← Book details Ƙayar Ruwa 2&3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 18 OF 113

Sashe 18

Ƙayar Ruwa 2&3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Muna isa gida muka tarar jikin Abbaa ba yanda yake, Yayyuna suna gefensa sai firfita suke masa, Ummani tayi jugum a gefe É—aya ta zabga tagumi tana kallonsa, kana kallon fuskarta kaga na wacca ta sha kuka ta gode Allah. Wai ashe kwanansa huÉ—u yau a kwance, saboda kar na san da ciwon aka ce min wayar Ummani ta lalace, Su Yashaik suka amshe don kar zuciyarta tayi rauni ta faÉ—a min, hatta Abbayoma ya zo shi da yake can garin damaturu amma ni da nake nan aka gagara sanar da ni rashin lafiyar mahaifinmu saboda kar a É—aga min hankali, a ganina ba'a min adalci ba sam.
Haka na isa gefen kan mahaifin nawa na zauna ina kamo hannunsa na riƙe, bai gane ni ba kwatata kwatata, ga dai shi idonsa akaina yake ashe ba ya gani yau ne ma idon ya ɗan buɗe masa amma jiya da shekaranjiya duk ba ya gani. cikin kuka na ke jera masa sannu ina cewa Abbaa ka yafe min don Allah. Sai da yaji muryata ya gane wacece, duk da a tsananin ciwo yake amma sai ce yay,"Me yasa kika zo alhalin wa'adin lokacin da na ɗauka maki bai cika ba, karo na biyu da kika take maganata Sa'ida". Yay maganar a wahalce.

Ni dai kuka kawai na ke yi, shi kuma cikin zafin ciwo faɗi yake na tashi na tafi gidana. Sai da Kaka yay magana kana yay shiru ya haƙura. Har bayan isha'i muna kan Abbaa, ciwo babu wani sauƙi har cewa yake a ƙyale shi ko yanzu ya tafi ai ya mori duniyar kuma dama kullum cikin jiran cikar lokaci yake, muyi masa fatan dacewa da rahmar ubangiji kawai, sannan mu haɗa kanmu Yayyuna su kula da ni, kuma mu riƙe mahaifiyarmu da kyau.
Wannan furucin nasa ya daɗa tsinkar da zuciyoyinmu, mazan ne kawai suka yi ƙarfin halin riƙe hawayensu a hakan ma ban da Abbayo, ni da shi kuka muke haiƙan. Sai wajen tara na dare ciwo ya lafa masa har bacci ma ya ɗauke shi.

A É—aki Ummani ke faÉ—a min ai tunma a ranar da ya fara ciwon aka kira Nazifi, aka ce kar ya bani aron wayarsa ma na kira gida, mamakin da tayi da har yanzu bai zo ba kuma waya ma bai kira ba, don É—azu ma da ana neman kuÉ—in da za'a yi masa scanning na hanta Yashaik yake cewa ko shi zai kira ya tambaya aron kuÉ—i sai ta hana.

Ko kirana bai yi ba yaji daga gare ni, ban san dalilin ma dana sa a raina cewa zai kira ni ɗin ba. Washe gari da safe sai gashi ya zo, yana bawa su Yashaik haƙuri wai ayyuka ne suka sha gabansa shiyasa, duk yanda ya so ya yakice ba yanda zai yi. Da zai tafi ya ajiye musu kuɗi Ummani tace ba za'a karɓa ba tasa Abbayo ya ɗauka zai mayar masa, ni kuwa na karɓa nace ba za'a mayar ba tunda dama cikin buƙatar kuɗin ake, Don yanzu haka wata allura aka rubuta dubu goma Yashaik da Yaya Imam na can sun fita nemo kuɗi.

