← Book details Maimoon Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 121 OF 190

Sashe 121

Maimoon Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

A hankali na bude ido na, ji nayi kamar yanzu na kwanta, amma kuma ina jin a jikina kamar gari ya waye, nayi sauri na kalli window naga haske yana shigowa. Na mike zaune da sauri na kalli agogo, 8:30, inna lillahi, ko sallar asuba banyi ba, na shiga uku, wannan wanne irin bacci ne kuma ko juyi banyi ba. Da sauri na shiga toilet nayo alwala nazo na gabatar da sallah sannan na tashi na gyara gadon dana kwanta na koma toilet nayi wanka na dawo daki, tun kafin in fara shiryawa na kira wayar sultan, still switched off, na shafa mai na shirya cikin lace coffee color, riga da skirt da suka kama jikina suka zauna sosai, na gyara kitso na, na bayan ya sauko har gadon bayana, na gaban ma na sake tufke shi yabi ta saman idona ya sauka a wuyana. Na fesa turare na na fito ina neman dakin dasu Hafsat suka kwana, dakin kusa da nawa basa ciki, na kalle shi naga kusan irin nawa ne amma nawa yafi shi girma. Na fita ta dan corridon da zai fita dani palo na, anan dakin ba'kina yake, na murda kofar na gansu sun ba rarraje suna kwasar bacci, nayi murmushi a raina nace 'sun gaji' na duba agogo naga kusan karfe goma, ni kam yunwa nake ji, na dan daki kafar Amina "ke ku tashi fa, kun ma yi sallah kuwa?" Hafsat ta sake jan bargo, nayi ajjiyar zuciya dan nasan ko nafi kuda naci Hafsat ba zata tashi ba, Amina na takurawa sai da ta tashi tana ta kunkuni wai ita bacci bai ishe ta ba an takura mata. Nan na barta tana kokarin shiga wanka na fita ina zagaya gida, a raina ina lissafin Sultan ne fa yayi min alkawarin zai zagaya dani, nasan lissafin yadda gidan yake a raina dan haka ban wani sha wahala wajen gano part din Sultan ba, na tura main kofar sa naji a bude take, na shiga palon sa, na jima a tsaye ina shakar kamshinsa, unique kamshin da yake sakani lumshe idona kullum na jishi, a hankali nake tafiya ina karewa palon kallo, kusan irin nawa ne sai dai ban bancin arrangement din kayan ciki, na shiga corridor dinsa, shima two bedrooms ne dashi irin nawa amma shi bashi da dakin bakin da nake dashi a palo, instead sai akayi part din baki maza daban wanda sai ka fita can main palo sannan za ka shiga gurin. Bedroom dinsa na farko bayanan, kamar ma ba'a taba shiga dakin ba, bedroom dinsa na biyu kuma ina shiga naga alamar anyi amfani dashi amma ba'a kwana a ciki ba, har da kayan sa da yaje daurin aure dasu akan gado, daga dukkan alama sauri yake ya shirya ya tashi gurin party kuma daga can bai dawo nan ba. Na juya jikina a sanyaye na fita. Ina sultan ya kwana? A main palo naga Amina ta fito suna zaune da Fa'iza suna ta zuba surutu, ina shigowa suka bini da kallo, fa'iza tace "wow, masha Allah, babbar yaya kinga yadda kikayi kyau kuwa? Kowa ya ganki yasan babu tantama amaryace" sai kuma ta leka bayana kamar mai jiran wani ya biyo bayana, sai kuma ta rage murya tace "ina angon? Ina fatan dai ba nan zai fito ba dan takura mana zai yi da harara da tsawa" nace mata "sha kurumin ki, baya nan, ya fita already" ta bini da kallon mamaki tace "ya fita kuma? Wanne irin ango ne haka zai fice da sassafe?" Nace "kinsan abokanan sa da suka zo bikin nan wadansu ma bada ga kasar nan suke ba, to duk yau zasu tafi shi yasa ya fita da sassafe dan suyi sallama" daga dukkan alamu ta yarda da bayani na, tayi ajjiyar zuciya tace "har naji dadi, na dauka har an fara gwadawa amaryar halin, kinsan fa sai kinyi hakuri wallahi, dan indai yaya Sultan ne sai ya saka miki ciwon zuciya, dan wani lokacin inya fice sai yayi kwana da kwanaki bama a san inda yake ba" dariya na mayar da maganar nace "really? Kice za'a samu chanji kenan yanzu. Kar ki damu daga yau duk sanda kike bukatar ganin yayanki kizo nan zaki ganshi, in kinga bayanan to office ya tafi" ta tabe baki tace "to Allah yasa" sai kuma tace "dama Hajiya naji tace azo a kawo muku breakfast shine nace bara in zo mu gaisa in kuma ga gidan sosai. Ga abincin can akan dining an ajiye" nace mata "mun gode, in kin koma ki mana godiya a gurin Hajiya" tace "laah chafdi, yaya Sultan fa duk gidan nan shine dan lelen Hajiya, kinga shi ba'ayi masa fada, ba'a saka shi ba'a hana shi, duk abinda yake so shi za'ayi masa, dan haka in kika ce zaki yiwa Hajiya godiya har sai baki kin ya gaji" muka kalli juna ni da Amina, Amina tace "ashe sultan dan gata ne mu bamu sani ba. To shi kuma daya brother din naku fa? Shi ba'ayi masa gatan?" Fa'iza tace "shi wannan ai sha wuya kenan. Shi fa ko time din kansa bashi dashi. Kullum yana tare da Takawa bacci ne kadai yake rabasu, komai nasa shi yake yi. Shi wannan ma banajin ko budurwa yana da ita. In kinga kuwa fadan da Hajiya take masa komai kankantar abu sai kinyi mamaki" Amina ta cigaba da bugar cikin ta "abin tausayi, kice ko karatu mai zurfi bai samu yayi ba kenan saboda bashi da lokacin kansa" tace "kamar kin sani kuwa, da kyar ya samu yayi diploma ya hakura, Hajiya tace masa menene amfanin karatun? Ai anayin karatu ne saboda a samu aiki ake samun kudi, shi kuwa he got all the money to last him a lifetime, aiki kuwa dama dashi aka haifeshi" Amina zara cigaba da yi mata tambayoyi na girgiza mata kai, na chanza topic din da cewa "ni fa duk wannan hirar da kuke yi ba jin ku nake yi ba, dan yunwa nake ji" daga nan muka tashi muka tafi cin abinci. Muna cikin ci Hafsat ta fito, taci kwalliya kamar ita ce amaryar, tayi joining din mu muka ci abincin tare. Dankali ne da kwai, sai farfesun kaji da farfesun ganda, sai kunun gyada mai dadi wanda ni shi nayi tasha, dan sam baki na babu taste, Sultan ne kawai a raina. Nace da Hafsat "kiyi waya mana a kawo khairat, kar tayi ta kuka" tace "ba zatayi rigima ba, nayi expressing breast milk da yawa na saka mata a freezer, da anyi warming an bata shi kenan".

