← Book details Ƙayar Ruwa 2&3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 24 OF 113

Sashe 24

Ƙayar Ruwa 2&3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Muka haɗa ido da shi, ko bai ce ba na san tunaninsa ni na kai ƙararsa, gabana naji yana ta faɗuwa don ni har ga Allah ba'a taɓa faɗa irin haka a gabana ba, kuma ban taɓa ganin ana yiwa babba kamar Nazifi faɗa ba don haka duk sai nake jin tsoro.
Malam ɗin ya kira sunana yana cewa,"Ke kuma Sa'ida me yasa ba ki taɓa zuwa kin faɗa min abubuwan da yake miki ba? Da ba sai ki bar masa gidansa ba don ubansa tun da shi ɗin me rama alkhairi da sharri ne. To daga yau duk abin da Nazifi yay miki na rashin kyautawa na sahale miki kai tsaye ki kirani a waya, zan tabbatar masa da ni Bala Mai Kalwa ubansa ne kuma mijin uwarsa".

Ya ƙara komawa kan Nazifin da cewa,"Ina iliminka Nazifi? Kaf ƴaƴana babu wanda na ke alfahari da shi irinka ashe zaka bani kunya, ashe kayi watsi da addininka, har abun duniya ya iya rufe idanuwanka, ita uwar taka idan tayi tsufan da ya ɗebe tunanin yakamatanta ba sai ka nusar da ita daidai ba. To wallahi kaji na rantse idan baka saita zaman gidanka ba ka zama adali tsakanin matanka ba zaka sha mamakina, domin ina mai tabbatar maka da akan yarinyar nan Sa'ida zan iya yafe ka. Ai ni ban mancewa da halacci".

Kuka na saka kaina a ƙasa na ce,"Don Allah kayi haƙuri Malam, duk ba haka ba ne, ba yanda aka faɗa maka ba...".

Katseni yay da ɗaga murya,"Rufe min baki, saboda kina da tsananin haƙuri shine za ki kare shi, ki zauna suna cutar da ke".

Ni ban ma san yanda zan kwatanta maku irin faɗan da Malam ke yi ba. Nazifin ya hargitse sai haƙuri yake ba shi, da ƙyar ya sassauto ya shiga yi mana nasiha mai matuƙar ratsa gaɓaɓan jiki, wanda ni dai irin yacca wa'azinsa ke shigata hawaye kawai na ke yi, shi kansa Nazifin muryarsa tayi rauni, ga irin ayoyi da hadisan da yake janyowa sai da na mugun jin tausayin Nazifi, take kuma naji a zuciyata na yafe masa duk abubuwan da yay min, to nawa rayuwar take ma? Allah kawai ya yafe mana gaba ɗaya.

Malam ma nunawa yay kamar bai san wata Zahra'u ba, muka baro gidan ran kowa babu daɗi, ta karɓe yarinyarta a hannuna tana yi masa kuka wai ana so a shiga tsakaninta da mahaifinsa, shi kuma ya ƙara rikicewa da kukan nata yana faɗin tayi masa shiru don Allah da wanne take so yaji. Tace ita dai koma waye yaje ya ɓatata wurin Malam bata yafe masa ba, sarai na san shaguɓe ta min, ni kuwa har muka isa gida ban kulawa lamarinsu ba, shi ɗin ne ma dai da muka shiga wajen rabuwa zan yi ɗakina yace wallahi matsawar ya bincika yaga da sawar hannuna wajen kai ƙararsa gun mahaifinsa to aurena na yiwa, tun da nake rayuwa da Nazifi a irin uƙubar nan bai taɓa yin furucin da ya dake ni ba irin wannan, wai aurena na yiwa! Kenan zai rabu da ni!

