Sashe 34
Ƙayar Ruwa 2&3 Complete Hausa Novel · about 8 min read
"Barta tayi baccin ko ya ya ne zata ji sauƙi a jikinta tunda ta jima bata samu yin ba, idan ta tashi sai ta sha amma ta bar wasa da shansa akan lokaci ai taji bayanin likitan ko".
"Eiii ai ko da muka dawo ma sai da na ƙara gaya mata".
"To Allah ya sawwaƙe, Kai zo ka saka min kujera a ƙofar gida".
Har dai na kwana biyar a gida babu wanda yay min zancen tafiya, ni yanda ma suke nuna min kamar ko na dawo gidan ne, zancen ma bana jin suna yi ko kaɗan, sau tari idan naji kiran Abbaa ko Kaka sai na tsammaci zancen zasu yi min sai kuma naji lafiyata ce dai za'a tambaye ni sai kuma ace ban da wata matsala? Aikin gida kuwa ƙememe Ummani bata barina nayi sai tace ina buƙatar na huta, ai kuwa ina hutawar don bacci na ke sha abuna a hakan ma don ban samu tabbacin yanda na ke so ba.
Yau ina zaune É—aki mun gama waya da Safiyya, wacca itama ke tambaya ta ko su Abbaa sun min maganar komawa na ke bata labarin komai, mun jima muna hira kafin muyi sallama wanda na ke mata godiya akan taimakonta gare ni, har ta haÉ—a ni da Baba ma a waya.
Bayan gama wayarmu na ɗakko reza ina yanke farce ina bin suratul Yusuf da na kunna. Muftahu ne ɗan wajen Baba Tijjani ya leƙo ɗakin nawa yana ce min naje Abbaanmu na kirana.
Da hanzari na aje rezar na saka hijabina. suna zaune shi da Ummani na shiga, zama nayi daga gefe kaina a ƙasa, gabana sai faɗuwa yake saboda sanin cewa kiran muhimmi ne daga yanayin yanda na samesu. sai dai tsorona da fargabata bai wuce ayi min zancen Nazifi ba da komawa gidansa.
Bayan Abbaa ya numfasa ne yace da ni,"Kun yi waya da mijinki?".
"A'a Abba".
"Bai neme ki ba tun ranar?".
Na É—aga kai,"Ehh Abbaa".
Sai ya kalli Ummani yace da ita,"Akwai wanda ya zo cikin yaran nan?".
"Anya kuwa, na dai ji kamar maganar Yashaik da safe a É—akin Al'amin".
Sai Abbaa ya sake dubana yace,"Me yasa ba ki taɓa karanta min irin zaman da ku ke yi ke da mijinki ba?".
Nayi shiru na kasa cewa komai har sai da ya ƙara min magana kana na ce,"Abbaa ban san ta in da zan fara bayani ba ne, sai kawai na bar komai a matsayin me wucewa. Ban taɓa tsammani zata kaimu ga lamarin da ya faru ba".
Na faÉ—a ina jin tahowar kukan da na kwan biyu ban yi ba.
"To za ki koma gidan nasa?".
Da sauri na kaÉ—a kai ina cewa,"A'a Abba ba na so na koma".
"To ai koma kin ce za ki koma ba komawar za ki ba, don ranar da mahaifiyarki ta faɗa min dukka halin da kike ciki na yanke hukuncin cewar zamanki da shi ya ƙare. ni duk ban san haka al'amarin yake ba, tunanina irin ƴan matsaltsalu ne dai na gidan aure da aka saba fuskanta shiyasa ko da yaushe na ke cewa kiyi haƙuri, ashe abun yay ƙamarin da muka shiga hakkinki tunda bamu taɓa ba ki damar yi mana bayani ba, kuma da sai ki rubuto min ko a takarda ne tun inda baki ne katse ki na ke yi, amma kiyi haƙuri".
Wayarsa ya ɗauko a aljihu, yana ƙoƙarin kiran Yashaik sai ga shi ya shigo, ya gaida su nima na gaida shi tukunna ya nemi waje ya zauna. Zamansa ba wuya Yaya Imam ma ya shigo, shima bacin sun gaisa ya zauna yana tambayata ya sauƙin jikina na ce masa naji sauƙi.
