Sashe 160
Maimoon Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
MAIMOON By Maman Maama Episode Eighty Seven : Riyadh Sai da naji daukewar numfashinta ta cikin wayar, sai kuma ta fara maganar da sauri cikin rawar murya kamar mai shirin yin kuka "what? What did you just said? Sultan is your husband? Yana ina ? Yana kusa dake?" Nace "yana jin duk abinda kike fada ummee" ta sake cewa "what? Sultan? Kana jina? My son are you there?" Sultan ya taso da sauri ya taho inda nake zaune ya kwace yawar daga hannuna, ban ankara ba sai gani nayi ya buga ta da jikin bangon dakin, a take ta tarwatse a kasa, ya tsaya yana kallona yana numfashi sama sama tamkar wanda yayi gudu, sannan kuma ba tare daya sake cewa komai ba ya juya ya shiga kofar corridon da zata kaika bedroom dinsa, yana shiga ya bugo kofar da karfi har sai da dakin yayi motsi. Na mike tsaye ina kallon kofar, dama nasan sai munyi drama da sultan akan ummeen sa, amma na shirya damarar sai na daidaita su, so help me God. Na karasa inda pieces din wayata suke na durkusa na tsince, wannan wayar ta gama yawo sai dai kuma wata ba ita ba, na zare sim card dina da memory card na tattara sauran na zuba a wastebasket, na kashe kayan wutar dakin na rufe koina na bishi dakinsa, ina shiga na tarar dashi a kwance a kan gado ko kayan jikinsa bai cire ba, idonsa a rufe kuma nasan ba bacci yake ba, na shiga toilet nayi shirin kwanciya nazo na saka wata T-shirt dinsa babba wacce tazo min har chinya ta, har yanzu yana nan a yadda yake, na kashe fitilar dakin na hau gadon nayi addu'ah sannan na jawo pillow na can nesa dashi na kwanta na juya masa baya, ko minti biyu banyi da kwanciya ba na jishi ya mirgino ya dawo jikina, ya saka hannuwanshi ya zagayo ni ta baya, bance masa komai ba, mun jima a haka sannan naji yace "why did you call her bayan na gaya miki I want nothing to do with her?" Nace "bani na kirata ba ai, ita ta kirani" yace "amma ai ke kika saka har ta kira ki din, kina sane ai" nace "afuwan, ayi hakuri" yace "please don't call her again" nace "I don't even have her number ta yaya zan kirata? Besides, ka fasa min wayar ma" yace "I will get you another one tomorrow. Ko ta kuma kiranki kar ki dauka, am doing perfectly fine without her" na juyo ina kallonsa na bata rai duk da nasan duhu ne ba gani zaiyi ba, nace "why are you blaming her wai? Bayan kasan bata da laifi" yace "she left me, shine laifinta" nace "she didn't, a gaba na Takawa ya gaya maka a ka aka dauke ta aka fita da ita, what is her fault in that?" Yace "she should have come back for me, why didn't she look for me all these years?" Nace "bansani ba sultan, amma nasan dole tana da dalilin ta, uwa tafi gaban komai a duniyar nan. Ba zaka san dalilin da yasa bata dawo ta neme ka ba har sai ka bata chance, har sai kayi magana da ita, idan kunyi maganar kaji cewa hujjarta is not good enough nayi maka alkawarin ba zan sake yi maka maganar ta ba" na daure shi da jijiyoyin jikinsa, bashi da amsar da zai bani sai cewa yayi "maganar ta isa haka. Let's sleep". Washegari na daura niyar fara abinda zan yiwa sultan, dan haka dana hada mana breakfast sai naci nawa a kitchen na kawo masa nasa coffee room dinsa, na tafiyata dakina, ina zaune a palo ya shigo, naji kamshin turarensa amma ban dago na kalleshi ba, yace "me yasa baki zo munci abinci tare ba?" Na bawa iska ajjiyarsa, ya karasa shigo wa dakin ya tsaya a gaba na, ya shirya alamar office zai fita, kallo daya nayi masa na dauke kaina, yace "magana fa nake miki Moon" na yamutsa fuska nace "naji ai, nafi son cin abincin ni kadai ne shi yasa" ya saka hannu ya juyo da fuskata yace "wai duk akan maganar wayar ne? Yanzu kafin inje office ma zan siya miki wata" bance masa komai ba kuma ban kalle shi ba. Ya dora lips dinsa akan nawa yana kissing, na kwace fuskata na mike na bar gurin ina juya masa bombom, ina shiga daki na bugo kofa ta da karfi irin yadda yayi min jiya. Ranar Amir ne yazo daukar musu abinci, yana zuwa ya miko min waya yace "gashi inji oga kwata kwata, yace yayi miki charge, kuma dan Allah ki kirasa yanzu" na karba nace "to nagode" yace "ki kirashi fa, dan tun safe yana can ya kasa zana komai, yace rashin jin muryarki ne" na kirkiro murmushi nace "zan kira ai" Amir yana fita na jefar da wayar akan kujera nayi tafiya ta daki. Ranar sultan bai kai yadda ya saba kaiwa a office ba sai gashi ya dawo, ya tarar dani na tasa gyada mai gishiri a gaba