Sashe 104
Ƙayar Ruwa 2&3 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Ina cikin wata na takwas Salim ya biya mana saudiya, lokacin za'ai aikin hajji, duk bamu san da tafiyar ba sai da ya rage saura satika, ni dai kamar an tsunduma ni a aljanna haka naji, ita kuwa Kudrat da ke ta jajje normal taji ta. Wallahi tsabagen farin ciki ban iya bacci ba a ranar, kwana nayi ina godewa Allah na, kwana nayi ina zabgawa Salim adu'a, godiyan farin ciki har da su kuka. Yace min,"Mene na kukan kuma, in dai saudiya ne yanzu kika fara zuwanta ke dai Allah yaci gaba da buÉ—awa".
Kudrat ita da yaran suka fara tafiya amma banda Rofi'at tunda ita a wurina take, ni da shi sai da muka biya ta kano, sai fa lokacin na zo gida tun auren, duk sanda nayi maganar zanje sai yace na bari sai ya samu hutu me yawa sai ya kai ni da kansa naje in yi kamar two weeks, tun ina maganar ina nacin har ma nayi fushi na daina, Ummani ma da na ke mata ƙorafi take ƙara nanata min auren daa sai afi shekara ma ba'a je gida ba.
Zuwan nawa kuwa ba ƙaramin farin ciki iyayena suka yi da ganina ba, musamman ganin na ƙara canjawa kamar ba Sa'idan da suka kai ba, ƴan uwana ma farin cikinsu ba zai misaltu ba. kwana na huɗu ina zazzagawa dangi da ƴan uwa da abokan arziƙi, gidan Safiyya na fara zuwa na yini sai dare ya zo ya ɗauke ni, da yake shi a gidan su Safiyyan yake kwana, naje gidan Hassana Tijjani da Maimuna, duk wanda ya ganni sai yay sha'awata sai yay min murna. Satinmu ɗaya a kano jirginmu ya ɗaga zuwa ƙasa me tsarki, la'ila ha'illah Allah ya kira duk wani musulmi zuwa wannan ƙasa, ni ban ma san ta yanda zan musalta muku irin daɗin da na ke ji ba, wani irin sanyi me daɗi da shauƙi zaka ji yana ratsa jikinka tun a jirgi, a sanda ƙafafunka kuwa su ka taka ƙasar ji zaka yi gaba ɗaya yanayinka ya sauya, Allah Alhamdulillah, godiya gareka a bisa tarin ni'imomin da ka yi min, a can muka samu su Kudrat su har sun buɗe ido ma don satin su guda.
Na ziyarci ɗakin Allah, na ɗaga hannu nayi kuka nayi kuka, ba kukan rashin wani ahu ba face zallar farin ciki, kuka na ke na tsantsanin farin cikin ganina a gaban ka'aba ɗakin Allah, ga ni gata ina taɓata, Ya Allah! Hawaye kuwa da yana ƙarewa tabbas zai ƙare a sanda na ke gaban ka'aba.
A duk sanda na je ƙabarin manzona da kuka na ke barin wajen, ni kawai ji na ke kaman in ƙare rayuwana a gaban wajen, ko da mutane zasu dinga tattake ni suna bi ta kaina, in sallamar in ƙara yi bana gajiyawa. Mun yi aikin hajji lafiya lafiya sai fatan Allah ya karɓi ibadunmu, ai kuwa na yi adu'an Allah ya bani halin da zan kawo Abbaa da Ummani wannan waje, haƙorin makka ai har biyu na saka, wai muna bidiyo da Safiyya ce take to farin shiga kar dai ki dawo mana kina faman yaƙe haƙwara, Ummani ma tace Hajiya Sa'ida haƙorin ya ƙara miki kyau sosai.
Watanmu guda curr da É—oriya muka fara haramar tafiya, har ga Allah da ni na kawo kaina wallahi ba zan tafi ba, ai nan kuma naga wurin zama, kuka har da su majina zan bar saudiyya.
Da saudiya kuwa Dubai muka wuce direct, kaman a zuwa ne Kudrat suka wuce gida najeriya, ni da shi da Rofi'at kuma muka wuce dubai ɗin yace kamar yanda ya kai Kudrat nima hakan ne. Ai ko dai mun yawata a dubai, tun da muka je ba zama kamar wadda taci ƙafar kare, har ce masa nayi dama a can Saudiyan ka bar ni wallahi.
Dubai ma fa ba dai kyau ba, arziqi me daɗi, inda kuɗinka ka sha shagalinka, haka na dinƙa bugawa Salim ƙauyanci yay ta dungure min kai yana ƴar madobi kawai. Ni kuwa da na samu sake a wurinsa bai hana ni fita ai sai na nemi wuce gona da iri, ko yana gida saɓar Rofi'a na ke mu fice inje in ta sakar laɓɓa ina ganin dogwayen gine gine, in ta jido siyayyan kaya yanda na ke kwasan abaya kun ce sana'arta zan fara, haka na yita yawon buɗe ido sai dai muyi waya da shi in ce ina wuri kaza.
Aikuwa a sati ukun da muka yi a dubai nayi wani fari kamar me shafa mai, fatana tayi sulɓi sai kace hutu na ke samu, ni dai to ban huta ba sai in ƙasar ce ta amshe ni, yo ban zama ina naga ta zama, yawo kullum ina kan hanya, yay ta mitan in barsa ya dirji soyayya a yanda ya samu hutun aikin nan, nace enaa ai soyayya ka jira mu koma delta, haka yake haƙura sai daren nan amma da safe da rana ina can na tafi galantoyina ni da ƴata, nayi wata ƙiba yanda ku ka san ina shan sha ka fashe, shi kansa Salim sai da yace ko sai yanzu Kunun Tamba ɗin da kusan kullum muke break fast da shi ya fara bin jikina, tunda yana saka ƙiba mutum yay mulmul da shi, Kudrat ƴar sharri har da cewa ko dai surgery naje aka min a kumatu suka yi luhu luhu haka kamar fanke.