Abbaa ya dubi Yashaik ya ce,"Ina ka nufa yanzu?".
"Ehh to daga nan dai zan je makarantar su Yasmin zan biya kuÉ—in makarantarta".
"Kai fa Imam?".
"Ba ni da wajen zuwa Abbaa". Ya faɗa wanda na san ba hakan ba ne, haka yake a ko da yaushe idan iyayensa suka tambaye shi me zai yi ko ina zai je sai yace babu saboda biyan tasu buƙatar.
"Yauwa to kasa kunne da kyau ka jini. Ka kira Nazifi kace masa ya aiko da takardar sakin Sa'ida, ya aiko da takardar sakin Sa'ida a yau ba sai wani lokaci ba, kar ya aiko min da takarda me É—auke da saki É—aya ko biyu, saki uku na ke so ya aiko min da shi, ka faÉ—a masa ya gama zama da ita har abada".
Yaya Imam ya É—auki wayarsa yana cewa,"Yanzu kuwa Abbaa, ai don kar nayi gaban kaina ne dama amma tun ranar da kotu ta sallame mu na so ya rubuta takarda a lokacin ya bayar, to da naji kayi shiru yasa na dakata don ban san me ka shirya ba".
Ni na karanto masa lambar wayar, ashe shi tuni ma ya goge lambobinsa, kiran farko ya katse na biyu da na uku ma haka duk ba'a ɗaga ba, sai da ya ƙara na biyar ɗin kana aka ɗaga, muryarsa daga can a daƙile yay sallama, Yaya Imam ya amsa masa da cewa,"Saboda amsata wajibi ne ban da haka baka isa na amsa maka ba, nama yi mamaki da har ka san ya kamatan sallama, ai ce na ke ka manta da addinin gaba ɗaya. Anyway ka kore watsatstsen tunanin da ke ranka akan kirana, ba kiran da aka saba yi da ba ne, lafiya shiru har wannan lokacin baka aiko da takardar sakin Sa'ida ba?".
Wani makirin murmushi yay irin na marasa mutuncin nan yace,"Mun yi da ita zan saketa ne? Idan ma tunanin hakan ne akanta to ta cire shi domin ni ba zan saketa ba, kuma ka faÉ—a mata ko ta gama zaman gidan ko ba ta gama ba ta tattaro ta dawo yau, dama ba bisa izinina ta tafi ba, kuma zata dawo ta same ni".
"Kaga dakata, magana na ke maka ta dole zaka saketa, ka rubuta takarda a yau ka aiko mana da ita".
"Imam ka ke ko? Ba zan taɓa yin abinda kuke so ba, Sa'ida sai dai ta ci gaba da rayuwa a gidan naku haka amma ba zan saketa ba, kuma ni da ku mu zuba mu gani".
Ƙit ya kashe wayarsa kuwa. Abbaa ya fara magana cikin kakkausar murya, kana jin yadda amon ta yake fita hakan zai tabbatar maka da yana cikin tsananin ɓacin rai,"Babu wani mahaluƙi Wanda ya taɓa tozarta mu kamar wannan yaron! Babu Wanda ya taɓa wulaƙanta zuri'a ta irin wannan yaron, me yake jin kansa? Yaushe ya taka matsayin da zai ci mutuncinmu haka? saboda yana taƙamar yana da kuɗi...".
"Taƙamar dai yana da tsiya da iskanci, kuɗinsa ɗin banza da wofi, mu ba irin talakawan da zamu bari mu wulaƙanta ba ne, ba ƴan tsiya ba ne mu amma tabbas zan nuna masa ƙaryar iskanci yake, zan nuna masa mun shallake gaban tunaninsa".
Cewar Yaya Imam.
Sautin kukana ne kawai yake fita a hankali, kaina bisa cinyar Ummani, sai faman goge min hawaye take yi, jikina ya yi zafi rau kamar wuta. Idanu na kawai na rufe gam saboda da zarar na buɗe su sai su riƙa haskomin abubuwa barkatai.
