← Book details Maimoon Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 55 OF 190

Sashe 55

Maimoon Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

I don't know why inna fara typing bana son tsayawa sai daga baya in ga ashe nayi da yawa. Ya kamata mu koma yi kadan kadan ko?

Episode forty four : America 2

Yana gama fadin haka ya ficewarsa ya barni. Naje nayi locking kofar amma a raina ina cewa wannan ai bonono ne rufe kofa da barawo. Na dawo na kyara inda muka ci abinci sannan nayi shirin kwanciya, ranar sam na kasa bacci saboda rashin sabo da sabon gurin, kawai na tashi nayi alwala na yita salloli ina rokon Allah ya bani karfin zuciyar da zan iya controlling Sultan shi kuma Allah ya shirya min shi, na tuno da maganar Amira da tace am too soft and Sultan is too hard, in dai har ina so in gyara masa rayuwarsa dole nima in zama hard amma how? I have been soft tunda nazo duniya how can I be hard kuma yanzu?.

Washegari muka fara aikin da ya kawo mu tukuru, aikin shine koyon yadda ake raba twins din da aka haifa a hade ta ka, yadda kowanne daga cikin su zai rayu. Kullum wuni muke yi a lab sai yamma likis sannan zamu dawo, kuma kullum muna dawowa zan tarar da abinci Sultan ya ajiye min, wani lokacin ma har da ruwan zafin wanka, sai yanzu na fahimci dalilin da yasa ya dauki spare key dina kuma inajin dadin yadda yake kula dani sosai, saboda badan shiba gaskiya zaman zai yi min wahala sosai, fita siyan abinci kawai sai ya isheni. Wani abin mamakin shine duk da cewa ni kadai nake zaune yanzu amma Sultan har yau bai taba kai hannunsa jikina ba, ko wani abu zai bani baya barin hannayen mu su hadu, na jinjina masa ta nan gurin sosai dan ba ko wanne namiji ne zai iya haka ba, wani lokacin har tunani nake "to ko he is not attracted to me?" Amma kuma in na kalli idonsa ina gani a ciki, wani lokaci har bana son hada ido dashi saboda irin abubuwan da nake karantowa a ciki, abinka da psychologist, lol. Watan mu daya a America wani aiki ya taso wa Sultan wanda ba zai iya yi tanan ba sai lallai yaje Nigeria, ji nayi kamar zanyi kuka har sai da ya gane yace to ya fasa tafiyar sannan na hakura. Kafin ya tafi sai da ya bada order a restaurant din da yake siyo mana abinci cewa kullum zasu ringa kawomin safe, rana, dare babu fashi. Yana tafiya muka dinke a waya, kudin da Sultan ya kashe a saka credit daga tafiyarsa zuwa dawowarsa Allah ne kadai yasan yawan su, koda yaushe muna tare a waya sai dai in zanyi waya da 'yan gida ince masa ya kashe kuma shima ana jimawa zai sake kira. Satinsa biyu acan ya dawo amma ji nayi kamar yayi wata biyu. Yana dawowa ya shiga lodo min siyayya yana ajiye min wai tsarabar da zan kaiwa 'yan gidan mu, nace "Sultan wannan uban kayan ya zanyi in tafi dasu?" Yace "shipping dinsu zanyi miki ai" na sake cewa "to yanzu in naje dasu gida ince da mommy a ina na samu kudin saye?" Na danyi tunani kadan sannan yace "tell her you won the lottery or something" kawai na saki baki ina kallonsa, shi a ganinsa wannan is a total excuse, shi bai saba in yayi abu a tuhume shi ba dan haka bashi da idea yadda za'a yi wa iyaye karya. Haka yayi ta lodo kaya yana jibgewa.

