← Book details Ƙayar Ruwa 2&3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 111 OF 113

Sashe 111

Ƙayar Ruwa 2&3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Kallonsa nayi duk don yaji bakina ne fa, ai ya san wanda ya lalata musu ɗin, so yake nayi magana yace ba wani nan rashin adanin yaran ne, alhalin Foridat na iyaka ƙoƙarinta akan adana abinsu, amma Ayman da fitina bai barin masu komai, sun kunna abar suna kallo ya ɗauki lemu ya sheƙa musu akai, kuma ko a jikinsa bai san ma me ya aikata ba, ai kuwa ya ɗalu a wurin Forida. Kudrat ta ce da ni bakinmu alaikum ya tasu.
To yanzu da zai ji an daki Ayman ɗin mun shiga uku da faɗa, Forida kuwa sai ya iya bugunta ƙila ma yace ba zai gyara musu ba ita ɗin ma ba zai siyo mata sabuwan ba, ba ya so sam a taɓa masa Ayman, shi ke ƙara tunzura shi ma yayta cewa,"Yayi Oga soja".

ÆŠaukan Ayman yayi suka fita, ba jimawa ya dawo shi É—aya, ya kuma É—aukan Umarul Faruq ya fita da shi, ai ganin hakan na fahimci inda ya dosa, haka zai kwashe su duk ya kai É—akin Yara. Ya dawo yana faÉ—in,"Wai ba ki gama ba shi ba ne".

Don in tsokane shi na ce,"So na ke ma ya gama sha na bar maka shi in tafi aikina, yau eba na ke so na mana, kar ɓomo ɗin can da na jiƙa ya lalace".

Killer smile yayi yana hayowa kan gadon, kuma kamar Ajmal É—in ya sani ya saki nono. "Kin gani shi ma yaro ya san lokacin Babansa yayi, ita ma Eba sai ta jira a sallami me gidan".

Yana dawowa ya faÉ—a kan gado tare da jawo ni jikinsa, nan da nan kuma labari ya sauya salo. Naga alama so yake in kuma É—auka tun ban yaye su Umarul Faruq ba.

*Bayan Shekara Bakwai.*
Ƙaramar ball ɗin da tayi shawagi a sama ta faɗo ƙwal a saman fuskar mutumin da ke zaune bakin Sahad Store na Mandawari kano. Ya dafe fuska cikin jin zafin buguwan, kuma kafin ya kai hannu ya kama ball ɗin ta gangara ta kifar da kwandon kayan gyaransa, kayan duk suka watse a ƙasa.

Ba zafin ƙwaluwar ba ma, bin hanya ya bibya tsinto kayan alhalin mutane na ta faman wucewa, wani ma sai ya take shi bai lura ba. Ya ɗago ransa a ɓace yana kai dubansa ga ɗan ƙaramin yaron da ya doka ball ɗin, Rofi'a da ke tsaye kusa da ƙanin nata tayi ƙwafa tana gyaɗa kai ta shiga ƙwala kiran,"Mommy! Mommy! Mommy!".

Hankalin Sa'ida yay can bata jita ba ma, sai da Isi'oma ta taɓota tana cewa,"Mommy kinga yaran can ko, kalle su fa acan baya, Mommy wai haka kullum za muke tafiya sai mun yi nisa muke ganinsu a baya, a ke barin su a gida kawai".

Na ɗaga kaina don kai dubana gare su sai na jiyo Rofi'a ɗin na cewa,"Mommy Ayman ya ƙwalawa me gyaran takalma ball".

Raina ya ɓaci sosai, na rasa irin Ayman sam ba ya ji indai akan ball ne, nayi faɗan nayi har na gaji, kawai duk wurin da ya samu doka ball yake da dogayen ƙafafunsa irin na Babansa, kuma ba'a isa azo fita ba sai ya saka rigiman lallai sai da ball ɗinsa zai fita, a hana shi a rasa kwanciyar hankali da faɗan ubansa, na ce hakan ba kyautuwa ba ne yace babu ruwana kar na ƙara hana masa yaro yin abinda yake so.

