← Book details Ƙayar Ruwa 2&3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 72 OF 113

Sashe 72

Ƙayar Ruwa 2&3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ina faÉ—in hakan ya zauna daga tsugunen da yake. "Au haba! Ashe haka aka yi?".
Ya tanƙwashe ƙafa ya amshe kofin hannuna ya kafa baki ya shanye kunun ayar. Ya sauke yana yin gyatsa kana ya kalle ni kaɗan yace,"Ina son kukun aya sosai, wannan yayi daɗi matuƙa, ki cewa Ummani ɗanta ya na godiya Allah ya ƙara mata lafiya, and i hope kema kin iya me daɗin hakan?".

Ƙura masa ido nayi kafin na ɗan harare shi, sai shima naga ya galla min harar ido kamar zai zazzago ka rantse macece, kawai sai na tsinci kaina da yin dariya kafin na sha mur. "Ehh ai gwara ki sani ba ke ɗaya ke da ido ba, harara ce kowa ya iya ai".

"Ina maka zancen serious kana É—auka da wasa, kuma na san ko Abbaa ya faÉ—a maka bana haihuwa don haka kar ka dage akan sai ka aure ni ba zaka yi farin ciki ba".

"Yau ba ki je aiki ba kenan? Ko duk zumuɗin zuwana ne da son ganina ya hana ki fita, to a albashinki ni babu ruwana, kar ki zo daga baya kina min ƙorafi an cire miki kuɗi".

Yay maganar da son shashantar da wancan zancen. Na tsinkaye shi da ƙara cewa,"Yanzu dai yaushe su Baba za su dawo ayi maganar sa rana? Ba na so ayi taking long, a yanda na tsara cikin satin nan su dawo a bada kuɗin aure a tsayar da rana wata guda, shima don na san za kice sai kin yi ƙaƙalen shirye shirye ne, to kafin dai mu shiga january na ke so na mallakeki ki zama matar lieutenant Salim".

Ɓata rai nayi ina masa wani kallo na ce,"To ni nace maka ina sonka ne da har kike lissafin ayi aure".

"Manta da wani so me wuyar dama shi ne mu fahimci juna kuma mun fahimta".

"Da yaushe É—in muka fahimta?".
"Ehhh kin fahimci ni mugu ne mara mutunci me wulaƙanta mace me tozaratata me cuzguna mata, ni kuma na fahimci ke ba kya haihuwa kuma an rubuta a goshinki ba za ki taɓa haihuwa ba, shikenan sai me ya rage kuma? Sai aure idan muka je can sai ayi ko wacce wacce".

Yanda yake zaro magana kamar bahaushen gaske, kuma magana ta masu karfin hali da zaƙewa, Na kauda kai gefe ina jin haushin ma maganar tasa, bai damu ba yaci gaba. "Safiyya ce babbar ƙawarki zan je na tambayeta sizes ɗin kayanki, tare zamu je haɗa lefen ko na haɗa da kaina ko kuma kuɗin zan ba ki?".

Na kuma yin shiru ina daɗa kallonsa da zaƙewarsa. Kai tsaye kuma yaci gaba,"Ba zan raba muku gida ba fa tare za ku zauna, yauwa bana son kan matana da yarana ya rabu, so na ke ko da yaushe inga iyalina a tare cikin farin ciki da kwanciyar hankali, kuma kinga abokiyar zamanki bata da matsala tana da sauƙin kai kamar dai ke ɗin nan".

A wani zabure na miƙe babu shiri ina neman hanyar fita. Ban san me yasa naji zuciyata ta motsa ba, sai ya kamo rigata ya maido ni na zauna, ina cin magani na ce,"Kar ka ƙara kama rigana".

Sai ce yay,"KuÉ—in jikina ba su da yawa da na bada sadaki yanzu".
Baki na murguɗa kawai, ni duk ya ishe ni raina sai ƙara ɓaci yake.
"Allah ba ki haƙuri, yanzu dai yaushe zan dawo? So na ke dai nayi zuwa biyu uku duk inda zan yi na huɗu sai dai ya zamana na zo ɗaukarki ne gaba ɗaya".