Sati daya ya rage mana mu dawo England, duk ayyuka sun yi mana sauki dan kusan zan iya cewa mun kammala, ana koya mana ne yadda za'a kula da twins din ana monitoring dinsu har su warware. Sai lokacin sultan ya samu damar fita dani yawon ganin gari, ai kuwa nasha gararamba lungu da sako na New York sai da ya shiga dani. A lokacin ne ya kaini gidan sa ya nuna min. Tun sanda yace min can zamu je na kudurta a raina cewa bazan shiga ba, muna zuwa yayi packing ya zagayo ya bude min kofa naki fitowa, ya tsaya yana kallona "ko sai na fito dake ne?" Nace "no kawai dai bazan shiga bane" in yayi mamaki ma ya boye bai nuna min ba yace "ohh really? Duk zirga2 da nake yi gurinki ke ko shiga ki saka min albarka a gida na baza kiyi ba? Thanks a lot" wani barin na zuciyata yace min, he is trying to control you, don't give in, na daga kafada nace "sorry, kawai dai naga kamar shiga gidan ka is way ahead of limit" shima kafadar ya daga yace "if you think so, amma matsalata guda daya ce, what I plan is in munzo nan zan barki anan zanje wani guri in karbo sako a gurin wani wanda gobe zai bar gari gobe kuma gurin da zamu hadu is no place for a lady especially lady din da ba zata iya shiga gidan fiancé dinta ba" na daga masa hannu nace "technically kai ba fiancé na bane yet" yayi murmushi tare da jingina da jikin motar yace "OK, yanzu ya kike so ayi?" Na kalleshi ya langwabar da kai side daya, na dauke kai a zuciyata ina cewa, don't fall for that, ya sake zagayo wa ta side din dana mayar da fuskata yace "na rasa me yasa har yanzu kin ki trusting dina, if I want something da tuni na karba, you are too precious for that, I just want you to see my house, nan shine inda na zauna for thirteen years, tun ina twelve years nake rayuwa a gidannan har na kai twenty five years" ba fito daga motar ina karewa gidan kallo, madaidaici ne, sama da kasa, da veranda a kofar gidan, gaba daya gidan a kewaye yake da flowers masu kyau. A hankali na tambayeshi "amma kai kadai ka zauna a gidan tun farkon zuwanka? Ina nufin girki da kula da gida" ya daga kafada yace "farkon zuwan mu akwai house help da driver da suke zuwa kullum, daga baya muka kore su muke kayan mu da kanmu, fifteen years na fara driving, Amir ya iya girku sosai, so we managed" na runtse ido na ina jin zafi a raina, sultan tun yana karamin yaro yake zaman kansa kuma a lalatacciyar kasa kamar America. Sultan ne ya dawo dani daga tunani na yace "look in baki yarda dani ba ga key ki bude ki shiga ki rufe kanki, just look around in na dawo sai mu tafi" ba kalleshi da tuhuma nace "how do I know baka da spare key?" Dariya yayi sosai yace "Wallahi bani da spare key, kinji na rantse miki dai" na karbi key din ina kunkuni na matsa baya, ya rufe kofar ya zagaya seat din driver ya shiga ya kunna motar yace "in kin shiga sama zaki hau, kasan anan friend dina yake zama, amma nace masa zamuzo dan haka ya fita" na gyada masa kai sai kuma ya tsaya yana kallona, na daga masa kafada alamar what? Yace "this is New York not Abuja, ki shiga ciki kiyi locking kofar sannan sai in tafi" Na turo baki na juya ina kallonsa yana yi min dariya har na shige cikin gidan na rufe kofa sannan ya tayar da motar ya tafi. Kallo daya na yiwa palon kasa na hau sama. Ina shiga wani katon hoton Sultan ba gani hannunsa rike da guitar fuskarsa da murmushi, akwai yarinta sosai a fuskarsa, na karasa gaban hoton ina kallonsa, na daga hannu a hankali na shafa fuskarsa ina jin wani sabon sonsa a raina, na shiga uku ni Maimunatu ya zanyi duk sanda aka raba ni da Sultan? Ba wani tarkace a palon amma kamar yadda nayi tsammani tas yake ko digon datti babu a ciki, na cigaba da kallon pictures din jikin bango, duk yawancin su shi da Amir ne, wani suna yara wani sun dan girma, gaskiya Allah ne kadai yasan shakuwar da take tsakanin Sultan da Amir. Wanj hoto ne ya dauki hankali na, Sultan ne da school uniform ana bashi gift a makaranta, gashin kansa a hargitse kamar wanda ya dawo daga filin dambe. So you are brilliant also. Na shiga bedroom dinsa naga gado ne kawai sai sif din kayan sa, na bude sif din a raina ina cewa kaima ai bude min kayana kake yi. Anan na saku baki ina kallo, sets din kaya ne sunfi karfin a kirgasu, a jere neatly, takalma, undies, p-caps abin ba'a magana. A raina nace dan gayu. Na koma kitchen naga babu kayan abinci amma akwai kayan electronics iri iri. Gaba na ne ya fadi da naga fridge, ko zan ga giya a ciki, a hankali na bude fridge din kamar mai taba wuta, na duba kaf banga alcoholic drink ba, na sauke ajjiyar zuciya na dauko orange juice na dawo palo na zauna ina sha.
Chapter 55 · 0% Book details