Ranar cikin dare a lokacin ƙarfe uku, ina tsakiyar sallah wayata ta shiga ƙara, bayan na idar kuma ina jan carbi ta ƙara yin ƙara na kai hannu zan kashe zatona alerm ne, ashe kira ne na ɗaga ma ina tunanin kashe alerm ɗin nayi, sai daga nesa nesa na ke jin kamar ana kiran Sa'ida, wayar na ɗauka da zummar kunna fitila na haska na fita ko Ummani ce ke kira, sai naga ashe a wayar ne kira ke tafiya.

Tsaki nayi na kashe kiran na koma kan sallayar, kiran ya ƙara shigowa raina a ɓace naja tsaki na ɗaga,"Ina jinka lafiya kira ya wannan lokacin kamar wanda ke bina bashi".

Muryarsa na shaida tsananin damuwar da yake ciki yace,"Muna asibiti ne Zahrau ce ke naƙuda, kin ganmu tun tara amma har yanzu shiru. Shine na kiraki don Allah ki sakata cikin aduarki, na san sallah kike yanzu. To don Allah kiyi mata adu'a sosai kin ji bana so wani abu ya sameta ita da yaran".

Nayi shiru zan sauke wayar a kunne yace,"Don Allah Habibty, kinga shekara cikin ta goma da aure sai yanzu Allah zai bani haihuwar nan, ko ba don ita ba kiyi saboda mijinki, nima kar kiyi don ni kiyi saboda Allah Habibty".

Ido na rufe ina jin wani abu na tasowa a ƙirjina, a hankali na ce,"Tom zan yi saboda jalla wa'azza, Allah ya sauketa lafiya. Ka kwantar da hankalinka kaima ka natsu kayi mata adu'ar".

A sanyaye ya amsa da,"To nagode. Na so ma ace kina nan, ya jikin Baban na ku da sauƙi ko?".

Ban amsa shi ba na kashe wayar na ci gaba da ibadata ina roƙawa mahaifina lafiya da kawo mana sauƙi cikin halin babun da ake, Haka kuma na haɗa har da ita me haihuwar nayi musu adu'a.
_____________________________________
*Gwarazan Labarai na ƙarshen shekarar 2023 masu ma'ana.*

*KWANTAN ƁAUNA*
Nana Haleema

*ƘAYAR RUWA*
Halimahz

*LOKACI NE*
Oum Mumtaz

*FARGAR JAJI*
Aisha Yabo

*WASA DA RAI*
Fadila Yakubu

Ɗaya ₦500
Biyu ₦800
Uku ₦900
Huɗu ₦1000
Biyar ₦1200

*Biyan Kuɗi Ta*👇🏻
6314170140
Fidelity Bank
Sa'adiyya Zakariyya Haruna

*Shaidar biya ta👇🏻*
09061794195

*Godiya tare da adu'an fatan alkhairi ga wanda suka sami damar mallakar littafanmu, son So fisabilillah🥰*

