Sashe 22
Ƙayar Ruwa 2&3 Complete Hausa Novel · about 8 min read
"Rike kije da shi. Kuma kar da ki tafi ki É—orawa kanki damuwa, ni na warke gobe ma a gida za ki jini".
Ummani ta rako ni har waje ranta duk babu daɗi, tana ta bani haƙuri da ƙara yi min nasiha. A bakin mota na same shi yana ganina ya murmusa da cewa,"Ai dama ma san Abbaa zai ce ki biyo ni. To ki ga hakan ai yafi, rashin zuwanki ɗin sai a fara ƙananun maganganu kin san halinku na mata, yanzu ace kina baƙin cikin haihuwar ne".
Na ce,"Ai ba su kaɗai ba kaima kana iya faɗa, yanzun ma ai shaguɓe kayi".
Sai yaji haushi akan me zan faɗi hakan. Tun da muka shiga motar ban ce da shi ƙala ba, duk da yana ta jana da magana yana ta faɗa min irin wuyar da Zahra'un ke sha. Wai ai har sai da aka haɗa da saukar ƙur'ani saboda an ce asiri aka yi mata akan karta haihu ana so a kwantar da cikin, yana faɗar hakan na ɗago na kalle shi, ban iya yin magana ba yaci gaba da bayani wai so ake ma a raba auren asirin dai da ake tayi babba ne.
Ni kuwa kamar na tambaye shi sai kawai nayi shiru. Sai da muka ɓata wajen awa ɗaya akan siyesiye da yake tsayawa yi, ya saya wancan ya siya wancan, ni ko bana ganin laifinsa dole yayi ɗoki tun da ya jima bai samu haihuwar ba, Ya tambaye ni ko ya siya min abinci nace a'a na ƙoshi.
Wani babban asibitin kuɗi ne a nasarawa GRA, haɗuwar asibitin kaɗai zai shaida maka asibiti ne na masu hannu da shuni, haka yake faɗa min kwanciyar duk kwana ɗaya dubu ɗari yake biya. Na ce to Allah ya ƙara horewa yace amin.
Su Iyam muka fara gani a ƙofar ɗakin tsaye da alama ma sun dawo daga rakiya ne, sai da suka gama gaisawa da ɗan nata kana nima na gaisheta ina cewa sun dawo lafiya, fuska babu annuri ta amsa kamar nayi mata dole.
"Sai yau kika ga damar zuwa kenan".
Banyi mamaki da furucinta ba, sai na tsareta da idanuwana cikin wani yanayin da na san ta girgiza da shi, na rasa me zan ce ma, tabbas da na san zata yi min wannan furucin ko gaisheta ba zan yi ba wallahi. Sai shine yace da ita,"Ina ga kin sha'afa na faÉ—a miki an kwantar da Babansu a asibiti".
Ni kuwa idan yana Babanku ko mahaifina mamaki yake ba ni, da yanda na ke kiran mahaifina haka shima yake kiransa, Abbaa sama Abbaa ƙasa. Tahowar nan tamu da suka yi waya da Baban Zahra'un tamkar zai yi masa sujjada, amma ni da yaje wajen mahaifina gaisuwar ma ina ga so yay Abbaan ya gaida shi.
Iyam tayi min wani kallo tace,"Oh anyi haka yo na mance ne, Allah shi sawwaƙe. Amma ai da ko sau ɗaya kya leƙo ki duba ita me naƙudar ba wai ki nemi wuri ki zamanki ba".
Ina murmushi me ciwo na ce,"Da yake abin da ya shafeka shi ya dameka".
Yaya na tsaye ita dama ban ma yi karambanin gaida ita ba, muna shigowa da ta ganmu da shi ta É—auke kai. To me zata ba ni? Don haka ban ce mata komai ba, haka ko ya mai jiki itama bata iya ce min ba duk da taji ana zancen.