Sai da muka yi sati huɗu ciff kafin mu ɗakko hanya, ina ta ce masa yaywa Allah ya tattaromu mu dawo Dubai da zama, me ake da wata lanjeriya, ya biye min kawai da cewa,"To! mu dawo nan ku ga bayan ATM ɗina ko, ko da yake dama ai ga ƴan naija ɗin nan suna ta tahowa aikatau, idan kun ƙarar da ni sai in koma shara da wanke wanke tunda salery ɗin da yawa".
Nace,"Allah ya rabaka ya kiyaye". daga nan nace a bar zancen, sai yay ta dariya.
Bamu wuce delta direct ba sai da muka sauka a kano na kaiwa iyayena da ƴan uwana tsaraban Makka da Dubai, aike har da Hassana Tijjani, Salim ya kyauta min muka je har wudil wajenta, ranar tayi farin ciki nima kuma nayi, don gaskiya Hassana tana da matuƙar kirki. kwananmu biyu a kano sannan muka wuce gida. A tsaraban da na yo zan iya cewa gidan su Salim in har a cikin gidan kake ko da tsinke ne kai to ka samu tsaraba daga wurina, kowa yaji daɗin karan da na musu sai cewa suke Allah ya maida ni don na iya tafiya.
Shekarana ɗaya da wata biyu da aure na fara shirin tafiya ƙaro karatu, kamar yanda muka yi da Salim dama yace min ba zai hana ni ba idan ina so, sun yi maganar ma da Abbaa, ko ina na ke so zai ƙyale ni naje kamar yanda ya bar Kudrat itama lokacinta.
Da muka yi waya da Ummani take cewa,"Sa'ida me yasa ba za ki bari sai gaba kya ɗora ba?". Nace,"Ummani ai gwari in yi in wuce wurin kawai, shekaru ƙara tafiya suke, kayi da ƙwarinka zai fi, kuma wata ƙila yanzu ne damar tawa".
Tace,"Haka ne, to Allah ya taimaka ya bada sa'a".
Harvard University ita ce makarantar da na zaɓa, da naji kuɗin makarantar sai da na razana, na cewa Salim,"To ko dai kawai na haƙura nayi anan?".
Yace,"Babu komai Allah zai yassare, zan yiwa Sir maganar yana da hanya, zai samar mana insha Allah".
Nayi farin ciki sosai, Salim ya ƙara ƙima a idona. Sai a lokacin ma na ke basa labarin wancan lokacin ma da na tafi wani bawan Allah ne ya ɗauki nauyinmu, yace,"Allah sarki ai kuwa ya kyauta haka ake so masu shi su dinƙa aikin alkhairi, sai Allah ya daɗa buɗa musu, Allah ya saka masa da alkhairi".
Na ce,"Amin Mahbub, wallahi ka ga ni dai har yanzu duk adu'ana sai na saka shi a ciki, ko da muka yi aikin hajji ma Mahbub sai da na ta faÉ—awa Allah na ce ya yalwata dukiyar bawansa kuma ya dawwamar da shi a farin ciki da kwanciyar hankali, yay masa sakayya da gidan aljannah".
Yay murmushi da cewa,"Allah ya amsa Myy kin masa adu'a me kyau, haka ake so ai mutum kar ya zama me manta alkhairi".
Na ce,"Wallahi dai wanda yay maka gata haka ina zaka manta da shi, mutumin da ya kawo maka canjin rayuwa, banda silar ina ni ina taka matakin da na kai. Ni dai Mahbub ka ga har sadaƙa ina yi masa fa, wainar da kaga ina sadaƙa duk friday gare shi na ke cewa Allah ya isar da ladan ai ban iya kuskure ba ko?".
A lokacin kawai sai naga ya dire laptop ɗin da yake dannawa ya rungume ni, ni dai na jima bai min runguma irinta ba, yay shiru kamar me bacci ina ta shafa kansa ni kuma, don naga kamar natsuwa yake so ya samu da hakan, sai can tsawon wani lokaci tukunna na kira sunansa sai ya sake ni yana cewa,"Allah yay miki albarka Baby, na gode sosai da sosai Allah ya jiƙan mahaifanki ba don sun mutu ba, ki ci gaba da masa adu'a da sadaƙan Allah ya amsa ya raba muku ladan".
Na tambayi shi adu'an fa na mene, sai ya manna min kiss yana cewa,"Na soyayyanki ne, Allah ya raya min ke in ga auren Rofi'a".
Nan fa na gyara zama na shiga karanta masa wata wasiƙa kamar yarinya, wai zancen tanadin auren Rofi'a na ke tun yanzu yarinyar da gaba ɗaya shekaranta biyar ne.
Shi kuwa sai ya kama dariya yana,"To ko Babar Forida ita me shekara goma sha huÉ—u ma bata fara zancen aurenta ba sai ke, sannu kin ji".
Ina jina a cikin nishaɗi nace,"Ita Babarta ba sonta take ba, ni kuwa ina son ƴata, saboda haka ka buɗe asusun tari tun yanzu kafin nan da lokacin da zan aurar da ita ka tara min da yawa, Mahbub tsinke ba zan siyawa Rofi'a anan ƙasar ba kaji ma da kyau".
Yay dariya kawai yana cewa,"To Myy Allah ya bamu aron rai da lafiyar kaiwa lokacin, insha Allahu za'a yiwa ƴarki komai kike so, ai Allah ya hore sai dai mu roƙe shi ya ƙaro mana".