#TeamFitattuBiyar
[2/2, 07:47] Hlm: *B2ƘR08FT5*
_Hohoho wani girkin sai wajen macen da ta san kanta🥳 yo ai idan ana faɗar kalmar ƙamshi da ɗanɗanon girki sai dai mu ce a garzaya Spicerite.ng. Amarya da Uwar gida me kuke ta jira har yanzu ku ka kasa hargitsa tunanin Oga da kasa natsuwa har sai ya baro aiki ya dawo gida ya kwashi girki? Hajjaju na ce to ai ƙamshin kaɗai ma ya isa ki mallake Oga da shi, wannan sabon sirrin mallaka ne na ke baki😉amma fa idan kin inganta girkinki kawai ta hanyar amfani da kayan ƙamshin da ke ƙarawa girki armashi aji ƙamshin abinci har a maƙota😋, wai wai wai daɗi mazaƙwai ba Oga ba kaɗai hatta baƙin da suka zo suka ci girki sai sun ƙara satar hanyar dawowa don kawai su sake cin haɗaɗɗen girkin da aka yi amfani da sinadaran girki na spicerite.ng...wato spicerite.ng lamba ɗaya a fagen sarrafa maku kalolin ganyayyaki masu ƙara lafiya domin ƙawata girkinku💯...ba anan kaɗai ba kazalika sun sauƙaƙa maku hanyar sarrafa kayan girki da dama, irin su garin ɗan wake wanda ruwa kawai za ki zuba masa, niƙaƙƙen yaji, garin alala da ƙosai, niƙaƙƙen daddawa, garin kuka, kuɓewa da dai sauran su. Amarya da kike so kiyi zarra a cikin gida Uwar gida ta kasa gane da me kika mallake Oga maza tuntuɓi wannan lamba 08147302739 domin fara girki da kayan ɗanɗanon abinci na spicerite.ng ko kuma ki aika da saƙo ta shafin su da ke instgram @spicerite.ng._
__________________________________
Baccin yammar da bai saba kwatata shi ya ɗebe shi bayan sun gama gurzar soyayyarsu, da ƙyar Zahra'u ta raba jikinta da nasa ta tashi tana jin jikinta duk ciwo, nan ta fita ta barsa ko motsi bai yi. kuma ba shi ya farka ba tun bayan la'ar sai da aka fara kiran magriba Zahra'u ta zo ta tashe shi. A da sabon sa ne bai baro masallaci sai anyi isha'i amma tun da ya auri Zahra'u ba ya izama, ana idar da magriba zai dawo idan anyi isha'i ya ƙara komawa, lazimi da sauran karatunka da ya saba yi duk ya watsar.

Yanzu ma ko da ya dawo daga masallacin a ƙa'ida ɓangaren Sa'ida zai wuce, tun da dama shigar lokacin kowacce bayan magriba ne, amma sai yay tsaki fuskarsa na nuna ɓacin rai, sam bai son komawa can, shi da zata taimaka ma ta amince da ya jingine aurensa da ita, zai bata maƙuden kudaɗe, bacin haka ma yana duba abu ɗaya ne shiyasa yake zaune da ita har kawo yanzu, amma shi ganinta ma bai son yi kuma a wajensa batta da amfanin komai tun da har ta gaza samar masa da ɗa, yana ta faman tsaki ƙasa ƙasa ya ƙara komawa ɓangaren Zahra'u.

Ko da ya shiga ɗakinta bai sameta ba don haka ya fito ya nufi falonta, can ya iske su ita da su Inna Zulai da Iftihal, Inna Zulai ta sakata gaba da cewar sai ta tattaka yawan zaman da take yi ya isa haka kam, ya kamata take motsa jiki ko dan ta samu sauƙi wurin haihuwa. Ganinsa ɗin ita kuma ta shagwaɓe fuska tana yin narai narai da idanu, Innar ya gaida su Iftihal ma suka gaida shi kana ya juya ya koma, cikin ransa yana ta adu'ar Allah yasa kar Inna ta hana Zahra'un fitowa tun da tasan yau ya fita a wajenta.

Yana tsaye ya tsurawa ƙofa ido sai gata ta shigo, ya saki ajiyar zuciya yana tafiya wajenta cikin nuna jin daɗi da ɗoki kamar wanda ya shekara bai ganta ba, rungumeta yay yana kai hannu cikinta, idonsa a rufe yake cewa. "Ina tsananin son ku, kune farin cikina, kune rayuwata, kune komaina, Allah yay miki albarka Swty, Na gode Na gode da ƙoƙarinki na samar min cikar muradina, Allah ya sauke ki lafiya, Allah ya kula min da ke da abin da za ki haifa min".

Sai ya zameta ajikinsa yana tallafo fuskarta yana ƙarema kyawunta kallo. "Nayi miki alƙawarin rabin dukkan abin da na mallaka, sauran kuma na abin da za ki haifa min ne, ni bana da buƙatarsu, babban buƙatata haihuwa kuma na sameki kin sama min ita a lokacin da na fidda tsammanin samu, don haka kin gama samuna da ni da dukkan wani abu da yake mallakina. Ina sonki so mai girma".
Chapter 18 · 0% Book details