Ya bani leda yace na shiga É—akin na kai musu Æ´an uwan Zahra'un na ciki, na shiga na samesu da yawa sunata hira da dukkan alama ma sun mance a halin da Æ´ar tasu take ciki. Muka gaisa suka amsa min kadaran kadahan, na ajiye musu ledar nace in jishi sannan na juyo na fito don ba zan juri irin kallon banzan da suke yi min ba, haka na zauna can gefe kan wata kujera ni É—aya, idan ka ganni sai kayi zaton marainiya ce gaba da baya.
Shi kuma yana ta kai komo zuwa ofishin likita, hankalinsa duk yaƙi kwanciya, daga baya kuma sai ga shi ya dawo ya zauna wajena yana ta roƙona in ke yiwa Zahra'u adu'a. ƙarfe goma da rabi ana shirye shiryen shiga da ita ɗakin tiyata sai ga wata Nos ta zo wajenmu, ganinta muka miƙe a tare da shi ita kuma tana tambayar,"Kune ƴan uwan Zahra'u Abdullahi?".
Da sauri ya É—aga kansa da cewa,"Ehh mune, an shiga da ita tiyatar ne?".
Kafin tayi wata magana tuni su Iyam suka ƙaraso wajen, ban san me ta gani ba ta dafa kafaɗata tana murmushi tace,"Ta haihu an samu ƙaruwar ƴaƴa biyu duka mata, ina taya ku murna".
Ai ji nayi kamar ni aka ce na haihu, don ban san lokacin da na kama murna ba, haƙorana talatin da biyu du a waje. Su Iyam aka yi hamdala su Yaya ma sai murna aka tafi sanar da ƴan uwanta don su suna cikin ɗakin ba su san wainar da ake toyawa ba.
Shi kuma yana ƙara tambayar Nos ɗin,"Babu namiji duka mata ne?".
Ta ce,"Ehh duka mata. Ba da jimawa ba za'a fito muku da yaran ana gyara su ne".
A iya zamana da Nazifi ban taɓa ganinsa a cikin tsananin farin ciki ba kamar yanzu, don zubewa yay kawai ya miƙa sujudu shukur. Bayan ya ɗago kuma sai ya dube ni yana,"Kinga lamarin Allah ko, mahaƙurci mawadaci, da nayi haƙurin kinga lokaci guda ya bani har guda biyu, nan gaba kuma na san zai bani abokin me taimaka min in sha Allahu. Ki tayamu murna Sa'ida".
Ina murmushin jin daÉ—i dan na mance ma ni da wata damuwa na ce,"Ina tayaka murna Allah ya raya mana, yay musu albarka".
Kowa dai a wajen murna yake, sai dai duk ana ce musu babu namiji sai naga jikinsu yay la'asar, haka ma Iyam tun da aka ce duk mata ne fuskarta ta sauya alamun ba hakan ta so ba. Ba'a jima ba sai ga Nos biyu tare da yaran, ya tafi da sauri ya karɓe su, bakinsa yaƙi rufuwa yanda ka san gonar auduga, wato Allah ɗaya yasan farin cikin mutum ke riskar kana a ciki idan ya sami haihuwa, haka ga wanda Allah bai ba shi ba Allah ɗaya yasan irin abin da yake ji a tare da shi, da taimakon Nos ɗin ɗaukan yaran ya daidaita a hannunsa.
Likita yazo yace da shi,"Zasu nuna muku É—akin da aka sauya mata, sai dai a yanzu mutum É—aya ne zai iya ganinta sai nan da wani lokaci kowa ya iya shiga".
Muka ɗunguma duk muka bi bayan Nos ɗin da ke mana jagora zuwa ɗakin, Shi dai ya kasa ma bawa kowa yaran duk suna hannunsa, bayan ya gama yi musu kiran sallah ne yay musu huɗuba tsautsayi yaja ni na miƙa hannu zan karɓi ɗaya sai ce yay min,"Yi haƙuri bari su fara jin ɗumin jikin mahaifiyarsu tukunna".
Ya faÉ—i hakan yana shigewa ciki, Na jiyo Iyam na faÉ—in,"To ai ko saboda ma ta tofe yaranta da adu'a gudun masu cutarwa wani ba ya É—auke su ba ita bata É—auka ba".