Kuma har yana cewa Ayman ɗin ka doka ball ɗinka duk inda ka ga dama, wanda ya fasa taɓa min ɗa bai cika isashshe ba, kayi ball a inda kake so Babanka soja ne Kakanka Soja ne Yayan Babanka soja ne kaima kuma soja ne.

To wa ya san yanzun ma ko yana wajen, tunda ajiye mu kenan da yayi mun dawo daga rakiyan Ummani da Abbaa airpot za su tafi Umaran da na biya musu. Shi ne ya aje mu nan in yiwa yaran su Yashaik siyayya zai je gidan sarki ya dawo sai mu wuce, yau ɗin muka shigo garin kuma kai tsaye filin jirgin muka wuce, da yake shekaranmu biyu kenan da komawan mu can Abuja, tun ma da muka koma ɗin bamu wani zazzo kano ba tun bayan rasuwan Kaka, Allah sarki Kaka har yau mutuwarsa na taɓa ni, duk da an sha zaman duniyar.

Cike da takaici na girgiza kai na kalli Isioma nace,"Kula da yaran nan ina zuwa". Na faÉ—a ina tafiya na barta da Umarul Faruq da Ajmal.
Ai fa tunda ya hango tahowata ya falla a guje yay jikin wani mutumi ya ƙanƙame shi, ga fitina ga shegen tsoron bala'i, idonsa duk yay wurƙi wurƙi ai ya san dole ma sai na murɗe masa kunne, yanzuma yasa hannu ya rufe kunnuwan dama haka muke da shi. Ni ban da yaci sunan Abbaana ma ai zane masa jiki zan ke yi.

Mutumin ya É—auke shi yana dariya da jin sha'awan yaron a ransa, Rofi'a kuma sai dariya take yi na mugunta dama sun saba a tsakaninsu, shi yay mata dariya idan irin hakan ta taso itama tayi masa, gata dai da Æ´an uwanta mata amma sun fi shiri da shi, duk wata kitumurmura tare su ke yi, in ce an dai ji kunya Yayar kawai.

"Mommy wallahi ki zane shi, sai da ina ta ce masa kar ya buga kar ya buga yaƙi jina, da zan ƙwace ma yace min sai ya faɗa ni da Paapa, ni kuwa na ƙyale shi don na san faɗan Paapa, haka kawai ya zo yana cewa kar in ƙara bugun masa ɗa, dama duk an fi sonsa ai".

"Ina wanda ya bugawa ɗin?". Na tambaya idona akanta ita ɗinma kamar na kwaɗeta, ba damar mu fita sai suke tsayawa a baya, kuma har a gaba zan tasa ƙeyarsu amma kafin na farga sun zilla sun koma bayan, sai mun ci uwar tafiya kan in ankare Isioma tace min,"Mommy ga Tom and Jerry ɗin can a baya".

Rofi'a ta kai hannu tana yi min nuni da mutumin da ke tattara kayan gyaran takalman nasa yana maida su cikin kwandon, sai naji tausayinsa ya kama ni don da gani yana cikin wani hali na neman taimako, amma ɗan albarkana ya daddage ya buga masa ball, abar da take da shegen zafi ni kaina ranar da ya ƙwalo min ita sai da na kusa ƙwalla.

Na gyaɗa kai ina niyyan in tafi inje in basa haƙuri sai kuma dai na fara tunkaran wajen wanda ya ɗauka Ayman, haka kawai ban sansa ba bazan bar masa yarona ba, wani abu ya faru na zo na shiga uku, ubansa ma sai yay min bulalai ya ɗaure ni, ya haka Family sakat sai an nemo masa ɗansa.

