← Book details Ƙayar Ruwa 2&3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 74 OF 113

Sashe 74

Ƙayar Ruwa 2&3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Jin haka na turo baki gaba ina haɗe gira sama da ƙasa na nufi soro ba don son raina ba, sai dai me! da zuwana soron naji gabana yayi mugu mugun faɗuwar da sai da na kai hannu na dafa bango, haka kawai na tsinci ƙafafuna da yin karkarwa. Da ƙyar na dawo hayyacina daga fitar da nayi daga cikinsa na ɗan lokaci, domin kuwa ƙamshin turaren da ya gauraye dukka soron da kuma tsadaddan takalmin da idona ya sauka akai sai ya nemi ya burkita ni.

Na haɗiyi yawu ina cire takalmana a kusa da wanda na ke gani, ƙafafuna suka ɗaga da kansu suka shigar da ni ciki, da yanayina na sanyi nayi sallama da ƴar ƙaramar muryar da zata ɗauki hankali ko ai'na ne, kamar wata sokuwa haka na maƙale a bakin ƙofa kaina a ƙasa na kasa sarrafa kaina saboda yacca na ke jin ido ya manne akaina da kallo.

A karo na biyu na ƙara cewa,"Salamu alaikum". Ban sani ba ko an amsa a wannan lokacin domin kuwa kunnena a toshe yake dumm haka na ke ji a cikinsa tun ɗazu.
Wucewar bugun zuciyata sau ɗaya, biyu, uku, huɗu naji kamar babu motsin halitta a ɗakin saboda haka na ɗago ido a tsorace, karaf ƙwayar idona ta sauka akansa da yay saurin sadda nasa kan ƙasa kamar ba daga kaina ya sauke kallonsa ba.

Zaune yake a gefen katifa, ya miƙe ƙafafunsa da na gansu dogaye, hularsa da ya cire ta yare a gefensa, yana wasa da yatsun hannunsa, kallonsa na ke da son na fahimto wani abu sai ji nayi na mugun tsorata dalilin jin ance,"Ga wani abu nan wajen ƙafarki".
Ƙara na ƙwalla, kuma maimakon in yi waje sai na faɗo cikin ɗakin ba tare da sanin yanda aka yi na dira a tsakiyar ɗakin ba, idona rumtse jikina sai kyarma yake, cikin bakina ina faɗin kalmar la'ila ha'illa anta a hankali, saboda tsananin tsoro da furgicin da na shiga har hawaye na sakko min.

Na jima a haka na kasa buɗe idanuna, sai naji kamar an rufa min abu akaina wanda hakan yasa ni buɗe idanuna a hankali, sai naga mutum tsaye a gabana, faffaɗan ƙirjinsa yay min rumfar na zama kamar wata ɓeranya a gaban nasa ƴar firit, a hankali kunnuwana ke jiyo min sautin bugun zuciya wanda na tabbatar da haƙikanin ba nawa ba ne nasa ne, sai naji wani dunƙulallan abu ya wuce ta maƙoshina gabana na tsananta faɗuwa sosai, so na ke tayi na ɗaga ƙafata na matsa daga baya amma ina kamar akan tarko na maƙale sam na kasa motsa ƙafata ko guda ɗaya.

Cikin wani irin yanayi da na ke jina a cikinsa kasantuwar kusancinmu, na yi saurin ɗauke idona daga kan ƙirjinsa da na ke mamakin faɗinsa ina kai wa saman kamilallar fuskar da ta ƙawatu da kewayayyen saje me haɗe da gemu. Kuma karaf ƙwayar idon mu ta sarƙe ata juna, lokaci guda naji jiri na neman ɗibana ya watsar, nayi saurin dunƙule hannu ina riƙe kaina a tsayen, irin murmushin da ake kira da killer smile ya saki wanda sautinsa yay sanadin girgizawar allon ƙirjina nayi saurin ɗauke ƙwayar idona daga cikin tasa, ban saba da irin wannan kusancin ba sam da wanda ba muharramina ba, don haka kaina na ƙasa ina rawan jiki na shiga ja da baya yayin da ya daɗa kiɗima ni da amon muryarsa da ya fito lokaci ɗaya da cewa,"Am sorry ban tsammaci za ki tsorata da yawa haka ba, nayi hakan ne domin ƙafafun da suka maƙale wuri ɗaya su samu takowa zuwa ciki".

Ina micincina idanu na ce,"To baka san ko a addinan ce babu kyau tsorata musulmi ba".

"Tuba na ke yi ba zan ƙara ba daga ranar yau, amma ki sani kina da me ba ki kariya kar wani abu ya ƙara tsorata ki".

Ni dai ja nake da baya har na zube kan ƴar ƙaramar plastic chair ɗin ɗakin ƙirjina sai faman sama da ƙasa yake yi. So na ke na ɗaga ido na kalla fuskar da na yiwa kallo ɗaya saboda na tabbatar da zargina. Sai kuma ringtone ɗin iphone ya cika ɗakin, wanda da sauri naga ya matsa daga inda yake ya isa katifar ya ɗauka, sai jinsa nayi yana magana cikin wani irin yare kamar jagwalgwalo babu daɗin ji, duk sai naji maganar tana hawar min saman kai har ta kai ga na rufe ido ina gwame fuska.

"Ina wuni".
Da sauri na buÉ—e idona ina dawowa cikin duniyar da na bari jin murya a gaf da ni, na kalle shi muka haÉ—a ido sai na kasa É—auke kallona a kansa gaba É—aya kuma na diririce. Zuciyata ta amsa da sunansa,"Salim!".
Mutumin da na sani shekaru goma sha da suka wuce, mutumin da watannin baya da suka wuce naga hotonsa a album É—in bikin Safiyya.

