← Book details Ƙayar Ruwa 2&3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 99 OF 113

Sashe 99

Ƙayar Ruwa 2&3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

A hankali na taka na shiga daga ɗakin da yake da girma sosai a gyare tsaf da shi, sai ƙamshi yake yi ga tiles ɗin ɗakin fari amma ko jurwaye babu a kansa har ɗaukar ido yake, ko anan a tabbatar da tsaftar matar gidan, idan wata ce yanda ba ya zama ai sai tiles ɗin sun rine, ba zata tashi gyara ba sai zai dawo, wannan kuwa da gani goge shi ake akan kari.

Ina tsaye ina raba idanu ya shigo, ya tako inda nake ya ɗaga hijabina ta baya ya cire shi ya faɗi ƙasa, ya saka hannayensa ya zagaye ƙuguna ya ɗora kansa a kafaɗata yana cewa,"Wannan fushin duk akan kishin Salim ne?".

Yanda yayi maganar a kunnena ya saka naji wani yarrr a jikina, na runtse idanuna sai naji yayi murmushi ya sake ni ya dawo gaba yana kallona yace,"Ashe haka kike sona da yawa ban sani ba?".
Kai na sunkuyar, ya É—ago fuskata yana cewa,"Bana son wannan sunkuyar da kan da kike fa, ki kalle ni ki faÉ—i abinda yake ranki, ko É—azun na yi maganar da bata yi miki daÉ—i ba?".

"Ni babu abinda yake raina". Na faÉ—a a hankali ba tare da na bari mun haÉ—a ido ba.
"Akwai, ni nasan akwai wani abu a nan". ya faɗa yana ɗora hannunsa a ƙirjina yana kallon fuskata. "Ina jin bacci". Ya waro ido da faɗin,"Bacci? Baby bacci a wannan daren! Ko kin manta wanne dare muke ciki ne?".

Nayi shiru ina faman lumshe idanu kamar me jin baccin gaske, sam ganinsa da maganarsa ne bana so, muka isa bakin gado ya zaunar da ni saman cinyarsa, hular kaina ya zame ya shiga shafa wuyana, nan take na fara jin wani sabon yanayi, lokaci guda kuma na ruɗe jin yanda ya ƙanƙame ni yana aikin shinshinar jikina yana faɗin idan ina sa irin wannan humran kullum to zan janyo a sallame shi daga aiki ne, don zai koma aikin kan gado till down.

Maimakon naji daɗi ya ratsa ni da furucin nasa sai ɓacin rai ya ƙara wanzar min, ya zo ya gama min surutai yaje can itama wata me ƙatuwan murya ya karanta mata irinsu. Sai ga hawaye riii a saman kuncina, mamakin kaina kawai na ke yi, ban taɓa tsammanin ina da kishi haka ba, ba zancen son kai ba ne kana matuƙar kishin abinda ka ke so ne, na kasa dannewa kuma, ban san ta ya zan iya danne kishina ba tsakani da Allah, fatana ɗaya kar ta sanadina na haifar da zaman da ba zai yiwa kowa daɗi ba.

Sannu a hankali lamarin ya fara sauyawa, na san komai amma sai na ji kaman ban san komai ɗin ba, ba wai don ba a yi min irin salon a baya ba, a'a abubuwan da yake min ɗin ne cikin irin nasa salon na shi kaɗai daban da irin wanda na sani ne, jikina duk ya ɗauka rawa tun ba'a je ko'ina ba har ina neman shiɗewa. Shi kuwa tuni ya gama susucewa da ƙyar ma ya iya zuwa ya kashe fitilan ɗakin, haka ya koma min tamkar wani mayunwacin zaki, na miƙa ragaman jikina gaba ɗaya wa Salim da ya bi ya susutar da junanmu, tuni ya canja labarin da ya sha banban da wanda na ke tunanin zai afku, kuma babban al'amarin ya faru ne bayan shimfiɗuwar lamarin da ya tafiyu cikin natsuwa da gwanancewa, haƙiƙa jin kaina na ke tamkar a yau ne karon farko da na fara shiga duniyar da sanin irin daɗin da ke cikinta.