ina ci, na daga kaina nayi masa sannu da zuwa na cigaba da abinda nake yi, yazo ya zauna a gaba na ya harde kafa yana leka fuska ta yana murmushi, saura kadan in mayar masa amma na daure na bata fuska, yayi ajjiyar zuciya yayi tagumi da hannu biyu yace "wa ya baki gyada?" Nace "ai kawa nayi aka siyo min" yace "amma kinsan duk abinda kike so ba tare muke zuwa mu siyo ba?" Nace "na hutashshe ka" yace "ina wayarki?" Nace "bana bukatar waya ni, tunda babu wanda zan kira da ita" Har ya tashi ya tafi kuma sai ya dawo ya sunkuya ya dauke ni chak ya tafi dani bedroom dinsa. Ban hana shi komai ba amma barinsa nayi yayi abinsa shi kadai, shi kadai yayi kidansa kuma yayi rawarsa, kamar zaiyi kuka yace "Love menene hakan ne kike yi wai. Please come back to your normal self, I don't like this new you" ba tare dana kalleshi ba nace "kai ka siya ai da kudinka" ya danyi shiru sannan yace "yanzu me kike so ayi?" Na juyo ina kallonsa nace "ka shirya mu tafi Riyadh" da sauri ya girgiza kai "no way, babu inda zamu je" na mike na dauki riga ta ina sakawa nace "ok, suit yourself" ina jin yana kirana nayi tafiyata ba tare dana waigo ba. Haka na cigaba da gasawa sultan gyada a hannu, he is beyond frustrated yanzu, ban hana shi taba ni ba amma shi kansa ba jin dadin abin yake yi ba, murmushi kuwa rabon da inyi masa tun kafin muyi waya da Ummee. Na kunna wayata na saka sim card dina saboda kar mutane suyi ta nema na, ban jima da kunna wa ba kuwa Hafsat ta kira ni "Moon me ya faru ne ranar nan? Wayar ta dauke kuma munyi ta kira shiru bata shiga? Na gaya mata duk yadda mukayi da sultan, tace "ai kuwa ta tayar da hankalinta, ranar kusan kwana tayi tana kuka, har sai da nayi nadamar tayar da maganar nan. Yanzu menene abinyi?" Nace "kin san halin sultan, and he is probing harder than I thought, amma zan cigaba da ganin yadda zanyi dashi. Ki kwantar mata da hankali, ki san abinda zaki gaya mata". Ranar hankali na ya kara tashi akan maganar ummee, na yanke shawarar zan shigar da Takawa cikin maganar. Yana zuwa da daddare na riga sultan zuwa, naje na gaishe shi ya amsa da fara'arsa yana min godiyar kokarin da nake gurin yi musu hidimar abinci. Na dauko waya ta na buda hoton Ummee na ajiye masa a gabansa ina kallon fuskarsa, ga mamaki na sai naga banga changin komai ba, ya dagi kai yana kallona yace "Hafsat ce ta turo miki?" Mamaki ya kara kamani nace "eh" ya gyada kai yace "tun washegarin ranar dana dawo hayyacina na aika har can Riyadh din nace a binciko min labarinta, an kuma bani labarin komai, nasan dan wanta ne yake auren yayarki Hafsat, har number dinta an turo min, what I lack is the courage to call her" na kalleshi da mamakin wai kamar shi ne zai ce bashi da courage, yace "yes, after all we went through together sannan kuma na tura mata da takardar saki kuma na kwace mata danta tsahon shekaru talatin, I don't know me zance mata in na kirata ko kuma na je wajanta" na sunkuyar da kaina, yace "sultan yaga picture din?" Nace "eh ya gani" yace "me yace?" Nace "he didn't say anything yet" yace "kina ganin zaije?" Nace "maybe, amma ba yanzu ba" yace "yayi fushi ko?" Kai kawai na gyada masa, kafin ya sake cewa komai sultan ya shigo dakin, ya bimu da kallo yana kallon waya ta a gaban Takawa, bai ce komai ba na mike na bar gurin, ina kallon sultan yana harara ta a raina nace yau akwai daru kenan. Ai kuwa Takawa yana tafiya sai gashi har dakina, "zancan me kuke yi dazu kafin inzo?" Nace "zancen Ummee muke yi" cikin fushi yace "dama dashi kuka hada baki kenan" na girgiza kaina nace "bamu taba maganar dashi ba sai yau, yanzun ma kuma ni ce na fara yi masa maganar, ashe duk abinda nake son in fada masa ya sani, yana da address dinta da number wayarta da komai amma ya kasa kiranta saboda bai san me zai ce mata ba" ya zauna a kusa dani yace "me yace?" Na juyo ina kallonsa nace "ya tambayeni in ina ganin zaka iya zuwa gurinta" ya mike tsaye da sauri "no, I am not going to be dan aiken soyayyar su, if he want his wife he should go get her by himself" nace "then go as her son, ba wai dan aiken takawa ba" ya sake cewa "NO, ita me yasa ba zata zo Nigeria ba? In tana son gani na tasan a inda nake, abinda zatayi kawai shine ta je airport ta shiga jirgi ya kawo ta Nigeria. Tunda kika ga tsahon shekara talatin bata zo ba to bata son ganina, ba zanje ta wulakanta ni inzo in ji haushi ba, maybe tayi wadansu yayan and she don't need me in her life"