Muryar Ya Imam na tsinta a cikin tunanin da nake yi yana faɗin,"Abba kayi shiru ka daina ɗaga muryarka akan wanda bai gaji arziƙi ba, ka bar lamarin komai a hannunmu, duk yanda zai yi sai ya bata takardar saki ko shi ya fi kowa taurin kai a duniya, nasa kaɗan ne zan nuna masa ƙaramin mara mutunci yake, ni ubansa ne a taurin kai, zan gwada masa wallahil azim Sa’ida tana da Yayye masu tsaya mata kuma ƴar gata ce, na baya ma da yay rashin sani ne shiyasa har ruwa ta sha".
Yashaik ya ce,"Ki bar kuka ke kuma, ai kuka ya ƙare maki, kar ki ji komi ki kwantar da hankalinki zama da Nazifi ne kin gama shi... Ko ya ba da takarda ko kuma daga nan har kotun ƙoli wallahi".
Yaya Imam yace,"Kotu zaka kai shi? Ka shirya ɓatawa kanka lokaci kenan, ai yanda Abbaa ya buƙaci takarda a yau tabbas a yau ba sai an kwana ba zai rubutata ko da yana rubutu jini na zuba a hannunsa, zan je har inda yake karɓowa, idan yay min garda wallahi zan raunata shi ne kuma na tilasta masa ɗaukan takarda da biro ya rubuta abin da muke so".
Yana faɗin hakan ya miƙe yana saka wayarsa cikin aljihu, kafin ya nufa ƙofa Ummani ta dakatar da shi tana cewa,"Imam dawo, dawo kar ka tafi a zuciye ina tsoron zuciyarka Imam, gwara ayi abun nan cikin maslaha idan bai bayar ba sai muje gaban alƙali, amma kaga yana ji da kuɗinsa kar abu ya kwaɓe mana".
"Je ka Imam, karɓo takarda sakin ƙanwarka a hannun Nazifi shi zai tabbatar min da kai jinina ne na gaske".
__________________________________
*Gwarazan Labarai na ƙarshen shekarar 2023 masu ma'ana.*
*KWANTAN ÆAUNA*
Nana Haleema
*ƘAYAR RUWA*
Halimahz
*LOKACI NE*
Oum Mumtaz
*FARGAR JAJI*
Aisha Yabo
*WASA DA RAI*
Fadila Yakubu
Ɗaya ₦500
Biyu ₦800
Uku ₦900
Huɗu ₦1000
Biyar ₦1200
*Biyan KuÉ—i Ta*👇ðŸ»
6314170140
Fidelity Bank
Sa'adiyya Zakariyya Haruna
*Shaidar biya ta👇ðŸ»*
09061794195
*Godiya tare da adu'an fatan alkhairi ga wanda suka sami damar mallakar littafanmu, son So fisabilillah🥰*
#TeamFitattuBiyar
[2/2, 07:47] Hlm: *B2ƘR17FT5*
"Kai kuma kaje ka gama da makarantar Yasmin É—in".
Abbaa yace da Yashaik wanda ke tsaye shima jikinsa na tsuma saboda fushi da ɓacin rai.
Ummani tace,"Abbaa na faɗa maka idan yaran nan suna cikin yanayin ɓacin rai ka daina saka su aiwatar da ɗaukan mataki, kaga ba'a san me zai je ya dawo ba. Yanzu dai da ka dakatar da Imam ɗin ka san halinsa kar ya zo yay masa dukan illah mu kwana a ciki".
"To ke kina zaton ko dukan mutuwa Imam zai yi masa zan ji daɗi ne? Ai a duniyar nan babu wani hukunci da za'ai wa Nazifi na ji sanyi a raina. Sakar min ƴa shi ne kawai zai ɗan ragen raɗaɗi, amma batun hukunci wannan sai mun haɗu a kotun Allah, ban da lokacin ɓatawa na yin shari'a da shi a duniyar nan".
Sai ya dube ni yace,"Ke me kikewa kukan to".