Ni ɗin ba sabuwa ba ce amma a yanda lamarin ya afku jina nayi tamkar yanzu ne aka ɓare ni, an tsumu, zuciyoyi da ruhi sun samu natsuwa, gangar jiki duk ta mace a cikin shauƙin daɗin da ta tsinci kanta, fitar numfashi da saukarsa kawai kake ji. Yana daga gefe nima ina daga gefe, ya tattaro ni ya janyo ni jikinsa ya ƙanƙame abarsa, ni kuwa sai faman sauke ajiyar zuciya na ke ina faman goga hanci da goshi a gashin ƙirjinsa.

"Myyy". Ya kirayi sunana cikin wata irin shaƙaƙƙan muryan da zan iya rantsewa ba nasa ba ne, yana ta aikin yawo da hannunsa a dukka ilahirin jikina.
"Thank you Baby, thank you so much, God bless you".

Haka yake ta faman jera min kamar wanda ya samu sabuwa fil a leda, kamar wanda ya shekara aru aru bai samu ba tsaban gulma, sai bayan wani lokaci kafin mu tashi mu shiga toilet mu tsarkake jikinmu.

[2/2, 07:47] Hlm: *B3ƘR15FT5*
Tun bayan sallar asuba da na kwanta na ke bacci a jikinsa, ƙarar alerm ne ya tashemu inda muka buɗe ido a tare, hasken ranar da ya shigo ta siririn buɗawan labule ya haske min ido, ya kai hannunsa yana kare min, sannan ya miƙe ya isa gaban window ɗin ya gyara labulen.
Dawowa yay ya kwanta yana mayar da kaina saman ƙirjinsa, muka haɗa ido da shi sai nayi saurin kulle idanu tare da kamo hannunsa na rufe fuskar tawa. dariya yayi da hakan yana cewa,"Baby gulma, mene ba ki sani ba to da zai saki jin kunyana".

Murmushi kawai nayi ba tare da na ce komai ba, sai ya miƙe zaune yana ɗaukar wayarsa, ganin tafiyar lokaci ya buɗe ido da cewan,"Subahanallah! Ashe haka lokaci ya tafi". Ina kallonsa na ce,"Har ƙarfe nawa dama?".
"Sha É—aya fa Myy, wanne irin bacci muka yi". Sai kuma yay murmushi yana shafo fuskana da cewan,"Ko da yake ai laifin ki ne".

Na É—an juya idanu farr da cewa,"Laifina kuma?".
Sai da yaja hancina tukunna yace,"Ehh mana, daÉ—in da aka jiyar da ni da kuma natsuwar da aka bani".

Idanuna buÉ—e ina kallon fuskarsa ba tare da na bari mun haÉ—a ido ba na ke shafa gashin gefen fuskarsa da cewa,"To kai ma ai ka bayar".

"Ummm na sani ai, shiyasa aka saki baki da hanci ana ta zuba munshari duk aka hana ni bacci".

"Kaiiii Salim ban da sharri dai".
Leɓena ya ɗalle da cewa,"Ai ba sani za ki yi ba, lokacin ma da kika ƙanƙame ni kina kar na sakeki please continue its very sweet ai duk ba ki sani ba".

A jikinsa na tusa fuskata ina ta murmushi cike da jin daɗi. Shi kuma yaci gaba da duba wayansa, waya ya kira ina jin yana magana akan tafiyan da za su yi in the next 5days, za su tafi can America ne da shugaban ƙasa akan tattaunawan da aka yi na ƙasar zata taimakawa Najeriya kan harkan tsaro.
Bayan gama wayar tasa attention nasa ya bani gaba ɗaya muna ta hiran mu cike da so da ƙaunar juna, a hiran namu kowanne ke bayyanawa ɗan uwansa irin abinda yake so da wanda ba ya so, yana ce min zai bani babban makamin mallakarsa gaba ɗaya, na buɗa dukka kunnuwa ina saurarensa cike da zaƙuwa kuwa.