Naja numfashi inda na haɗe da ƙamshinsa da ke tsumani na zuƙe, sannu a hankali ƙamshin turarensa ya ɗebe ni ya kaini tunanin germany, sauka a airport, cikin napep. Ba tare da sani ba kawai na tsinci bakina da furta,"Kai ne?".

Sai naga ya É—aga gira dukka biyu yana kallona kawai, kafin yace,"Ai na?".

Na tsuke gira ina tuna komai daki daki na ce,"A airpot ranar da na dawo, da kuma ranar ma a adaidaita".

Sai ya lumshe ido yana girgiza min kai alamun a'a. Na ɗan duki ƙafa a ƙasa na ce,"A'a wannan ƙamshin ne".

Ba zan ce ga da irin muryar da nayi magana ba don ba zan iya tantancewa ba, amma sai naji ya kwaikwayi muryan da cewa,"Ba wannan ba ne, irin wannan É—in ne".

Kawai sai kunya ta kama ni na kai hannu ina rufe fuska, har ga Allah nema na ke na kasa controlling kaina ba don komai ba sai saboda ƙamshinsa da shi kansa da cikar haibarsa tayi gama gama da ɗakin musamman da yake zaune a gabana.
Dariya naji yayi ƴar ƙarama yana maimaita gaisuwar da yayi. Sai na ɗan saci kallonsa, ni ya kamata ace na gaida shi ai to amma ta ya zan samu sakewar hakan mutum babba na zaune a gabana kamar yarona?

"Ba za ki amsa ba?".

Sai na samu kaina da cewa,"Ai kana zaune a gabana kuma ni ya kamata na gaishe ka".

"Ni dai a amsa mini domin kuwa cancantar Sarauniya ne da isarta a duƙa a gabanta a gaida ita, musamman ga mutumin da ya zo da ƙoƙon bara".

Tsintar kalamin nasa nayi har ɓargo da jijiyoyin jikina, kuma kafin na ankare sai gani nayi ya haɗe hannayensa alaman roƙo gami da ɗan karayar da kai yana cewa,"Please a amsa min, domin a ƙage na ke da na miƙo ƙoƙon barana bani a karo na biyu".

Baki na buɗe ganin yacca yay da fuska kaman ƙaramin yaron da ke shagwaɓar ayi masa abinda yake so. Sai ya miƙo hannunsa yay kamar zai zura yatsa cikin sakakkun laɓɓana nayi saurin kauda fuska gefe cike da kunyar da ta kama ni, domin kuwa surar fuskarsa ce ta ɗauki a hankali, kallon da ban samu damar yi masa a wancan lokacin ba, dama wannan kyan ne Safiyya take ta faɗa min? Amma kuwa idan haka ne Allah ya saka masa domin me hoto ma ya rage masa kyau sosai da sosai.

Yunƙurawa nayi zan tashi yay saurin dakatar da ni,"Please koma ki zauna". Ya faɗi hakan yana gyara zaman tanƙwashe ƙafafunsa tare da mayar da yanayinsa na masu magana da gasken gaske.
Sai na ce,"To don Allah ka tashi a gabana".

Wani kallo yay min yana sosa gira sannan yace,"Ni fa ki ƙyale ni a yanda kika ganni, ki zauna kawai muyi magananmu, ba dafa ki zanyi na cinye ba, in ma zan yi hakan tukunna dai. Muhimmiyar magana ce ta sani na ke zaune haka a gabanki saboda haka koma ki zauna, idan kuma salon zaman ne bai ba sai na gyara".

Ya faɗa yana ƙoƙarin miƙewa ya dire gwiwoyi a ƙasa. Da sauri na shiga girgiza masa kai ina cewa,"A'a du Allah".
Komawa nayi na zauna kamar me koyon zaman, shi kuma ya shafo fuska yana girgiza kai kafin yace,"Zan iya sake gabatar da kaina?".

Kai kawai na kaÉ—a masa alaman ehh. Da yanayin barkwanci yace,"Awwa Allah sa dai kar ki ce wannan ya fiya naci kamar in mammake shi".

Furucin ya ban dariya na ɗan dara kafin kuma na haɗe rai. Kuma sai ji nayi yace,"Ki gama haɗe haɗen ranki indai za ki buɗen ƙofa shikenan. Anyway kamar yanda na faɗa miki a baya ne My name is Salim Sadiq Oluwa, ni ɗan ƙabilar igbo ne.....".

[2/2, 07:47] Hlm: *B3ƘR07FT5*
Ina kallonsa ya miƙe tare da jan kujera baya ya bar wajen, haka na bi bayansa da ido kamar me shirin tashi ta bisa, har ya ɓacewa ganina ban ɗauke ido ba, sai daga baya na kulle idanuna ina kifa kai saman dining table ɗin, wannan ne irin son da yake faɗi? a haka zan yi auren ana min famin ciwo? A hakan ake cewa za'a mantar da ni baya? A haka za'a cika alƙawarin?
Ji nayi na ƙoshi da abincin da na ke ta marmarin ci, me yasa ma zan damu da shareni ɗin da yay? Bayan hakan ban san me ya tsaya min a zuciya ba har na ke jin ƙunci da ɓacin rai. Tashi nayi na bar wajen, toilet na shiga na wanko fuskata nayo alwala jin ana yin kirayen sallar la'asar, ina idarwa na ɗebi kayana na bar gidan ba tare da na yiwa Safiyya sallama ba tana can sama, ni ba zan wani tsaya sauraronta ba balle ta ƙara ɓata min rai, haushinta ma na ke ji.
Chapter 74 · 0% Book details