Sai lokacin na dawo cikin hayyacina na shiga hankalina na daina ɓarin jiki, don haka na koma gefe na rakuɓe. Ta glass ɗin tagar ɗakin na ke hango yanda Nazifi ya haɗa yaran da uwarsu ya rugume yanata sumbatarta.
Sai bayan awa guda kana muka shiga ciki, aka baibayeta kowa na mata barka. Ta kalle ni muka haɗa ido da ita, murmushi na sakar mata ita kuma lokaci guda yanayin fuskarta ya sauya daga farin cikin da take. Sai da ƙyar aka bani yaran na ɗauka, don nunawa ma suka yi basu san ina wajen ba, sai da Innarta ta karɓeta su ta miƙo min tukunna.
Kallon yaran kawai nake yi ina jin kamar kar wani ya karɓe su, na yi adu'a sosai na tofa musu, haka kawai naji soyayyarsu ta rufe ni, ma sha Allah kyawawa da su farare tass, ga hanci har baka irin na mahaifinsu, dukansu kamar su ɗaya da mahaifinsu ni dai ban ga ta inda ma suka yi kama da Babarsu ba banda haskenta da suka ɗauko.
Na shagala a kallonsu Yaya ta zo ta karɓe su daga hannuna tana faɗin ai daga haihuwar yaran ba'a dinga jagwalgwala su ba. Haka ina ji ana ta yada min magana, wata cikinsu na cewa da Zahra'un tayi mamaki da taga duka mata, da aka yi scanning ai mace da namiji aka ce.
Sai wata da bata jima da zuwa ba kamar ma Yayarta naji suna cewa, tace,"To kin manta kishiya ce da ita, kishiyar ma juya, ai dole za'ai ƙulla ƙullar ganin an hana haihuwar namijin. Irin basu da imani, basa zama kullum a tafe suke cikin jeji, kuma fa tun da ta samu cikin nan nake cewa da ita ta dage da adu'a kar tayi sakaci don yanzu kishiyar zata iya hanata haihuwar ma, kinga dai irin baƙar wuyar da ta sha ai kwana kusan goma ana naƙuda, nayi imani asiri tayi mata ta so kwantar da cikin, to sai Allah yasa mu ƴan uwanta ba zaune muke ba tafe muke muma".
Maganar ta soki raina, nayi ƙasa da kaina ina ambaton Allah. Ina jiyo ana kwaɓarta da cewa tayi shiru gani can zaune, sai ta kallo ni tana cewa,"Au wai ita ce ma kishiyartata? Ni wallahi ce nake wata cikin ƴan aikin gidan ne. Tabɗijam".
Iyam ma ta kawo ruwan rubutu tana cewa a bawa Yaran wai saboda mahassada kar su cutar da su, tun da ba kowa ke murna da zuwan na su ba.
Gaba É—aya sai naji na tsani kaina, kamar na tashi na fita to amma me amfanin fitar? gwarama na zauna tun da magangunsu dai ba fito min a jiki zasu yi ba. fatana É—aya kar Nazifi yace anan zai barni na kwana don ban san ya zan yi ba.
_____________________________________
*Gwarazan Labarai na ƙarshen shekarar 2023 masu ma'ana.*
*KWANTAN ÆAUNA*
Nana Haleema
*ƘAYAR RUWA*
Halimahz
*LOKACI NE*
Oum Mumtaz
*FARGAR JAJI*
Aisha Yabo
*WASA DA RAI*
Fadila Yakubu
Ɗaya ₦500
Biyu ₦800
Uku ₦900
Huɗu ₦1000
Biyar ₦1200
*Biyan KuÉ—i Ta*👇ðŸ»
6314170140
Fidelity Bank
Sa'adiyya Zakariyya Haruna
*Shaidar biya ta👇ðŸ»*
09061794195
*Godiya tare da adu'an fatan alkhairi ga wanda suka sami damar mallakar littafanmu, son So fisabilillah🥰*