Sashe 181
Maimoon Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Episode Ninety Seven : The Real Prince Bikin Amir aka fara. Babu abinda Ummee da Takawa basu yi masa ba. Duk wani gata da 'da yake nema a gurin iyayensa Amir ya samu a lokacin bikinsa, sanda za'a tafi dauko amarya Ummee hana ni zuwa tayi, tace maiduguri yayi nisa bazan je ba, amma sanda aka kawo amaryar direct fada aka kawo ta gurin Ummee, ni kuma ina zaune a hannun daman Ummee. Sai a lokacin naga abinda Amir yake yiwa naci, ba wai kyau ne da yarinyar na kuzo mu gani ba, a'a, nutsatstsiya ce sosai, kana ganin ta kasan she is well brought up, har cikin raina ina kyautata zaton cewa Amir yayi dacen mace ta gari insha Allah. Washegarin da aka kawo Aisha, ni da Sultan muka shirya musu dinner. Takanas na kira saratu da fa'iza suka taya ni organizing dinner din, a cikin fada muka karbi hall akayi, sultan ya zuba kudi sosai, kuma abin ya kayatar sosai. Bayan an tashi daga dinner Amir ya sake kawo min Aisha har gida muka sake gaisawa. Haka kawai naji ta kwanta min a rai. Saratu da Fa'iza kam by now sun fahimci cewa auren iyayensu ya rabu amma bana jin sun san dalilin rabuwar auren. Ba laifi sun dangana, dan suna yiwa Ummee biyayya dai dai gwargwado, Ummee kuma kullum tana jan su a jikinta, dan komai zatayi sai ta hada da daya daga cikin su. Abbas har yanzu basu shirya da Hajiya ba, dan har yanzu anan gurina yake komai nasa. Yaji shawarata kuwa, dan ya koma makaranta, shi da kansa yaje ya nemarwa kansa admission, saboda sunan Takawa da yake amfani dashi bai sha wahala ba gurin neman admission aka bashi, tunda ya fara zuwa makaranta ya tattara harkar sarautar ya ajiye a gefe ya rungumi karatunsa. Dama ashe ba wai so yake ba tunda ba'a jininsa take ba, kawai dai dan ana matsa masa ne shi yasa yake yi. Ya nuna min rashin jin dadinsa game da kafsa masa da Amira tayi, ni kuma nayi masa alkawarin zan samo masa mata wacce tafi Amira komai. Na sami wani private hospital mai kyau, likitan su kwararre ne a harkar gynecology, nayi booking anan zan haihu. Sun yi min aune aunen duk daya kamata suyi min kuma sun gayamin zanke zuwa duk sati ana dubani, tunda yanzu edd na saura sati uku ya cika. Likitan yayi noticing high bp na, kuma mun zauna munyi magana dashi akan irin kalubalen da zan iya fuskanta. Na riga na sani, tun sanda na samu ciki, amma so far Alhamdulillah, dan lafiya lau nake bani da wani problem in banda bp din da take high. Rannan muna palona ni da sultan, ina zaune akan kujera shi kuma yana kwance akan kujerar ya dora kansa akan cinyata muna kallo, na saka hannuna absently ina shafa gashinsa, ina jin cikarsa da laushinsa, nace "wannan gashin dai ya kamata a rage shi, in ba haka ba zan fara yi maka kitso" ya danyi dariya yace "bismillah" na fara tsagawa da hannuna ina kitsawa, yace "ouch, da zafi fa" nace "kar ka bada ni mana, ka tsaya inyi maka mai kyau" ya biye min kuwa ya tsaya, nayi ta jagwalgwala masa gashin, nayi masa kitso guda biyar, ya tashi zaume yana shafa kan ni kuma ina tayi masa dariya, shine har da zuwa bedroom ya kalla a madubi, ya dawo ya tsaya yana kallona yace "da ace ni macene da maza sai sun bi layi sannan zan zaba" nayi dariya ina kallonsa nace "Allah yasan nufin jaki shi yasa bai bashi kaho ba" ya koma daki sai gashi da comb ya dawo ya kwanta ya dora kansa a cinyata yace "tsefe min" na karbi comb din ina tsefe masa ina tajewa. Yana kwance yayi shiru kamar mai bacci amma ba baccin yake ba. Na fara magana "I fell in love with you the second time I saw you" ya gyara kwanciyarsa yayi rigingine yana kallona yace "a dinner din Hafsat?" Na girgiza kaina nace "A Hilton" ya dan bata rai alamar tunani yace "that's the first time" na girgiza kaina nace "no, it is the second. The first time dana fara ganin ka a TV ne. Kuna fada da wani akan titi 'yan jarida suna dauka, daga baya aka kirawo police suka zo suka kama ku, they handcuffed you and you were smiling, it was as if you were enjoying yourself" ya danyi murmushi yace "I was" na cigaba "wannan shine dalilin da yasa sanda muka hadu a Hilton, duk da cewa naji wani abu a zuciyata game da kai amma sai na baka wrong information, saboda a lokacin na riga na saka a zuciyata cewa you are a bad person. But my love for you is too strong. A hankali na fara gane ainahin ko kai wanene and the love I have for you grow stronger" duk maganar da nake idona yana cikin nasa hannuna kuma yana kan fuskarsa ina shafawa. Na cigaba "a lokacin burina akan ka gida