← Book details Maimoon Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 175 OF 190

Sashe 175

Maimoon Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Episode Ninety Four : RIP Ya rike fuskata a hannunsa yana kallon cikin idona yace "kinsan dai da rayuwa da mutuwa duk na Allah ne ko? Kinsan babu wanda ya isa ya raya wani idan har Allah ya rubuta cewa kwanansa ya kare ko? Kuma kinsan babu wanda ya isa ya kashe wani in har kwanansa bai kare ba ko? Iyaye, 'yan uwa, miji ko mata, 'ya'ya dukka Allah ne yake bamu su kuma shi yake karbar su a lokacin da yaga ya dace. Duk lokacin da muka rasa wani abinda ya kamata muyi shine mu gode wa Allah daya bamu su tun farko, har muka rayu dasu muka ji dadinsu suma suka ji namu, dan daga mu harsu na Allah ne. Idan mutum ya riga ya mutu babban abinda yake bukata daga gare mu shine addu'ah, mu nema masa rahamar ubangiji tare damu baki daya, mu kuma yi fatan Allah ya sada mu dashi a aljannah inda zamuyi rayuwa ta har abada ba tare da tsofa ko mutuwa ba. Maimunatu Allah yayi wa Baffa rasuwa jiya da daddare, yau da safe akayi jana'izarsa aka kaishi gidansa na gaskiya." Wani sabon kuka ne ya taso min, yayi sauri ya hade bakinsa da nawa, sai da yaji na tsayar da kukan sannan ya sake ni, na ture shi da sauri na fara kokarin mike wa, ina jin kaina yana juyawa, wayyo Allah baffana, wai baffa ya tafi ya barmu shikenan ba zamu sake ganin sa ba? Na runtse idona ina hango kyakykyawar fuskarsa ta fulani mai cike da kwarjini da fara'a, innalillahi wa inna ilaihir rajiun, sultan naji ya sake rike ni yana kokarin zaunar dani "Moon zaki fadi fa, menene hakan wai? Shi yasa tunda aka kaishi asibiti aka ce kar a gaya miki saboda an san halinki" na juyo da sauri ina kallonsa bibbiyu, nace "asibiti? Au dama bashi da lafiya amma baka gaya min ba? Daya mutum ma har sai da aka binne shi sannan za'a gaya min" ya sake kokarin rike ni na ture shi, yace "to inda an gaya mikin ma menene zaki yi masa? Za ki cire masa ciwon ne ko kuma zaki hana shi mutuwa?" Da karfi nace "I could have been there for him, I could have hold his hands and say goodbye to him" yace "and what difference will that make?" Nace cikin fada "It would have make me feel better". Na rufe fuskata da hannayena na fara kuka a hankali mai shiga zuciya. Duniya kenan, ina nan ina enjoying rayuwata ashe Baffa yana can yana sallama da duniyar gabaki daya. Sultan ya zo ya durkusa a gaba na, har yanzu swimsuit din jikinsa a jike take yace " ya salam, moon da kinsan yadda nake jin kukanki a raina da kin daina, da ina da dama da ba zaki taba kuka a rayuwar ki ba, amma ba zan iya dawo miki da baffa ba, dan Allah ki tausaya min ki daina kukan nan haka" ni haushi ma naji yana bani, daga shi har sauran 'yan gidan mu duk haushi suke bani, tunda duk muna waya dasu kuma duk sun san baffa yana asibiti amma babu wanda ya gaya min. Ya dora hannunsa akan cinya ta na ture hannun na juya baya na na cigaba da kuka na. Ina jin shi ya mike ya shiga toilet, naji alamar shower sai kuma ya fito ya shirya, har lokacin ina zaune ina kuka na, yazo ya zauna kusa dani, na matsa. Yace "am sorry Love, nasan bashi da lafiya amma kinka yanayin da kike ciki, ga problem din bp dinki, wannan yasa aka ce kar wanda ya gaya miki, babu wanda yasan mutuwa zaiyi saboda babu wanda yasan gawar fari sai Allah. Am sorry" yayi kokarin juyo dani in kalle shi amma naki yarda, ya rabu dani yace "zan je airport yanzu in gani ko da akwai plight zuwa Nigeria yau ko gobe. Please dan Allah promise me you will stop crying" ya zagayo ta side din da fuska ta take, ya saka hannu ya bude fuskata dana rufe da hannuna, fuskarsa tayi abin tausayi, ya goge min hawayen fuskata, yace "kinji abinda na gaya miki? Ina so inje in samo mana plight tickets amma bana son in barki kina kuka kuma, please ki daina sai in tafi. In baki daina ba kinga ba zanje in sama mana plight ba ballantana mu tafi Nigeria" na goge fuskata ina kallonsa nace "na daina to" yace "promise" nace "I promise" sai da yaga na tsaida hawayena sannan ya fita, yana fita na hau kan gado na kwanta na cigaba da kuka na. Wajan karfe daya ya dawo, inajin shigowarsa na rufe idona kamar bacci nake yi. Ya dan jima a tsaye yana kallona sannan ya hawo gadon ya dan taba jikina, yace "my God, kukan ki ka cigaba kenan ko? Bayan kinyi min alkawarin ba zakiyi ba" bance masa komai ba, naji ya sauka daga kan gadon, na bude idona ina kallonsa naga ya dauko first aid box din mu ya