Sashe 178
Maimoon Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read
hira har akayi sallar magrib, sultan ya fita masallaci mu kuma mukayi anan, tare suka dawo da Takawa, ni dai yana shigowa kaina a kasa na gaishe shi, ya amsa min sosai harda tambayata ya karin hakuri, na dago kaina na amsa masa "Alhamdulillah" and he smiled, this is the second time dana taba ganin murmushinsa. He looks different shima, he looks happy, har wani haske naga yayi da wani annurin fuska irin na angwaye. Tare muka ci abincin dare, ni dai duk a takure naji ni. Su kam hirar su suke yi sosai, Ummee sai dariya take yi, she looks so happy, basu da wani problem in the world, komai yayi farko yana da karshe, duk wata wahala da mutum yake sha a rayuwa mai wucewa ce, musamman idan kana kan gaskiyar ka, musamman idan baka zalinci kowa ba, to ka tabbatar cewa ubangiji yana sane da kai, kuma He has a special plan for you. Allah yasa mu dace. Muna zuwa gidan mu a palon farko na tarar da baba gaji da 'yammatanta, bakunan su har kunne suna murnar dawowa ta, gidan kal kal kamar banyi tafiya ba, ko'ina sai kamshi yake yi. Na zauna duk suka zo suka gaishe ni kuma duk na ambaci sunayensu, suka dauko kayayyaki na suka kai min dakina, zasu kawo min abinci nace musu na koshi. Anan palon na baje dani da cikina muna hutawa, sai da na gama hutawa sannan na tashi na tafi part dina. Ina tura kofar corridor naka duk fitulun gurin a kashe, amma kuma ga haske nan yana fitowa daga kofar da take facing dina, kofar dakin da sultan ya gina a matsayin our baby's room, ni dai a sani na dakin a rufe yake tunda aka kawo ni ba'a taba koda bude shi ba saboda babu komai a cikinsa. Na karasa na tura kofar naji ta a bude, ina shiga naji kida a hankali yana tashi, irin wakokin nan na lullaby. Ido na bude ina kallon dakin, exactly irin dakin da na taba gani a cikin system din Ummee a Riyadh. A zahiri ma sai naga yafi kyau akan hoton. Kadan ne ya rage ban saki kara ba saboda mamaki, hannuna yana rawa na dauko wayata na kira sultan, "sultan baby's room din nan yayi kyau sosai" yace "what baby's room?" Nace "gashi kuwa, an gama an saka komai" da sauri yace "wait a minute, gani nan zuwa" bai fi minti biyu ba sai gashi ya shigo, ina nan tsaye har yanzu a inda nake ina kallon dakin, komai na dakin blue ne, sai shades din ne wani mai duhu wani mai haske, an saka komai tun daga labulaye da capet, baby crib da drawers, da sofa guda daya da breastfeeding pillows a kanta, ga playpen da toys da yawa a ciki, baby swing, baby carrier, trolley, walker, feeders da starilizer, hatta tissues babu abinda babu a dakin, na karasa na bude closet din dakin, nan ma wani mamakin nasha, kayan baby ne fal a ciki, wadansu anyi hanging wadansu an jera su a lockers, kuma abin burgewar shine yadda akayi arranging kayan according to size, from newborn, sai 1-3 months, sai 3-6 months, 6-9 months, haka har 5 years. Diapers da wipes kuwa ina jin sai mun shekara bamu nema ba. Na juya na rungume sultan nace "oh sultan, it is beautiful" yace "I have no idea yaushe aka hada dakin nan" na dan cika shi ina kallonsa nace "nasan waye, Ummee ce" ji nayi kawai babu abinda nake so irin inga na haihu na fara kula da baby na, har wata kwallar dadi naji tana bin idona, ya ilahi, bansan ta inda zan fara gode wa Allah ba. Na saka hannu ina shafa lallausan bargon da aka shimfida akan crib din, a lokacin ne ido