Washe gari ƴan taron suna duk suka watse, gida ya dawo yanda muke da, sai Innarta dai tana nan wacca aka bari zata dinƙa yi mata wanka. Daga baya Mamanta ta zo itama tana da kirki gaskiya domin uwa ce ta gari, tasa aka kira ni tayi mana nasiha, tace kuma ƴaƴan da aka haifa bana Zahrau ba ne kawai nima na ɗauka nawa ne, don duk macen ƙwarai tana ɗaukar ƴaƴan miji matsayin nata ne, don Allah mu haɗa kanmu mu zauna lafiya fitina ba wata abar so ba ce kar mu biyewa sharrin zuciya.

To ni dai zatona samun yaran nan zai kawo canjin zama me daɗi, sai dai ina ashe ba haka ba ne. Zahra'u da Iyam sun mayar da ni muguwa abar tsoro, ban da ikon tunkarar in da yaran suke za su farga suna maganganun marasa daɗi, har cewa suke suna gudu ne kar na lashe kurwar yaran, kullum in har zanga Zahra'u sai tayi min gorin haihuwa, sai ta nuna min ita ke da gida da miji yanzu, ni kuma haka kawai Allah ya ɗora min tsananin ƙaunar yaranta, ko wa naga ya ɗauke su sai na ce zan karɓe su in dai ba hannun Iyam suke ko kuma uwarsu ba.

Da naga abun yana yawa sai na haƙura kawai na kame kaina daga yaran, na kama kaina sosai ko ubansu ne ya ɗauko su bana sha'awar ma na kallesu balle ɗauka. Hakan kuma sai ya janyo wata sabuwar maganar a wajensa shima, wai nasa baƙin ciki a raina shiyasa duk na lalace ina ta ƙarewa, to koma dai me na ke nufi na ke kuma ƙullawa Allah ya fini, yana yiwa ƴaƴansa adu'a kuma yana yiwa mahaifiyarsu, nan da lokaci kaɗan ma zan ƙara ganin ta samu wani cikin. Ni kuwa ina kallonsa a nutse na ce Allah ya bada masu albarka bana baƙin ciki.

Wata É—aya bayan nan ina zaune ina haÉ—a kayan wankinsa ya shigo, yana goye da Noor Iman kuma tana hannunsa. Ya zo ya kwantar da su kan gadon, tun da na kalle shi sau É—aya na É—auke kai naci gaba da abin da nake yi. Can sai jinsa nayi yana faÉ—in,"Sa'ida me yasa ba kya son É—aukan yaran nan?".

Na kalle shi hankalinsa na kan yiwa yaran wasa, ni mamakin ma maganar tasa nayi, yo idan ya zo da su ba ya ji ba ya gani, idan zan masa magana dubu da wuya ya amsa min ɗaya, dama zaman namu da shi gashi nan ne dai wai ai ance masa asiri na ke neman yi akan yaran. Jin nayi shiru ya ɗago ido ya kalle ni, sai ce yay,"Zan shiga wanka ki tafasa min shayi kafin na fito. Anjima kuma zan yi baƙi ki san me za ki tanadar musu".

Na ce masa to amma ya karɓo lemu wajen Iyam da kansa. Fita yay ya barni da yaran, naci gaba da aikina ina jin Noor tana kuka amma ban juya kai na kalleta ba, ya shigo ya ganni ina abin da nake sai ya kama faɗa akan rashin ɗaukar yarinyar na lallasheta. Nace,"To so kake na ɗauketa Iyam ko Uwarta su zo su ganta hannuna su ce nayi mata wani abun".

Harara ya watsa min yana faɗin na ƙware a kimtsa magana, ya ɗauki yarinyar ya kaita aka bata nono ya dawo da ita har tayi bacci ma, dama ita Iman ɗin bata fiya kuka sosai ba barta da bacci. Shigarsa wanka ba daɗewa Noor ɗin ta farka da sabon kuka, na kalleta kamar zan ɗauketa kuma sai na ƙyaleta.
Ya buɗe ƙofar banɗakin ya leƙo yana cewa,"Yanzu tsakani da Allah kina ɗakin saboda rashin imani kina jin yarinya na wannan kukan ba za ki iya ɗaukarta ba. Dilla Malama ɗauketa ki rarrashta, banza me baƙar zuciya kawai".

