← Book details Ƙayar Ruwa 2&3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 109 OF 113

Sashe 109

Ƙayar Ruwa 2&3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Na yi shigan suna na haɗuwa, in saka in cire kace sabuwar amarya, ni da yarinyata Rofi'a shiga iri ɗaya muka dinƙa yi, haka itama Kudrat da yaranta, ashe har anko tayi mana ban sani ba sai a ƙarshe da taro ya kusa watsewa ne take cewa to ga ankonmu har da Mijinmu, haka muka yi shigan irin kayan yarensu na saƙi, mun yi kyau sosai aka mana hotuna, Paapa daɗi ya cika shi baki sam yaƙi rufuwa.

Ni dai kyautuka sai in ce har gajiya da karɓa nayi, na samu kyauta Ayman ma ya samu, yo kayan da Ayman ya samu ai har ya girma ba zai saka wasu ba, gaskiya dangin Salim sun yi a rayuwa, dangin mutunci dangin karama, dangin bugar ƙirji, yau ko ba na jikina ba zan wa mace kwaɗayin shigowa cikin wannan ahali na ban girma.

Bamu tafi ba sai washe garin ranar suna, lokacin zamu tafi mun jewa Sir sallama ya bani takardun fili ɗauke da sunan Salman Salim Sadiq(Emeka Oluwa), sai naji sunan ya ƙara burgeni, mallakin ƙaton fili kyauta daga kakansa, ashe haka suke, idan suka samu ƙaruwan jika sai kakansa ya mallaka masa kadara me girman gaske, to shi Baban su Salim jikokinsa duk filaye yake ba su kuma manyan filaye, da yake gaskiya ba wani talaka a familyn kowa da rufin asirinsa iya gwargwado, sai dai mahaifin su Salim ɗin duk yafi su kuɗi.

*B3ƘR19FT5*
Muka koma gida na ci gaba da rainon Ayman cikin kyakykyawan kulawa, Mama A'i na tare da ni har muka yi arba'in, na ƙara samun cima me kyau. Sai bayan mun yi arba'in naje kano, ranar muka tafi gaba ɗaya har Mama A'i, Kudrat kawai muka bari a gida don gaba ɗaya da yaran muka wuce, ba jirgi muka hau ba a mota muka tafi, daga can gidan su Salim aka turo mana da direbobi biyu, Babban motan ƙiran Land Cruiser Prado a cikinta ne ma ake fita da Maa, muka shiga ciki gaba ɗayanmu, tawa kuma Lexus RX 350 wadda Salim ya bani ranar suna sai muka zuba kayanmu a ciki ɗayan direban ya biyo bayanmu, kuma saboda yawon arba'in da zanyi idan munje can ɗin shiyasa muka yi tafiyan motan, Salim yace sai direban yake kai mu duk inda zamu je tunda ban riga na iya motar ba, shi bai son ake masa yawon hawan mota da jaririnsa duk ya kwaso ƙura da iskan hanya.

Zuwana gida kamar a cinye ni, Ayman kuwa tunda yaje hannun Yaya Al'amin sai da ya kusa awa guda tukunna ya dawo da shi, har da zolayansa na bari yay yawo da É—an gidan Æ´an gayu masu kuÉ—i, matarsa na zaune ya nuna mata yana cewa,"Irin wannan me kyan za ki haifa idan kin tashi, ki yi ta saka shi gaba kina kallo har su tafi".

Ummani ce ta kora shi a wajen tana faÉ—in,"Mara kunya". Naji daÉ—in yanda na samu labarin matar Yaya Al'amin, da yake lokacin da aka yi bikin ina America, É—akina Yaya Al'amin ya gyara ya haÉ—e da nasa wanda aka shigo da shi ta ciki, don Ummani ce tayi bata so ya matsa a kusa da ita, Matar ita ma me kirki da ita Ummani tace wallah ji take kamar tana tare da ni, iya ladabi da biyayya da taimakawa dai Buzuwa na yi mata, ita dai Ummani kam tayi dacen surukai saura kuma matar Abbayo, shima Allah ya haÉ—a shi da ta gari.