Ranar tamkar wanda ake sake yin wani bikin a gidan, dan sosai gidan ya cika da mutane mostly 'yan uwan sultan masu son ganin amarya da kuma dakin amarya. Na gode wa Allah dasu Hafsat basu tafi sun barni ni kadai ba, dan su sukayi ta hidima dasu suna zagayawa dasu daki by daki, kowa kuwa sai ya yaba da tsarin gidan. Duk kuma wanda yazo sai Amina ta zuba musu kayan gara da snacks din partyn jiya da ba'ayi ba ta bashi. Ni kuma akwatin lefe na na kayan kyalliya guda daya na bude nake rabarwa. Har magriba muna abu daya. Hafsat tayi waya gida ta gaya musu sai dare zasu dawo saboda baki sun yi min yawa, nan da nan sai ga yammata biyu Mommy ta sake turo wa, suka taho da katan katan na drinks da chocolate saboda yara. Abinci kuwa daga cikin gida akayi ta aiko mana, dan haka ko tukunya bamu dora ba. Sai da mukayi sallar magrib sannan kafa ta fara daukewa. Har lokacin babu Sultan babu labarin sa. Na kira wayarsa har na gaji amma still switched off. Bayan munyi dinner muka hadu muka gyara gidan tas har fa'iza da yake bata tafi ba. Muna gamawa muka zauna muna hira, hafsat ta lura ina ta danna wayata ta sake tambayata a hankali "har yanzu bai kunna wayar ba?" Kai kawai na gyada mata, tace "ki kira Amir, shirun yayi yawa" na sake dialing number din Amir, ya dauka muka gaisa yace "ai nayi niyyar shigowa dazu kuma na hango gidan a cike na fasa" nace "wallahi kam yau gidan masha Allah" nayi shiru, yace "bai dawo ba?" Nace "eh, kuma wayar a rufe" yace "amma da mamaki, kusan 24 hours fa kenan" naji hankali na ya kuma tashi. Yace " I will know what to do, am sure yana cikin gidan nan tunda duk friends din mu da suka tafi a gaba na suka tafi kuma bai shiga motar kowa ba, sannan all his cars are here. Za muyi organizing search party mu nemo shi duk inda ya shiga" nace "to na gode, duk abinda ake ciki dai sai a sanar mana" ina kallon Fa'iza tana kallona tana son ta san maganar me nake yi. Tace "wai yaya sultan ba zai dawo bane har yanzu? Tun safe fa nake gidan nan amma baya nan" Hafsat tace mata "a cikin mutanen kike so ya shigo ya zauna?" Tace "a'a wai dai ko yaya ne ai a gaisa dashi. Gashi har dare yayi kar mu tafi mu barta ita kadai"
Chapter 121 · 0% Book details