Sashe 97
Maimoon Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read
Na kalli cikin idonsa nace "I will never leave you, dama parents dina kawai nake ji, tunda yanzu na samu go ahead din su babu abinda zai saka in rabu dakai" a hankali yanayin fuskarsa ya fara chanzawa daga bacin rai zuwa murmushin da ya saka nima na fara murmushi yace "then I don't need anybody else" Mun dau hanyar gida again naji wayata tana ringing, na daga naga Mommy, ina dauka tace "ya akayi har yanzu baku dawo ba? Ku zarto asibiti mun tafi da Hafsat yanzu tana labor" a rikice ta katse wayar ina kallon sultan nace "Hafsat....labor... Hospital" nan take Sultan ya gane abinda nake nufi ya juya kan mota muka tafi asibitin da Hafsat take antinatal. A hanya na dauko wayata ina neman number, sultan yace "wa zaki kira?" Nace "Zayed" yace "No, ki bari sai ta haihu tukunna" na mayar da wayar na ajiye. Muna zuwa da sauri na fita na bar sultan a mota, a waiting room na samu Mommy da Amina, Mommy tana ta faman jan charbi. Na samu guri nima na zauna. Ba'a jima ba aka leko aka ce wata a cikin mu ta shiga ta zauna da ita, da sauri na tashi na shiga. Zan iya cewa tare muka yi laborn da Hafsat, in tana kuka nima sai in kama kukan, in tana addu'ah in taya ta. A haka mukayi ta fama har dare ya raba, Sultan yana ta kira yana tambayar jikin Hafsat, a lokacin na kara jinjinawa mata da irin wahalar da suke sha a gurin haihuwa, a lokacin kuma na kara jin haushin duk matar da zata haihu ta dauki dan taje ta yar, kuma na kara tsanar duk dan da zai ki yiwa iyayensa biyayya. Hafsat ba ta haihu ba sai da alfijir ya fara keyowa, ta rike ni gam tamkar zata ballani sannan ta haifo kyakykyawar 'yarta mace, ana goge yarinyar na karbe ta na rungume ina jinsonta yana shiga zuciya ta, Hafsat ba kunya babu tsoron Allah tana samun kanta tace in bata 'yarta, har nurses din wajan sai da suka yi dariya. Na dora mata ita akan cinyarta ta fara shayar da ita (shayar da baby a wannan lokacin yana taimakawa wajen tsayar da jini da kuma saukin fitar mabiyya, kuma yana taimakawa jariri wajan saurin koyon shan nono da wuri kuma wannan ruwan nonon na farko yana da matukar amfani a gurin jariri). Gari yana wayewa aka fito dasu dakin hutu, nan fa dakin ya cika da 'yan ganin baby, ina ta Allah2 in kira Zayed ashe har Sultan ya riga ni, Mommy da Daddy sai rige rigen daukan baby suke, Hafsat kam cewa tayi ayi mata allurar bacci dan tana son hutawa, tayi kwanciyarta a ciki mu kuma muka taho daya dakin muna ta hayaniyar mu. Bayan azahar sultan ya kirani a waya, ina fita na tarar dashi a mota ya ce min "shigo" ba musu na shiga, naga ya tayar da mota, nace "ina zamuje?" Yace "gida zan kaiki kije ki huta, jiya baki yi bacci ba throughout" nasan gaskiya yake fada dan haka na kira Mommy nace mata zanje gida in anjima zan dawo, ina zuwa kuwa na tafi daki na na kwanta sai bacci, ban koma asibitin ba sai da daddare muka tafi tare dasu asma'u da suka dage sai sunje sun ga baby ba zasu jira su dawo gida ba, muna zuwa Zayed ya kira daddy yake gaya masa cewa ya samu delay din flight dinsa amma dan haka daddy yayi wa baby huduba da sunan Mommy, Fatima Zahra, Mommy kasa rufe baki tayi dan murnar an yi mata takwara, kowa sai murna har Hafsat taji dadi sosai, Daddy ya karbe ta yayi mata huduba ya miko min ita, Amina ce tace "to Hafsat yanzu me zamu ke ce mata kenan, tunda dai ai mu ba zamu kira ta da sunan ta ba" Hafsat ta daga kafada, sai gaba daya suka juyo suna kallona, ni aka barwa zabi kenan, na kalli babyn sosai ina ganin tsantsar kyawunta na larabawa, nayi murmushi nace "Khairat, we will call her Khairat" a tare Daddy da Sultan suka juyo suna kallona, nayi kamar bansan sun gane me nake nufi ba, Mommy tayi dariya tace "perfect, yayi sosai, Allah yasa ta zama sanadin alkhairi a gare mu baki