dauko min magunguna na, ya dauko bottle water ya bude ya hawo gadon ya mikar dani tsaye ya bani nasha. Na koma na kwanta ina kallonsa nace "so.., when are we going?" Ya dan shafa kansa yace "babu plight zuwa Nigeria yau da gobe, sai jibi idan Allah ya kaimu." ya miko min tickets guda biyu na karba ina kalla, that means sai Baffa ya kwana uku da mutuwa sannan zanje gida. Na lunshe idona ina jin jikina yana relaxing saboda maganin da nasha. Ina nan a kwance ina kallon sultan yana kokarin fara hada mana kayan mu, yayi waya restaurant ya fada musu abinda zasu kawo mana for lunch, da kyar na tashi nayi sallah na koma na kwanta. Bana kukan yanzu amma kuma raina gaba daya babu dadi, duk maganganun da muke yi da baffa ne suke dawo min rai na. Irin nasihohin da yake yawan yi mana akan gudun duniya, akan zumunci, akan biyayya ga iyaye da kuma miji. Da kyar sultan ya matsa min na danci abinci na koma na kwanta. Karfe biyar na yamma sultan ya gaji da zama shi kadai ya fita waje, sai kuma gashi ya dawo da sauri yazo ya daga ni tsaye ya fara kokarin cire min riga, na rike hannu sa, "sultan menene haka?" Bai ce min komai ba ya dauko wata rigar mai kauri da dogon hannu da collar ya saka min, ya saka min hula da safa ni dai duk ina kallonsa, nace "ina zamu je kuma" yace "kifi zaki je ki kamo mana ki gasa mana muci da daddare" na dan bata fuska nace "kifi kuma? Ni ban iya kama kifi ba" yayi murmushi yace "yau zaki koya, common, let's go" ya kama hannuna muka fita. A hankali naji na dan fara sakin raina, bawai na daina jin zafin mutuwar bane ba, na dai daina jin haushin sultan. Wani boat muka dauki haya muka shiga, daga ni sai shi, shi ya tuka ya kaimu tsakiyar ruwa sannan ya dauko wani dan kwando ya bude ya dauko wata kugiya ya daura zare a jikinta, sannan ya zagayo ya zauna a baya na, ya saka kafafuwansa a both sides dina, ya kama hannayena da nasa, ya saka fuskarsa a wuyana yace min a cikin kunnena "I am going to teach you how to catch a fish" cikin raunanniyar murya nace "sultan Baffa ne fa ya mutu, how can I just be busy catching fish bayan Baffa ya bar duniya?" Yace "mutuwar Baffa tana nuna mana abubuwa da yawa, daya daga cikinsu shine; there is an ending to life. Duk shekara, duk wata, duk sati, duk yini, duk awa, duk minutes, duk second din daya wuce ba zai dawo ba. What we need to do is to make the best of our time kafin namu lokacin muma yazo. We should live our life because it is a gift from God. Baffa yaji dadi, yayi rayuwa mai tsaho kuma mai kyau, ya tafi ya bar zuri'ah mai albarka. Wani tun kafin yayi aure ma yake mutuwa, wani tun yana yaro ma kafin yasan menene rayuwa yake mutuwa, wani ana haihuwarsa yake mutuwa, wani kuma tun a cikin mahaifiyar sa yake mutuwa, shi ko duniyar ma bai gani ba ballantana yaji dadinta. Wani kuma zai yi rayuwar mai tsahon har yakai kamar shekarun Baffa amma kuma sam babu abinda ya tsinana a cikin ta, babu abinda in ya tafi za'ace ga abinda ya bari na alkhairi sai dai na sharri. Amma baffa kuma fa? Ko mu daya bari ba mun isa mu taya shi gode wa Allah ba? Mu taya shi neman rahamar ubangiji ba?. Mutuwa is a circle of life, wani ya mutu sannan a haifi wani. Jiya da baffa ya mutu hundreds of babies were born all over the world, sannan hundreds of people sun mutu tare dashi" ya dora hannayen mu akan babyn mu da yake ta tsalle tsallensa babu abinda ya dame shi, yace "ranar da za mu haifi babyn mu, ranar hundreds of people zasu mutu. And what favor of our Lord do we deny?" Na lumshe idona ina ina jin dadin iskar gurin, ina jin dadin dumin jikin sultan, ina kuma jin dadin kalamansa, sannan inajin dadin motsin baby na a ciki na, what favor of my lord do I deny? Allah yayi min komai, ya bani komai, why should I be sad dan ya karbi abu guda daya daga cikin dubun daya bani? Na bude ido na ina kallon clear ocean din nace "I thought we are suppose to be fishing? Ya dan yi dariyar jin dadi yace "yes Love". Mun kama kifaye da yawa, dan sai da muka cika dan basket din da muka taho dashi, daga baya sai muka fara zaba, duk wanda muka ga mummuna ne sai mu mayar dashi cikin ruwa, gaba daya hankali naji ya kwanta, babu wani sauran bakin ciki a tare dani, nishadin mu kawai muke muna dariya, in mun kamo kifi yana ta tsalle mai in kankame sultan wai tsoro nake ji kar ya cije ni, in mun mayar dashi ruwa kuma sai muga sun fita a guje, nan ma muyi tayi musu dariya. Bamu ankara ba sai gani mukayi rana zata
Chapter 175 · 0% Book details