Sai da ya fara manna min kiss a baki kana yace,"Idan kina so ki mallake ni totally na zamar miki raƙumi da akala to ki so Ƴaƴana, ki riƙe su tamkar ke kika haife su, ba na son ki nuna musu banbancin mahaifa, ko a bayan idona ban yarda ki hantare su ko muzguna musu ba...then".

Sai yay shiru, zuciyata dai na ta motsi cikin wani irin rauni da tayi, ina kallon ƙwayar idonsa na ce,"Then what?".

Sai da ya sauke numfashi, ya kamo kafaɗuna ya tayar da ni zaune muka fuskanci juna yace,"Ni mutum ne mara ɓoye ɓoye da barin abu a raina ina kallon mutum da shi. Ki sani ina darajta matata, ban ƙaro aure don bana sonta ba, ban ƙaro aure saboda tana da wata makusa a gare ni ba, ban mata kishiya domin ta gaza ba, ban mata kishiya don na wulaƙantata ba... Kuma ba ina faɗa miki hakan ba ne saboda ɓata miki rai ba ko kuma ke bana sonki ba, no! Bana so kiyi amfani da wata damar ne na ganin kamar kin fita a wurin miji ki samu hanyar cuzguna mata, duk ku biyun ina son ku, so da ƙauna ne yasa na aureku na ke fatan kuma har a aljanna mu kasance tare, dole son wata zai fi na wata amma wannan abu ne kawai da ke iyacin cikin zuciyata gudun haifar da fitina a gidana, ina sonki itama kuma ina sonta, Baby please ki controlling zuciyanki, ki iya sarrafa kishinki kamar yanda ƴar uwarki ta sarrafa nata. So'ida a ƙabilarmu idan ka ce zaka ƙara aure tashin hankali hakan ke zame maka tsakaninka da iyalinka, amma tunda na tunkari Kudrat da zancen aurenki zuwa kawoki da nayi ban fuskanci wata aba damuwa ba, hakan yasa ta ƙara samun girma a idanuna, ba wai bata kishina ba ne ta danne ne kawai, kema don Allah ki danne abinda na gani jiya a reaction ɗinki da ƙwayar idonki, if kika ce zamu tafi a haka to zamu samu matsala da ke sincerely speeking, fatana matana su haɗe kansu, ku zama abu ɗaya, ba faɗa ba gaba, sai kun fini jin daɗin zaman ma, duk kuwa wadda ta tayar min da fitina tabbas she will see the other side of me".

Zuciyana na zafi kamar zan saki kuka na ce,"To yanzu duk mi É—aya ka faÉ—awa haka?".

"Yanda na karanta miki haka na karanta mata, shiyasa jiya na jima a wurinta har hakan yay sanadin da kika ƙullace ni a ranki, Baby kar ki bari zuciyarki ta rinjaye ki please, kike kaudar da duk wani abu da ba ki da tabbas akansa, kishi dole ne amma kiyi kishin wayayyu masu ilimi irinki".

Hawaye ne ya sakko min, ina wasa da yatsuna na ce,"Insha Allahu zan so yaranka, zan riƙe su kamar ni nayi tsugunon haihuwarsu, and zan zauna lafiya da matarka, ba zaka taɓa samun matsala ta ɓangarena ba nayi maka alƙawarin hakan mijina".

Sai ya kwanto ni jikinsa yana shafa kaina yace,"Na gode matata, na gode da kika fahimce ni, nayi miki alƙawarin zan samar miki da farin ciki da dukkan iyawata, zan kuma iya bakin ƙoƙarina wajen ganin ban haifar da ɓacin rai ko damuwa ba a tare da ke, alƙawarina ne kuma ba zan taɓa bari ki zubar da hawaye ta dalilina ba ko ta dalilin wani nawa".
Chapter 99 · 0% Book details