← Book details Maimoon Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 153 OF 190

Sashe 153

Maimoon Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Episode Eighty Three : The News Moon Na jima da wayar a kunnena ina lissafa maganar ta amma na kasa bata amsa saboda wani irin shock da naji, har saida tace "Moon kina jina kuwa" nayi sauri nace "ina jinki Hafsat vara in duba picture din" na katse kiran na shiga WhatsApp, hannuna har rawa yake yi "oh dear God, let it be" na fara downloading picture din amma gani nake yi kamar ba zai gama budewa ba, sau biyu yana failing ina sake trying. Finally ya bude, sai da na dauke numfashi na saboda mamaki abinda na gani, hoton balarabiyyar na gani, amma kuma kamar sultan da siffar mata, the eyes, the nose, the lips, the eye brow, the eye lashes duk irin na sultan ne, hatta murmushin da tayi irin na sultan ne, farin fata kawai ta fishi sai kuma kasancewar ta macece, amma kuma anya wannan ce ta haifi sultan? She is too young to be his mother, amma kuma har sunan iri daya. Na kira Hafsat, tana dauka tace "kin ganta ko Moon?" Nace "na ganta Hafsat. A ina kuka hadu?" Ta fara min bayani "Aunt din Zayed ce, kanwar babansa, to irin bata shiga mutane sosai shi yasa tun da muka zo bamu ganta ba, sai dazu baban Zayed yace masa lallai yau ya kaimu gidanta mu gaishe ta. She live alone a gidan nata ma. Wato Moon kudi ne da ita kamar banza, 'yar kasuwa ce sosai, babu da babu jika, babu kuma miji, ina ganinta gabana ya fadi, nayi ta kallonta ina tunanin dawa take yin kama? Kawai sai da tayi murmushi na gane sultan ne, kuma na tuna cewa mamansa balarabiya ce, amma ban tambaye ki sunan ta ba" na sauke ajjiyar zuciya nace "Sunan ta khairat" da sauri Hafsat tace "Allah da gaske? Moon ita ce mamansa kenan?" Nace "I don't know Hafsat, amma baki ganin tayi yarinta da yawa?" Tace "ke dalla can hutu ne fa, kinga sisters dinta data girma kuwa?" Nace "amma me zayed yace miki a dangane ta ita? Ta taba aure a nan ko kuma ya labarinta yake?" Hafsat tace "it is all mysterious Moon, zayed bai san komai a kanta ba, da yake shi kinsan ba'a Riyadh ya tashi ba kawai abinda ya sani shine rayuwar ta take yi ita kadai bata shiga mutane, kuma tunda ya santa bata da aure" na danyi shiru ina tunani nace "please Hafsat can you get her to talk to you?" Hafsat tace "I think so, kinsan hali na da bin kwakwkwafi, kuma daga gani na ta fara sona bansan dalili ba, ga kuma khairat mai sunan ta" sai kuma tayi shiru sannan tace "wai dama sunan ta kika sakawa khairat" na danyi dariya nace "eh sunan ta ne" Hafsat tace "Munafuka, shine kika saka wa yarinya ta sunan surukarki ko?" Nayi dariya nace "to ai gashi nan kema maybe surukar taki ce" Tace "show sultan the picture ki ji abinda zai ce, ni kuma zan fara tambaya inji labarin ta, ko a gurin ummeen zayed ne, daga nan sai mu gane ko ita ce ko ba ita bace ba" na danyi shiru sannan nace "Hafsat bama tare da Sultan yanzu" kamar bata ji sosai ba tace "what?" Na ce ina jin hawaye yana taruwa a gefen idona "ina gida yanzu" tace "subhanallah Moon wannan wanne irin muguwar magana kike fada min hakan? Sultan din tafiya yayi kika zo gida?" Nan hawaye ya balle min nayi tayi, tana jina bata ce min komai ba, sai da na gama dan kaina sannan na fara bata labarin abinda ya faru gaba daya, na kara da cewa "Hafsat ban san ya zanyi ba, Sultan zafin zuciyarsa yayi masa yawa Hafsat, shima Ibrahim ban san me yake so inyi masa ba, nayi aure kuma ina ruwansa dani?" Hafsat tace "to ai ni sultan yayi min dai dai, cin ubansa ya kamata yayi yadda gobe in ya hango ki a guri da gudu zai fita. Yanzu kina nufin akan Ibrahim din kika baro gidan mijinki?" Nace "Hafsat ba'a kan Ibrahim bane ba, akan Sultan ne, akan bakar zuciyarsa, Hafsat kisan kai fa yayi niyyar yi, da Ibrahim ya mutu me kike ganin zai faru da shi? Me kike ganin zai faru dani? Sannan zargin da yayi min shi yafi komai kona min rai, he should have trusted me" Hafsat tace "tayaya kike tunanin zaiyi trusting dinki bayan ko cikin da kike dashi baki gaya masa ba? Idan da ace yasan da cikin da duk haka ba zata faru ba, idan kakar chocolate kike so zai fita ya sayo miki, in ma ya ganki da Ibrahim din yasan ba purposely kika hadu dashi ba. Idan kika yi la'akari da rayuwar sultan dole yana da trust issues, he is scared of loosing you, gani yake yi kamar kowa is against him" nace "amma Hafsat, upon all what we went through together, ya kamata ace by now ya yarda dani" tace "kin bashi reasons din da zai yarda da ke ne? Mun jima muna tattauna wa da Hafsat