Muka gaisa da mutumin yana cewa,"To ya za'ai ai haka yara suke sai haƙuri, kar ayi masa faɗa please kuma kar a duke shi, zai daina wataran, bari naje na bawa shi mutumin haƙuri".

Kaina na ƙasa na ce,"Shikenan na gode".
Ya tafi tare da Ayman ɗin wai ma don kar ya bar min shi in duke shi, yana riƙe da shi a hannunsa, na bi bayan mutumin da ido har ya kai ga wajen me gyaran takalman.

"Mommy É—auke ni". Ajmal ya faÉ—a cikin nasa rigiman, ba zai barni na huta ba ai, ya girman ma shi bai yarda da kowa ba, shi ko Umarul Faruq dama indai da Isioma bai da damuwa.

Na duƙa zan ɗauke shi daidai lokacin kuma da Nazifi ke ɗago kai ya kai dubansa ga Babar yaron da mutumin yaje basa haƙuri yay masa bayani, me idanunsa za su gane masa? Kamannin da ba zai taɓa mancewa ba ne ba fa, fuskar da ya ke ta son gani ce fa, a wani razane yake kallonta har ya kuma yar da kwandon gyaran takalman suka watse a ƙasa, baki a buɗe ya kasa rufewa.

Zuciyarsa ta shiga harbawa fat fat kaman zata fito waje, kafin a hankali laɓɓansa su haɗe da furta sunan Sa'ida. Tambayan farko da ya fara shiga ƙwaƙwalwansa ita ce,"Yaran waye a hannunta?".

Kuma kamin wata tambayar ta sake gifta masa idanunsa sun haska masa kamannin yaran maza dukka uku a cikin idanuwansa. Ba sai ya nemi ƙarin bayani ba, kuma ba sai an faɗa masa ba, ko makaho ya shafa yaji ya san wa'annan kyawawan yaran maza tubarkalla masha Allah na ta ne. Kawai sai ya tsinci saukar hawaye a saman kuncinsa, haka yaji ƙafafunsa na neman gaza riƙe shi, yay saurin ja da baya yana jingina da bango.

Rayuwa kenan, wacca ya wulaƙanta ya tozarta ya gorantawa ita ce ke tsaye haka a gabansa, gata nan ta zama mace cikakkiya mai aji da ilimi da wayewa, wadda ta taka matsayin da shi bai taka ba, kallonta yake daga nesa kallon da ya san tafi ƙarfin ya isa wurin da take, da dukkan nuni ta samu kowanne kalar cigaban rayuwa da ake nema, shi kuma ga shi cikin wata rayuwa na halin ƙaƙa na ka yi, halin rayuwar da cin yau ke masa wahala balle na gobe, godiyarsa ɗaya ma ya samu Allah ya jiƙansa ya sawwaƙe masa manyan basukan da ke kansa, banda haka yana jin da zuwa yanzu kam yana can bursun zaman da babu lallai ya fito.

Ya kai hannu ya share hawayensa, ba kowa ya tuna ba sai mahaifiyarsa wadda Allah yaywa rasuwa shekarar da ta wuce, kuma a yanzun haka ya tuna da lokacin da suke tare da Sa'ida ne, irin kulawar da ta bawa mahaifiyarsa abar ƙaunarsa, irin hidimar da ta yi mata, saɓanin matar da ya sake aure wacce zai iya cewa ita ta zama silar ajalin mahaifiyarsa, don ita ta zubar da karkashi bata gyara wajen ba Iyam ta zo ƙofar ɗaki tana ƙwala masa kira, sai Marawiyyan ta fito tana mata rashin kunyar da ta saba, dama bata girmama mahaifiyarsa sam yo auren ma da ƙaƙa aka yi, ita ta aure shi ma don bai da kuɗin auren, to haka kullum take cikin jawa uwarsa kunne na kar ƙara zuwar mata gida tana kiran ɗanta, idan son ganinsa take ta dinƙa kiransa a waya ya zo gida ya sameta.
Chapter 111 · 0% Book details