na ya hango pictures din da aka rataye a both sides din gadon, daga hannu dama hoton wani baby ne, na dauka ina kalla, sultan ne yana baby, with his red lips, ya tabe baki irin yadda babies suke yi in zasu yi kuka, dariya na kama yi, yazo ya karba shima yana dariya, na lakuce masa hanci nace "daga gani dama kai rigimamme ne kana baby" ya dauko picture din barin hagu shima yana kalla, ni ce nima ina baby, nayi murmushi dimples dina duk biyun sun lotsa, ya saka hannu yana shafa fuskata a hoton, nace "see? In dai babyn nan yayi rigima to kai ya dauko" ya ajiye hoton ya juyo yana kallona yace "idan kuma yayi surutu fa? Da shagwaba, da son jiki?" Nace "oho, wannan kuma bansan wa yayo ba" ya jawo ni jikinsa ya rungume ni ta baya yana dan juyi damu yace "kin san lissafi nake yi yau in kin huta gobe zamu fara shiga kasuwa siyayya?" Nace "ai mu yanzu 'yan gata ne, komai yi mana ake yi" ya yi murmushi yace "yeah, you are right. Ni fargaba ta daya, kada a haifi babyn nan su dauke mana shi su hana mu" nayi dariya nace "shikenan sai mu bar musu shi mu haifi wani". Hmmm kawai yace min. Na dauko waya ta nayi dialing number din Ummee, sultan ya gani yace "ke cikin daren nan zaki kira mata tana dakin mijinta" na harare shi, tana dauka nace "oh Ummee, it is beautiful" tayo dariya tace "har kun gani kenan, do you like it?" Sultan ya zuro kansa yace "we love it Ummee and we love you" ina jiyo dariyar Takawa a background, a raina nace 'dama yana dariya?' Ummee tace "we Love you too sweethearts. Yanzu saura abu daya ya rage" nace "Ummee komai komai ya kammala babu abinda yayi saura kuma" tace "akwai. Addu'ah. Addu'ah ita zamu saka yanzu a gaba muyi tayi ba dare babu rana. Allah ya sauke ki lafiya ya kawo mana new little love lafiya" sultan yace "what? Ummee sunana ne fa?" Tace "daga ranar da aka haife shi za'ayi maka retire, amma before then, you are still our little love, so enjoy it while it last" mukayi dariya a tare, tacigaba da cewa "maimunatu daga yanzu ki dage da cin dabino sosai, sannan kike cin abinci sosai kuma mai kyau wanda zai kara miki karfi da lafiya. Sannan abu na karshe ki tabbatar kullum wayarki tana kusa dake kuma ki tabbatar akwai kudi a ciki kuma akwai chaji. Hospital bag din ku tana gurina, na hada miki kayanki dana baby wanda zaku bukata a asibiti. Allah ya sauke ki lafiya." Sultan yace "Ameen" nima na fada amma a raina, ya karbi wayar ya kashe. Ranar a dakina muka kwana, sultan sai da ya karbi dukkan bashin daya ke bina, nima kuma haka, dan nima ina son mijina. Na kwanta a jikinsa ina shakar kamshin sa da nayi missing kwana biyu, ya taba cikina da yake ta mutsu mutsu yace "kai fa na lura kiriniya ce da kai, to ka sani, wannan wasan bana yara bane ba, ga playpen dinka can Ummee ta sayo maka da toys dinka, sune abokan wasan ka ba mu ba, idan Mommy da Daddy suna yin wani abu yara basa zuwa gurin" nayi dariya ina shafa kansa nace "idan bai yi kiriniya ba ai sai Allah ya tambaye shi" ya dan bata rai yace "yarinyar nan naga alama kinga gurin kwana na shi yasa kika raina ni, zanyi maganin ki ne, dan kinka yanzu ina dan daga miki kafa ko? I will be back to my normal self and sai kin raina kanki" kafin muyi bacci na tambayi sultan "wai Ummee ta dade a garin nan ne har ta shirya dakin can?" Yace "watanta daya da sati daya a Nigeria yanzu" sannan ya bani labarin abinda ya faru bayan tafiyar mu daga Riyadh.