a waya, ban ankara ba kawai sai naji wayar ta mutu, ban kunna ta ba kwanta ina lissafa maganganun Hafsat a raina, is what happened my fault? Ban boye wa Sultan maganar cikin nan saboda komai ba sai don ina son inyi surprising dinsa, but I get more than what I bargain for. Naji an fara kiraye kirayen sallah dan haka nasan inna ce zan kwanta bacci zanyi missing din sallah asuba, dan haka na saka phone dina a charge nayo alwala nazo na bude al'qurani na na fara karatu, ina nan har akayi assalatu nayi sallah sannan na kwanta, kafin bacci ya dauke ni na yanke shawarar cewa first thing in the morning zan nuna wa Daddy picture din da Hafsat ta turo min, tunda ya san mahaifiyar sultan zai iya tabbatar min idan itace ko a'a, next thing zan kira Sultan inji halin da yake ciki, my heart can't take hurting him. Amma ga mamaki na ban farka ba sai after 11am, kuma nasan physical and mental exhaustion ne ya kawo min dogon baccin. Ina tashi na kunna wayata, ko wanka banyi ba na saka hijab dina na tafi neman Daddy, a palon sa na same shi shida Mommy, na karasa na gaishe su, Mommy tace "yanzu nake tunanin ko tashin ki za'ayi kichi abinci, sai Daddy n ki yace a barki ki tashi da kanki" na danyi murmushi ina searching picture din da Hafsat ta turo a waya ta, food is the last thing on my mind babu abinda nake so irin inga Sultan, maybe I am weaker than I thought in dai akan soyayyar Sultan ne. Ina samo picture din na karasa gaban Daddy na mika masa nace "Daddy kasan wannan?" Ya karbi wayar daga hannuna sannan ya mike zaune daga kashingiden da yake, ya kalleni sannan ya kuma kallon screen din yawar yace "a ina kika samu hoton khairat? An ganta ne?" Ji nayi wani excitement yana taso min tun daga kafafuwana har cikin kaina, nace "Daddy ita ce mahaifiyar Sultan?" Yace "of cause itace mana, baki ga kamar ba?" Da sauri Mommy ta matso tana kallon hoton tace "Allah mai iko, kamar tasu har ta baci" na tashi da sauri na rungume Mommy ina jin dadi, sai kuma naji kunyar ta na sake ta, Daddy ya tambayeni inda na samu hoton nayi masa bayani, nan suka kara wani mamakin, ikon Allah kenan, wai all this while a she sultan da Zayed 'yan uwa ne babu wanda ya sani. Mommy tace "to yanzu menene abinyi? Zaki gaya masa ne ko zaki bari Hafsat tayi bincikenta a can muji dalilin da yasa duk tsahon wannan shekarun bata nemi danta ba?" Na girgiza kaina , a raina nace "not again, na daina boyewa sultan komai insha Allahu" a fili nace "Mommy zan gaya masa, yana da right ya sani, shi zai yanke decision din me ya kamata yayi" Daddy ya amince, yace "amma ai naga jiya kin kore shi, yanzu kiransa zaki yi? Na dan sunkuyar da kaina ina murmushi, Mommy tace " kar dai kice min shikenan har kin gama horon nashi da zaki yi? Duk kurin zubar da ciki da waye har ya kare kenan, kar ki rako mata mana maimunatu" na rufe fuskata da hannayena, Daddy yace "in kin huce ma ni ban huce ba, sai yazo ya bada hakuri kuma yayi min alkawarin irin haka ba zata kuma faruwa ba. Shi kuma wancan har yanzu fa bai dawo haiyacinsa ba, dan haka nasa anyi wa family dinsa waya a can ibadan an gaya musu halin da yake ciki" bance komai ba saboda bazan iya yiwa Daddy musu ba amma ni kam da zai barni da yanzu zan tafi in kira sultan in bashi labarin mahaifiyarsa, maganar Ibrahim kuma naji babu dadi, it is a pity, naji tausayin mamansa da 'yarsa, a raina nayi masa addu'ar samun lafiya, Daddy yace "ko zaki je ki duba jikin nasa?" Nayi saurin girgiza kaina, there is nothing more between me and him, ni yanzu kawai mijina nake son gani. Jin basu sake cemin komai ba na gane sun gama magana dani kenan, na tashi na tafi palo ina neman abinda zanci, na faki ido naga babu wanda yake kallona na dauko waya ta nayi dialing number din sultan, amma bansan me zance masa in ya dauka ba, tana ta ringing amma ba'a dauka ba, a raina nace yayi fushi shima, nafara duba messages wai ko ya turo min message ban sani ba, babu message din sultan sai na Amir, na buda na fara karantawa "your husband is sick, kuma ke yake nema" wayar ce ta zame daga hannuna ta fadi kasa, nima na bita na zauna dabas a kasa, for seconds kaina ya toshe, sannan kuma cikin karkarwar hannu na dauki wayar zuciyata tana wani irin bugawa na kira number din Amir, bugu biyu ya dauka yace "Moon ina kika shiga tun safe ina ta nemanki wayarki a rufe. Muna asibiti da Sultan fa bashi da lafiya" cikin muryar kuka nace "Amir me ya samu Sultan? Ya jikin nasa? Amir na shiga uku" yace "baki shiga uku ba Moon jikin Sultan da sauki, dazu dai babu
Chapter 153 · 0% Book details