Ranar dai Ayman ya sha jagwalgwalon hannu, wannan ya ɗauka wancan ya ɗauka, manyan nan maƙota ƙawayen Ummani ai ba su jira gari ya waye na shigar mu ba, shigowa suka dinƙa yi suna sun zo ganin Hajiya Sa'ida da Balaraben Ɗanta.
Tun zuwana baki yaƙi rufuwa, haka murmushin fuskata yaƙi ɗaukewa, duk wanda ya ganni sai ya ƙara kallona ya ce,"Masha Allah".

Gida kuwa mamakin yaren da bakina ya kama suke. Ummani ta ce,"Gaskiya Sa'ida kin yi ƙoƙari, yo wannan idan ni ce ta ina zan fara iya wannan yaren, ni fa ɗazu da kuna yi da yaren gani na ke kamar ba ku san me kuke cewa ba".

Na ƙyalƙyale da dariya na ce,"Ummani kuma fa ba wahala, nima fa da na je ban taɓa tsammanin zan iya ba wallahi, wahalarsa na dinga gani, shima da yaga naƙi mayar da hankali na iya sai ya daina min turancin ya ke min yaren, kuma fa Ummani kin san maƙasudin iyawar?".

Ina dariya na ce,"Haushi yaji yace to ya daina magana da turanci a gabana shi da Kudrat, da yare za su dinƙa yi ko na dinga tsarguwa naji haushi".

Ummani ta kama dariya,"Ai kin ga yay maganinki".

"Wallahi fa Ummani tuni na zuciya, don haushi na ke sosai naji sun sauya yare a gabana, ba shiri kuwa na dage na koya nima, to yau da gobe ga shi ma idan ina yi sai ace nima su ce ba bahaushiya ba".

"Haka ne, ai ni dai wannan aure na ki Sa'ida abin jin daɗi abin alfahari, ke dai ki ci gaba da biyayya da ladabi, ki kuma tsaya akan gaskiya, ki kama danginsa kamar na ki, matarsa yanda ya ke so ku zauna ki fishi ƙoƙarin ganin ma kun zauna a hakan kin ji".

Na ce,"Insha Allahu Ummani".

Muka bar tsakar gida muka koma cikin ɗakinta. Muna cikin hira Buzuwa ta shigo ta duƙa tana cewa,"Anty Sa'ida ko yaran za su mu kwana a can".

Na kalli Ummani bata saka mana baki ba. Na ce da ita,"Ba takurawa Buzuwa?".

"Ah babu Anty Sa'ida, ai akwai waje".
"To shikenan".

Sai da muka gama cin abinci da yaran kana na shirya su, Rofi'a ba zata ba dama, maƙale mata ce, Isioma da Forida na turawa Buzuwa can, da ma mun taho da manyan barguna guda biyu tunda na san yanda gidan namu yake.
Ai har sha ɗaya muna ta hira da Ummani, zazzaɓi ya rufe Ayman, ina faɗawa Ummani tace,"Yo ba yasha ɗauka ba ai dole yay zazzaɓi, kin san jikin jarirai, don ma ya fara zama mutum".

Ai kuwa ba shiri na ɗau takarda na rubuta sunan magani na bawa Mustafa Ƙanin Hindatu yaje chemist ya siyo min. Duk rigimansa yau dai shiru kaman ya san mun zo baƙunta, na ba shi maganin yana sha kuma sai bacci, da yana ta wuntsil wuntsil ɗinsa.
Ban kuwa faɗawa ubansa bai da lafiya ba, don faɗa ne zan sha ƙarshe ma ya rage mana kwanakin da muka zo yi.
Washe gari can gidan Hajjo muka fara zuwa, muna ta waya da Safiyya na ce min ba zan zo ba sai na gama tsufa a garin.