daya" nan kowa yace "Ameen" Hafsat ma murmushi take da alama sunan itama yayi mata dadi, sultan bai yi magana ba sam, ni kuma ban kalle shi ba, sai daga baya na lura ya fice daga dakin. A mota na same shi ya kwantar da kujera ya rufe idonsa kamar mai bacci, na zauna kusa dashi nace "in bacci zakayi ka tafi gida mana" ba tare daya bude idonsa ba yace "why Khairat? Why do you want her when she doesn't want me?" Bance masa komai ba saboda babu abinda zance masa, jin nayi shiru ya saka ya bude idonsa yana kallona yace "yanzu zaki tafi gida ne?" Nace "a'a, anan zan kwana ai" yace "OK, but ki tabbata kinyi bacci sosai, kar ki biye wa little Khairat" nayi murmushi na fita, na tsaya nace "good night" yace "good night love". Washe gari da safe aka sallame mu muka koma gida, a ranar kuma Zayed yazo. Sati yana zagayowa akayi suna, anyi taro sosai, kayan barkan da Sultan ya hado in wani ya gani zai iya tunanin shi aka yiwa haihuwar. Ana gama hidimar suna Mommy ta juyo kaina, tace yawo ya kare, babu inda zan ke zuwa. Shirye shirye ake yi sosai, dan har gyaran gida Daddy yayi, Amira da Amir sune chairman da chairlady din committee n shirye shirye, Sultan yace shi big wedding yake so, a cewarsa it will be the biggest day of his life, dan haka dole yayi celebrating. Ni nafi so ace anyi komai kadan amma mutane sunfi karfi na, dan anko sai Amira ta fitar da kala biyar, wai kowanne event sai anyi masa nasa ankon, kawayen mu na secondary school duk sai da Amira ta je ta gayyato su, ni dai ban samu damar zuwa ba saboda Mommy ta hana ni fita sam. Takanas Mommy ta dauko wata mata daga maiduguri wai zata min gyaran jiki, ni dai kawai jinsu nake dan banga abinda za'a gyara a jikina ba. Ranar farko da matar tazo muka shiga daki da ita, ta shiga toilet ta hada wani ruwa a tub, tace in cire dukkan kayan jikina in shiga ciki sai nayi awa daya tukunna, ina jin haka na dau waya ta da ear piece na je na shiga na kwanta na kira Sultan lokacin yana office muke ta hirar mu, ban ma san sanda awa dayar ta wuce ba, sai ganin matar nayi ta dawo da wani soso a hannunta, na yiwa Sultan sallama nace mata "wannan soson fa?" Tace "dashi zanyi miki wanka yanzu da wannan sabulun" na bata rai nace "ni zaki yiwa wankan?" Tace "eh, ai wannan ruwan da kika shiga kamar jika ki nayi yanzu kuma zan chuda ki ki fita tas" ni dariya ma abin ya bani, wato ana nufin duk wankan da nake yi ba fita nake ba shine yanzu za'a yi min wani. Bana son in gwale matar nace mata "OK, bani soso da sabulun, ni zanyi wankan da kaina" tace "ai ba zaki iya da kanki ba, anfi so wani yayi miki saboda zaki fi fita" yau naga rigima, ni kam babu yadda za'ayi in zauna kamar wata jaririya ayi min wanka. Ganin na dage da gaske nake ba zata yi min ba yasa ta fita ta kirawo Mommy, Mommy tana zuwa ta karba tace ta bata ita zata yimin da kanta, ai kuwa kam nasha durza kamar za'a ciremin fata, ni gani nake duk wahalar da ni suke yi suma suna wahalar da kansu, ban tashi sanin bani da wayo ba sai da na fito na kalli kaina a mudubi, gani nayi kamar wadda aka cire min fata ta aka saka min wata, a hankali nasa danyatsa na taba jikina, wani laushi da santsi naji jikina yayi. Ina fitowa kuma aka hada wani kaskon turaren wuta aka saka na tsuguna akai, wani irin kamshi ne mai tsadadden dadi yake ratsani, bargo matar ta saka ta lullube ni, sai fuska ta ce kawai a waje, sai da nayi 30 minutes a haka. Bayan na tashi kuma ta dauko wani mai ta bani tace duk in daina amfani da mayuka na sai shi kadai har lokacin biki na, kuma tace in na tashi shafawa a duk jikina zan shafa. A haka muka rabu da ita tace bayan kwana uku zata sake dawowa ta sake yi min wani wankan da turaren. A raina nace wannan me kuke so in zama kafin lokacin bikin? Ta kara jaddada min kuma banda fita rana, sam ba'a son rana ta taba ni.