← Book details Maimoon Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 144 OF 190

Sashe 144

Maimoon Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

dana gani a office din Ibrahim, she looks so happy, yanzu ta zama marainiya babu uwa babu uba because of me, sultan da yake ta faman kula da marayu kullum maganar shi bata wuce ta marayu yau muguwar zuciyarsa da bakin kishinsa ya nawo yayi making marainiya da kansa. Kuka nake yi sosai inajin ciwon kaina yana karuwa. Muryar Mommy naji tana cewa "Haba Moon, kukan menene kuma wannan? Daga rashin lafiya sai kuka? BP dinki ne fa ya hau idan baki daina kuka ba kuma tayaya zai sauka?" Daddy ya kalli sultan yace "kace a kitchen ta fadi ko?" Sultan ya dan kalleni kadan sannan ya gyada kansa ba tare da yayi magana ba, Daddy yace"amma menene zai sa BP dinta yayi wannan hawan haka? Bai taba hawa kamar haka ba" Sultan ya sunkuyar da kansa fuskarsa kamar zai yi kuka amma sultan never cries, Mommy tace "may be zafin kitchen ne dear, dama masu hawan jini ba'a so su ringa kusa da wuta sosai" Daddy ya karaso ya rike hannuna yace "maimunatu kukan me kike yi?" Kafin inyi magana sai ga doctor ya shigo, yana murmushi yace "finally ta farka ashe, ya jikin?" A hankali nace "da sauki" yace "menene kuma na kuka? The pregnancy is intact ai, munyi nasarar tsayar dashi bai fita ba" a tare Mommy da Daddy suka ce "pregnancy?" Na juyo na kalli sultan naga gaba daya fuskarsa tayi fari tas kamar babu jini, ya juyo da sauri ya kalle ni, na kalli su mommy naga gaba daya hankalinsu yana kan doctor yana musu bayani, na gyada masa kai nace "shi yasa nace ina son chocolate din" hannu biyu ya saka ya rike kansa, Mommy naji tana magana cike da fara'a tace "I suspected as much, bana son in saka rai ne ko ba haka bane inzo inji babu dadi shi yasa na dora wa zafin kitchen" doctor din ya gama yi musu congratulations ya fita, Sultan har yanzu kallona kawai yake yi sannan da sauri kamar wanda aka jawo ya taho gurina, kara na saka da duk dan karfin da ya rage min, wannan ya jawo hankalin Mommy da Daddy kaina, Mommy ta taho da sauri kusa dani tace "lafiyar ki kuwa? Ciwon kan ne?" Na nuna Sultan nace "kar ka karaso inda nake, it is over between us" cikin muryar abin tausayi yace "Moon dan Allah kar kice haka, bazan iya rayuwa in babu ke ba mutuwa zanyi please" nace "then so be it" bai hakura ba ya sake taku daya, na dunkule hannuna na daga dai dai kan mara ta nace "kana kara wani takun zan fitar da abinda yake cikina in baka kayanka" a tsorace ya tsaya, he looks scared, I have never see Sultan scared tunda na san shi. Mommy ta rike hannuna da sauri tace "baki da hankali maimunatu? Me ya hada ku haka?" Fuska ta babu alamar wasa kwata kwata, na kwace hannuna daga hannun Mommy na kuma dagawa a saman mara ta, da sauri sultan ya ja baya, yanayin fuskarsa kadai ya isa ya saka mai karamar zuciya ya fashe da kuka. Daddy ya tafi kusa dashi yana cewa "Sultan me ya faru?" Bai amsa ba ya juya da sauri ya fice daga dakin. Yana fita na kifa kaina akan pillow na fara rera kuka, Allah kai kasan me kake nufi damu, Allah ka shiga lamarin mu. Ko kadan abinda Sultan ya aikata bai chire min ko digo na soyayyarsa daga raina ba. Amma abinda na fahimta shine; Sultan is too hard for me to break, diamond ne shi kafin a narka shi sai anyi amfani da ice da fire, I have used the ice bai yi min amfani ba, now I have to use the fire. Daddy ne yazo ya zauna kusa dani yana shafa kaina yace "Maimunatu talk to me" na dago kaina naga Mommy tana ta sharar kwalla, na runtse idona ina tuna duk abubuwan da suka faru a ranar, na kwalli agogon bangon dakin naga 3:30 na dare, hakan yana nufin an dauki hours da yin abin, hakan yana nufin Ibrahim yayi spending hours a cikin ramin day fada, wani kukan ne ya taso min, na dora kaina a kafadar Daddy nayi mai isa ta sannan na share hawaye na, tiryan tiryan na basu labarin duk abinda ya faru, na karasheda wani kukan "yanzu Daddy sultan ya kashe Ibrahim, ya zanyi? Shima hukuncin kisa ne akansa in aka san maganar nan, idan kuma nayi shiru ban fada ba kuma kamar na daure wa cin zali gindi kenan, ya zanyi Daddy? Mommy ki taimaka min" Mommy ta jawo ni ta rungume ni tana kuka tana salati "mun shiga uku mun lalace ni Fatima" Daddy kuma cike da mamaki yace "waye shi Ibrahim din ne?" Mommy tace "wannan copper din da yake sonta da a makaranta" Daddy yace "That yaroba guy?" Kai kawai na gyada masa, yace "a dai dai ina abin ya faru? Kamata yayi muje first mu dauko shi, maybe yana