Mun zazzaga ƴan uwa da abokan ariziƙi ni da yarana, wani wurin in muka je har tambaya ake wai ƴaƴan kishiyar tawa barin gidan tayi ko mutuwa tayi.
Kwana goma muka yi a Madobi har da matar Yaya Al'amin muka tafi, ita ce me jigilar goyon Ayman, idan ya zo hannuna to nono zan ba shi, ƴan uwan Ummani da na Abbaa ƙalilan ne ban je musu ba, ai kuwa jikina ya faɗa min, haka na yi ta faman shan maganin ciwon jiki, Yaran kuwa sometyms har ƙorafi suke ba ya Rofi'a mage uwar son jiki, shi kansa direban da ke jigilar yawo da mu sai da yaji a jikinsa, da muka je madobin can ya zauna masaukinsa a gidan Baba Audu suna kwana tare da ɗansa Muzammil.

Watanmu guda currr a kano, ranar da zamu koma sai da naji kamar kar mu tafi, Salim ne ya zo zamu wuce tare da shi, ya dawo daga Ekiti sai ya biyo ta nan É—in, yara da suka gansa murna kaman me, ranar har cikin gidanmu ya shigo, sun kanainaye shi sun hana sa ma zama, Abbaa na tsokanar su ai anan za'a tafi a barsu, Salim É—in ma yana murmushi ya ce dama ai an barwa Ummani su.
Da goma sha tara ta arziƙi haka muka bar gida, iyayena sun cika ƴaƴan Salim da abubuwa, Yashaik ma babban kwalin choculate haka ya siya musu, ga yaran da shiga rai da saurin sabo, ba wanda bai kewansu ba da zamu tafi.

Da muka biya ta gidan su Safiyya Umman su hanamu tafiya tayi a ranar sai da muka kwana, na yi tawa Salim dariya kuwa, ya azalzalo ni daga gidanmu mu tafi shi kewata yake yi, kuma mun je yaywa Umma sallama ta riƙe mu, ni dai har ya fita a falo dariya na ke masa, ga babu damar mu kwan tare da shi a gidan, haka dole ya haƙura ya riƙe yunwarsa.

To haka rayuwa ta ci gaba da tafiyar min, idan na kalli kaina sai nayi mamakin yanda na koma, Allah ya kai ni matakin rayuwar da ban taɓa haskowa kaina ba, dama an ce nasarar mahaƙurci da wanda aka wulaƙanta ba ta zuwa a ƙarance, har godiya na ke ga Allah da ya rabo ni da waccan rayuwar ta gidan Nazifi ya musanya min da mafi alkhairinsa.

Watan Ayman goma sha huɗu na fara sabon laulayi, na faɗa sabuwar duniyar murna da jin daɗi, wallahi ban ƙi ba ayi ta bani, ina so mijina ma kuma na so, don mun tara da yawa ba zamu gaji da su ba, mu abun alfaharinmu tun da ko Annabi ce ya ku hayayyafa domin na yi alfahari da ku.
Wannan karan kuwa na wahala nayi ciwo fiye da wanda nayi lokacin cikin Ayman, sai dai shi wannan gwajin farko aka gane ciki ne, bai ɓuya ba kamar na Ayman. Ba shiri na yaye Ayman, ranar har da Kukana sai kace rabamu za'ai, na sha tsiya kuwa wurin Mahbub da matarsa.

Wajen Kudrat Ayman ya koma dan ita ce uwar Yayen, kan kace me kuwa yaro yaje hannun kulawa sai ga shi yay ɓul ɓul da shi, har wata ƙiwa ma yake min, na ce lallai ne Ayman ka riƙa ka riƙe. Sai in ya so ne ma wataran idan ƴan rigimar na kansa to fa sai ya zo wajena za'a samu salamar kuka, dama shi indai kuka ne ya iya, har ce na ke da Mahbub kai kuwa wanne irin kuka kayi da kana yaro, yay dariya ya ce ke dai wanne irin kuka kika yi, ni ai da an ganni anga salihin bawa.
Chapter 109 · 0% Book details