biyu ne, na farko shine in aure ka, kuma Alhamdulillah, wannan burin nawa ya cika" wani tattausan murmushi yayi min, ya daga gira yace "and how does it feel?" Nace "what?" Yace "how does marrying me feel?" Na mayar masa da murmushinsa nima nace "great, really great, better than I imagined it would" yace "good. Then what is your second wish?" Na danyi shiru ina tunanin ta yadda zan gaya masa ba tare da yayi wa abin wata fassara ta daban ba, nace "burina na biyu shine ina so mutane su sanka kamar yadda na sanka" ya dan bata fuska yace "bangane me kike nufi ba?" Nace "Mu mutane muna da wata halayya, abinda duk muka fara gani ko ji a dangane da wani shine abinda muke rikewa a ran mu, har sai wani abin ya faru da zai chanza mana ra'ayin mu. Ka tuna ranar da na ganka a hanya ka tare hanya da motar ka ka hana mutane wucewa?" Ya danyi murmushi yace "Of cause I remember" nace "a lokacin mutanen da suke gurin gaba dayansu babu wanda yake fadin abin alkhairi a tare da kai, wani a gurin bai ma taba ganin ka ba, dan haka abinda yaji an fada a gurin shine abinda shima zai tafi yana fada a gaba. Wannan misali daya kenan, na tabbatar akwai examples da yawa na irin wadannan abubuwan da suka faru tsakanin ka da mutane. Yanzu da ace zaka yi baddakama ka fita cikin mutanen gari kayi musu tambaya a game da kai nasan da zaka sha mamakin amsoshin da zasu baka. Na san ka chanza, wadanda suke tare da kai ma duk sun sani, amma sauran mutanen gari fa? Ta yaya zasu sani?" Yace "I don't care about mutanen gari. I never care about what people say akaina" nace "but I do. It has always been my dream to clear your name. To make people know you and love you" yace "what are you going to do then? Are you going to change their minds?" Nace "No, but I will do something that will create something that will make them change their minds" ya dan dauke kansa daga kallona yana kallon side, na saka hannu na juyo fuskarsa gurina nace "please sweetheart" yace "Maimunatu bana son kije kiyi abinda zaki shiga trouble a kaina. We are happy the way we are." Na langwabar da kai nace "nayi maka alkawarim abinda nake son yi babu trouble a cikin sa, ina cikin gidan nan zan yi ba tare dana fita ko gate ba. Please just say yes" kamar ba zaiyi magana ba sai kuma yace "OK. Amma duk abinda zakiyi sai na sani tukunna" na sunkuya nayi kissing dinsa a goshi nace "Thank you". Na riga na gama tsara duk abinda nake so inyi, dan haka washe gari tun da nayi sallar assuba ban jira sultan ya dawo daga masjid ba, na fita na tafi dakina. Na dauko laptop dina na dube project din da nayi akan sultan. Na zauna na fara editing, nayi summarizing ya zama page daya kawai, sannan na kara abubuwan da nayi learning recently akan sultan. Sai da na gama kuma sannan nazo na fassara da hausa. Sai ya zama kamar ace front and back ne, front din turanci back din hausa. Sai dana gama sannan kuma nazo na zauna na sake redrawing zanen sultan dana taba yi, exactly irin wancan sai dai a wannan ma na kara abubuwan da na kara a wancan. Ina cikin zanen sultan ya shigo, ya zagayo bayana ya tsaya yana kallon zanen yace "hmmm, wannan shine plan dinki?" Nace "yes" ya kalli zanen yace "ni fa nace miki shape din kaina ba kamar mangwaro bane ba. So kike ki rage min kasuwa dan kar wata ta shigo ko?" Kalmar watan daya fada naji ta daki kirjina, kawai sai na hango shi a idona tare da wata, na ajiye pencil din hannuna na rufe computer ta na mike tsaye, ina jinsa yana yi min dariyar ganin yadda na bata raina amma ko kallonsa banyi ba saboda wani haushinsa da nake ji. Ya rike hannuna yana kokarin juyo dani in kalle shi amma naki, ya rabu dani ya rungume ni ta baya ya saka kansa a wuya na yace "fushi kika yi Love?" Bance masa komai ba, yace "wasa fa nake miki" nace "I know, but it still hurts" yace "rikon da kika yi wa zuciyata Moon bana jin da akwai wacce take da karfin karbarta a hannunki. My heart was made to love you, only you. I was born to love only you. Ban taba son wata ba kafin ke kuma bazan taba son wata ba bayan ke. Only you" ya juyo dani yace "to yimin murmushi mana in gani" na sunkuyar da kaina ina son in dan kara tsahon fushin nawa, chakulkuli ya far yi min, nan take na fara dariya har kamar zan fadi, yayi saurin rike ni ya hada da jikinsa shima yana dariyar. Muka juya muna kallon zane na, yace "to taya zaki raba wa mutane? Binsu za kike yi gida gida kina basu?" Nace "Nope, am going to use a helicopter" bude baki kawai yayi yana kallona. Amir na kira a waya