da rai yana bukatar taimako, in ma bashi da ran kamata yayi ai muje mu dauko shi" nayi musa kwatance ya mike yace "bara in nemi sultan shima inji me yake ciki, I don't want him hurting himself kuma" na girgiza kaina nace "he won't. He would want to see his child". Tunda Daddy ya fita babu wanda yayi magana ni da Mommy, kowa da abinda yake zuciyarsa. Mun jima sannan naji Mommy ta fara yi min magana, ga mamaki na maimakon inji tana fadan abinda Sultan yayi sai naji tana addi'ar Allah yasa babu abinda ya sami Ibrahim. Muna cikin haka wayar ta tayi kara, ta dauka tace " wannan number ce ma babu suna, waye zai kira ni cikin daren nan kuma" ta daga tare da sallama, take naga yanayin fuskarta ya chanza, tace "Amina slow down kiyi min bayani yadda zan gane. Kina ina?" Ta jima tana sauraron Amina tana kuma kallona, na mike zaune ina jiran inji abinda ake gaya mata, tace "OK, kinyi kokari sosai Amina, ki zauna anan inda kike bara in kira daddyn ku in gaya masa" ta kashe wayar, bata yi min magana ba sai tayi dialing number din Daddy tace "ba sai kunje gurin ba dear, su Amina sun dauko shi sun tafi dashi general hospital. Yes, he is alive, zan yi maka bayani later" ta kashe tana kallona, wata ajjiyar zuciya na saki na koma na kwanta, duk da bansan details din me ya faru ba amma na fahimci cewa Ibrahim is alive, wannan information din kadai ya isa ya kwantar min da hankali. At least Sultan is safe now, amma kuma dole zai fuskanci hukunci daga gurina, sam ba zan yi masa da wasa ba, he must learn to control his temper especially yanzu da zamu fara ajjiye zuri'a. Daga baya Mommy tayi min bayanin cewa ashe duk abinda ya faru a store Amina ta gani, taga fitowa ta da kuma fitowar Sultan, bayan ta fito itama waje sai taga tafiyar mu a guje, sai kuma taga Ibrahim ya biyo bayan mu shima a guje, shine taji tsoron kar wani abin ya faru ta hau taxi tace yabi yaban mu, munyi musu nisa dan haka basu ga sanda abin ya faru ba amma sunga motar mu tana juyowa amma bata ga ta Ibrahim ba, suna zuwa gurin suka ga alamar anyi accident, ita da mai taxi suka fito sannan suka ga inda motar Ibrahim ta fada, mutane masu wucewa ne suka taimaka masu aka fito da Ibrahim, lucky for him shima ya saka seatbelt kuma motar sa akwai airbag dan haka bai wani ji mugun ciwo ba amma still he is unconscious, sun kai shi asibiti an kaishi emergency. Gari yana wayewa Daddy ya shigo, ya gaya mana cewa har lokacin Ibrahim bai farfado ba amma doctors din sunce he is stable. Sultan daga bakin kofa ya tsaya yana kallona, kallo daya nayi masa na dauke kaina gefe, ya gaji da tsayiwa ya juya ya fita. Da la'asar aka sallame ni, direct gida aka nufa dani, naji dadin haka dan dama ina ta addu'ar Allah yasa kar Daddy yace a mayar dani gidan Sultan. Shima kansa Daddyn naga ya hade wa Sultan rai sosai. Muna zuwa gida Daddy ya saka ni a gaba yace "zaki dan zauna a gida Moon, hakan ba yana nufin zan raba ki da mijinki ba, a'a, so nake mijinki ya gane cewa abinda yayi ba dai dai bane, for him to think cewa zai iya daukan ran mutum koma me mutumin yayi masa is very bad. Zaki koma amma sai na tabbatar da cewa something like this will not happen again" na share hawayen ido na nace "na gode Daddy" yace "yanzu so nake dake ki nuna masa kuskurensa sosai, kar ki raga masa ko kadan. Ke ce abinda yake so fiye da komai a duniya, kuma yana takama ne cewa kina sonsa, show him you can leave him in dai har ba zai iya controlling kansa ba" na gyada kai na sake cewa "na gode Daddy". Dakina aka gyara min, na shiga ina karewa dakin kallon, I never thought zan kuma dawowa dakin in kwana a ciki. Dare yana yi nayo alwala nazo na fara jero salloli ina godewa Allah daya ta kaita abin, sannan kuma ina sake neman guidance dinsa akan abin da na saka a gaba na. Na duba agogo naga karfe daya da rabi na dare, na kashe fitila na zauna akan gado ina kallon kofar balcony, I know he is coming, and I pray for God to give me the strength to do what I plan to do. Ban jima a zaune ba naji ana taba kofar, sannan aka bude ta, duk da cewa dakin da duhu bai hana ni gane shi ba, ya jima a tsaye yana kallona amma ya kasa cewa komai, nace "me kazo yi nan?" A hankali ya karasa shigowa dakin yace "Maimunatu dan Allah ki tsaya kiji abinda zan gaya miki" nace "me zaka gaya min, a gaba na kayi kokarin kashe mutum, you almost make me miscarry our child" da sauri yace "how can you say that, ke ma kinsan bansan dashi ba" nace "how can you say naje store ne dan in hadu
Chapter 144 · 0% Book details