Kallonsa nayi kawai na girgiza kai bayan na ce na gode da zagi. kukan yarinyar ne ya taɓa ni naje da sauri na ɗauketa ina jijjigata, haka kawai sai naji kamar tawaz da naga taƙi yin shiru na ɗau ruwan fida na bata tasha, kukan nata ya tsagaita na goyata a bayana har ta koma bacci. Ina aiki a kicin yarinyar ta fara mutsutsu a bayana, da alama dai nono take so sai na sakkota, na fito zan kaiwa Babarta sai wata zuciyar tace da ni kul don haka nayi ɗaki in bawa ubanta shi da ya ɗaukota.

Sai da na shiga na lura da Idanun yarinyar sun juye, jikinta kuma ya saki, haka nan naji zuciyata ta amsa. Sai na nemi wuri gefen gado na zauna ina jin sanyi na ratsa ƙafafuna, a hankali na shiga bubbuga bayanta ina jijjiagata duk sai naga bata motsi, hankalina ya tashi na ɗaga ido na dubi bakin ƙofar banɗakin. Na ambaci innalillahi wa'inna ilaihi raji'un, ashe da ƙarfi na faɗa ma ban sani ba, ai kuwa sai ga shi ya fito daga banɗakin a guje yana tambayar lafiya.

A ruÉ—e na ke nuna masa ita ina cewa,"Kaga idanunta naga sun juye".

Karɓarta yay yana kallonta kafin yasa yatsansa a hancinta. "Ya naji bata numfashi?". Ya faɗa yana ɗora hannu saman ƙirjinta, sai kuma yasa tafin hannu ya rufe mata idanu. A kiɗime ya ɗago ya kalle ni yana daka min wata razananniyar murya da cewa,"Me kika yi mata Sa'ida?".

Ido na zuba masa ina kallonsa cikin kaɗuwa, da ƙyar na iya buɗa bakina na ce masa,"Me kuwa zan yi mata Hubbi, wallahi babu abin da nayi mata, goyata nayi kawai har ma tayi bacci sai take ta mutsu mutsu a bayana, na sakkota zan kaiwa Zahra'u na ce bara na bari ka kaita da kanka. Kawota na bata ruwa muga...".

Fizgewa yay ya fice fuuu, na bi bayansa da sauri, ɗakin Zahra'un na bi shi na kasa haƙuri na cusa kaina ciki, ya duƙa gabanta ya kama nono yana ta sakawa ƴar a baki bakinta a datse taƙi kamawa, na tsaya daga gefe ƙirjina sai lugude yake, uwar tuni ta fara hawaye tana ƙwala kiran Inna Zulai, sai gata itama ta zo da gudunta, tana zuwa ta karɓi ƴar ta jujjuyata a hannunta, ina kallon yanda ta bimu da kallo dukanmu kafin a sanyaye tace,"Wannan ƴar ai ta koma".

"Kamar ya ta koma Inna?". Na faɗa cikin rawar baki ina kai hannu na taɓa yarinyar.

Innar ta maimaita,"Haƙuri za'ai Allahn da ya bayar ya karɓa, ina Iman ɗin?".

"Kina nufin ta mutu Inna?"...

Ƙarar da Zahra'u ta ƙwala ita ta katse sauran maganata, ni kuma a kiɗime na durƙushe a ƙasa ina ɗora hannaye saman kaina, Tsautsayi! a hankali cikin harɗewar harshe na ke faɗin innalillahi, jikina sai rawa yake yi, idona cikin na Nazifi da ke kallona da wani kalar ƙwayar idon da ban taɓa saninsa da ita ba. Sai girgiza masa kai na ke kafin na shiga ranse masa da cewa ban yi mata komai ba.

"Kin kashe min Ƴa Sa'ida, sai da kika san yanda kika rabani da ƴata, duka biyun kika kashe?".

Kuka na fashe da shi ina cewa,"Akan me zan kashe maka Æ´a, akan wanne dalili, wallahil azim ban mata komai ba, ka yarda da ni wallahi banyi mata komai ba".
Chapter 24 · 0% Book details