Na ware ido. "Dama haka ake yi?".
"To ni haka zan yi kuma na tabbata Abbaa zai yarje min, idan kuma kina da kuÉ—in biyan jirgi ko motar Æ´an kai amarya ne shikenan sai ki yi zugar jama'a, ni dai ba me kuÉ—i ba ne da a kano zan zauna ne dai sai in iya cewa zan biya kuÉ—in mota".

Na dakatar da shi,"Kaga please joke apart and let be serious". Zama ya gyara yana tallafe haɓa ya maida hankalinsa gare ni da kyau. Nayi ƙasa da kai yatsuna a sarƙe nace,"Ni da gaske na ke maka ban da ra'ayin aure, ba zan ƙara yin wani auren ba, saboda haka ka janye maganarka kawai don Allah ka tafi wani wajen".

Kawai wai sai naga ya kifa kai yana kukan wasa, har da su shashsheƙa yana faɗin,"Yanzu ni wanne kalar zunubi na aikata da ban cancanci likita ta so ni ba".

Nace,"To ai ni ban ce bana sonka ba". Ya É—ago ido ya duben, na kulle ido kafin na ce,"Kuma ban ce ina sonka ba". Shi kuma yace,"Kuma ko darajan Safiyya da Umma ba zan ci ba?".

Nayi saurin cewa,"Za ka haɗa ni da ƙawata kenan".
"Bari ma na kirata na shaida mata, ai ƙanwar tawa ƙawata ce".

Da sauri nace masa,"Aa don Allah kar ka faÉ—a mata, Safiyya akwai taking abu so serious".

"To ki ce kina sona kuma kin yarda za ki aure ni".

Raina still a cukule na ce,"Ba yanzu ba".
"To sai yaushe?".
"Sai sanda na gama nazari da tunani".

Ya É—aga kafaÉ—a,"Tom shikenan na ba ki lokaci...yanzu zan wuce kar Abbaa yaga na jima".

Nayi saurin miƙewa ina cewa,"Tom". Shima ya miƙe yana faɗin,"Ai dama na san kin gaji da ni, kina ta zagina ma a zuciyarki".

Shiru nayi ban biye masa ba, haka dai ya tsaya kusa da ni yana shafa waya, ban yi masa sallama ba na fita a ɗakin na barsa, wa ma ya san nayi sallama ko ban yi ba haka na shiga gida, ina shiga ɗaki na faɗa kan katifa ina ta sauke numfarfashi, kaina a kife yake kan hannuna, ba tunani na ke ba haka ban san me yake cikin kaina da abinda ke haskawa a idona ba, amma dai cikin zuciyata ina jin zafi kamar an hura wuta. Na jima a haka can naji muryan Ummani na faɗin,"Masu karɓar ɗinki sun zo na ba su".

Nayi saurin miƙewa zaune da sanyin jiki nace,"Ummani kika ba su kuma, ban fa gama sanya stones ba".

"Su suka ce a ba su a haka wai yau za su saka, ina ce stones ɗin a ƙasa ne kawai ba ki saka ba?".

Na É—aga kai alamar ehh ba tare da nayi magana ba. Sai tace,"To na haÉ—a su da Yasmin su tafi tare ta saka musu acan kafin su gama shiryawa, bana so Abbanku yaji ne ya fito ya kama faÉ—an rashin gamawar".

Nasa hannu ina goge hawayen da duk ya wanke min fuska, ina jin idonta akaina kafin tace,"Sai ki yi istikara ai ki nemi zaɓin Allah ba ra'ayin zuciyarki ba, shi kukan mene amfaninsa banda ɗorawa kai ciwo, kuma dai ai ba zuwa aka yi aka ce ana ƙin ki ba".

Na waiga ina dubanta na ce,"Amma Ummani ni kawai...".

