba tarbiyya ce dasu ba. Bayan rabuwarsu da khairat da shekara kawai rannan babansa ya kira shi palonsa na ciki, yana zuwa ya tarar da baba Abdullahi, wanda kani ne a gurin babansa, ya gan su cikin tashin hankali, ya gaishe su suka amsa, nan Sarki Abdallah yake gaya masa cewa Zuwaira ce