Ba ta jira ƙarashen zancena ba tace,"A'a ba da ni aka yi maganar ba yana ɗaki kije ki sameshi, mene a ciki dan kin ce masa ba kya so, mu dai ai ba kwaɗaki zamu yi mu cinye ba, lokacin kuma da kika sakko akan ƙudurin na ki ai kinga kya auri sa'an Kakanki".

Tana faɗin haka ta fita tana cewa,"Ki fito ki tankaɗe min gari, ki kuma ƙarasa haɗa miyar gata can na ɗora a wuta".

Na koma na kwanta ina ta tunanin ta yanda zan yarda na komawa duniyar aure, Mazan ba duka suka zama ɗaya ba na sani, to amma zaƙin bakin namiji fa? Ni a ganina tunda har Nazifi ya canja to tabbas kowa ma zai iya sauyawa, kuma tunda har ya daina sona ya tsane ni akan rashin haihuwa to bana tunanin akwai wani Namiji da zai iya shimfiɗa rayuwar aurensa da ni a yanda na ke.
Ringing ɗin wayata ya katsen tunani, na ɗauka na duba naga Safiyya ce, ban ɗaga ba saboda fushi na ke da ita don na san ta san komai game da zuwan Salim, sau uku tana kira ni kuwa nayi biris kamar ban gani ba, sai can ga message ɗinta ya shigo da cewa,_"Zancen gaskiya wannan karon kika ƙi ɗan uwana to zamu samu saɓani da ke, kuma Umma ma kanta tace zata san zaman da zata yi da ke in har kika guji ɗanta, ke dolenki ma ki so shi ki shirya zama amaryar ending month na gama magana"._

Ina gama karantawa na tura mata da reply É—in,_"To Sa'adatu Abdurahman Madobi"._ wato uwata kenan.
Har tsawon kwana huÉ—u ina ta tunanin matsaya, gaba É—aya na kasa yanke shawara akan lamarin, har yanzu ban ji ina sha'awar sake yin aure ba, haka ban san ta inda zan fara kallon Safiyya na faÉ—a mata cewa ta sanar da É—an uwanta ba zan aure shi ba, Abbaa dai bai min maganar ba tun ranar, shi kansa Salim É—in tun ranar bai neme ni ba ko irin É—an kiran nan bayan ya tafi, Ummani kuwa sai dai tayi ta jefa min magana cikin magana, bini bini tace yo Allah na tuba tsofaffi gasu nan da yawa a duniyar.
Yau tunda na zo aiki duk na ke jina wani iri, sai dai wani ɓari na zuciyata nata karanta min ki yi istikara yau ki samu mafita ki huta.
[2/2, 07:48] Hlm: *B3ƘR04FT5*
"Masha Allah! Abbaa ya faÉ—a yana jinjina kai.

"Salim da gaske kake kana son Æ´ata tsakaninka da Allah ba domin wata manufa ba?".

"Ƙwarai Abbaa ina son Sa'ida ba tun yanzu ba, ko a wancan lokacin na haƙura ne saboda ta nuna bata sona, kuma ko a yanzu ma zan iya haƙura idan har ta ce ba zata iya aurena ba, ba zan zamar mata dole ba kamar yanda ba zan so ayi mata dole ba, ni dai burina ne auren nagartacciyar mace kamar Sa'ida, idan kuma hakan bata Faru ba na san da cewa Allah ne ya rubuta cewar ba zan rayu da ita ba a inuwa guda matsayin ma'aurata, kuma zan karɓi hakan a madadin ƙaddara".

Abbaa yay ɗan jim kafin ya sake cewa,"Ka san da cewa ita ba budurwa ba ce bazawara ce ƙaddara ya rabata da mijinta?".

"Na san da hakan Abbaa".

Abbaa ya ƙara mayar masa da cewa,"Fatan kowanne miji ne ya samu zuri'a tare da matar aurensa, Shekaran Sa'ida goma da aure bata taɓa haihuwa ba Salim".
Chapter 72 · 0% Book details