← Book details Ƙayar Ruwa 2&3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 113 OF 113

Sashe 113

Ƙayar Ruwa 2&3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Tashi yay jiki a matuƙar sanyaye ya shiga ɗan akurkin ɗakinsa, ya aje kwandon sana'arsa, ya saki yagalallan labulen ɗakin sannan ya kaɗe saman tabarmar ya kwanta idanuwansa na kallon rufin kwanon ɗakin da hasken rana ya shigo ta ɓulolin jiki. Samun kansa yay da rufe fuska da tafukan hannu yana fashewa da kuka, komai na rayuwan baya ne ke dawo masa daki daki, haɗuwansa da Sa'ida, Shaƙuwansu, matsayin da aka ɗaukesa a gidansu kamar ɗan gida, soyayyarsu, aurensu, rayuwar auren da suka shimfiɗa a farko, halin tsananin da ta zauna da shi, irin sadaukarwar da tayi akansa, halaccinta gare shi, samun arziƙinsa ta dalilinta, ɗaukakar da ya samu, wulaƙantata ɗin da yay kamar kare, ƙofar da ya bawa ƴan uwansa na cin zarafinta, mayarsheta baiwar da mahaifiyarsa tayi, gorin rashin haihuwar da ya dinƙa mata, ƙazafin da yay mata, rabuwar aurensu, halin da ya fara faɗawa, abinda Zahra'u tayi masa, zaman kurkukun da yayi, mutuwar mahaifiyarsa zuwa yau da Allah ya nuna masa ita tun bayan shekaru goma sha biyar, ya ganta a mataki na matsayin da bai taɓa tsammanin zata je ba, ya ganta cikin kwanciyar hankali da farin cikin da shi bai sameshi ba sam.

Kawai sai ya daki kansa a cikin kayan wankin da yay matashi da su, ya shiga kukan da babu sauti, a hankali muryansa ke fita da,"Allah ka yafe min wulaƙanta rayuwar baiwarka da nayi, Allah na roƙe ka kaji tausayina kasa Sa'ida ta yafe min, Allah ko dan yaran nan guda biyu da ka bani mata ka bani halin da zan inganta rayuwarsu, na ba su ilimi da irin gatan da jin daɗin da ƴaƴa ke samu wurin mahaifinsu".

Yana tsaka da hakan su Iman suka yi sallama a ƙofar ɗakin nasa, yay saurin tashi zaune yana goge fuskarsa, sai da ya saita kansa tukunna ya ba su izinin shigowa. Suka shigo Mubina na tafiya wajensa ta faɗa jikinsa, Iman kuma ta duƙa ta miƙa masa kuɗin da cewa,"Baba ga shi ɗari biyu da hamsin ne ya ragu, na taho da gawayi ma, Anty ta hanamu taɓa mata nata".

Sai dai yay namijin ƙoƙari wajen hana raunin da ke tare da shi fallasa a gabansu. "To kun siyo komai?".

"Ehh Baba, gawayin zaka haÉ—a min, kuma naga kaman baka da lafiya".

Tayi maganar cikin jin tausayin mahaifin nata kamar zata yi kuka.
"ÆŠagani Mubina in je in haÉ—a muku wutar can, ko ba kya jin yunwa ne?".

Tana wasanta a jikinsa tace,"Ina ji mana Baba, yau fa bamu ci abincin safe ba ka manta, sai da muka je can gidanku fa Amarya ta bamu ƙosai guda biyar, suma ya ƙare lokacin Yaya Iman ce ma tace mun ƙoshi bayan sai da Baba Adamu yace zai bamu kuɗi mu siyo wainar fulawa".

"To yanzu dai ai ga shi za'a dafa, irin taliyar ma da kike so, sai kin ci kin ture Æ´ar lelen Baba".

Tare da shi suka fita, Iman ta ɗakko masa kujera ya zauna gaban burkoti, dama basa iya haɗa gawayin sai dai shi ya haɗa musu. Sai hira suke masa wanda hiran na su ne ya ɗebe masa kewa, Mubina na tambayarsa yaushe za su wurin Mominsu, yace to sai yasa kati a waya sai ya basu su kirata su ji. Duk da ya san abu ne me wuya don ko da wasa mijin Zahra'u bai yarda yaran suje gidansa ba, yace hakan a bakin aurenta, ita ganin ta ɗebi shekaru da yawa ba auren yasa ta ke lallaɓa igiyan aurenta.

*****Sai dare Mahbub ya zo ya É—auke mu a gidan Safiyya, can muka yini yau kam, ita ma yaranta huÉ—u dukka mata, ga dai wani cikin nan da muke ta sa ran zuwan namiji. A mota muke waya da su Abbaa ina alhazawan baÉ—i insha Allah, don so na ke idan suka dawo a Umra to aikin Hajji ma ayi da su, yanzu haka ma na haÉ—a kuÉ—in mutum É—aya saura na mutum É—aya, kuma kafin zuwan lokacin Allah zai hore in haÉ—a, na fi so suje dukka su biyun

"Mommy ina bindigan da Mami ta ba ni". Ayman ya faɗa yana zuro kansa ta tsakanin kujeran motan, ni ban so Safiyya ta ba shi bindigar ba duk da ta wasa ce ni bana so, ko da yake Babansa ma ba shi ta gaske yake yi. Nayi masa shiru kamar ban jisa ba. Umarul Faruq ma ya kama cewa,"Mommy nima ai Mami ta bani jirgi irin wanda Paapa ke hawa". Shima na masa shiru, Ajmal kuwa sai taɓo Mahbub yay ya ce,"Paapa har da ƙatuwan mota Mami ta bani nima".

Na girgiza kai muka haɗa ido da Mahbub, ya ƙaramar ariya yana cewa,"Hmm duk ma za ki fitowa da yara kayansu ne, sai aiwa yara kyauta ki riƙe".

"Naji, ni É—azu ma ban baka labari ba, sirikata ta kira ni wai don Allah asa musu rana suna so zasu zo ayi maganar aure".

Murmushi yay da cewan,"Wacce surukar taki, don naga duk kun tara surukai, Æ´aÆ´an gaba É—aya kun bayar da su".

Nayi dariya da maganar tasa, daga cewa za'a haÉ—a Ayman da Æ´ar gidan Safiyya Iftihal shi ne tsaban sharri wai duk mun bayar da su. Na ce,"To dai Allah zancen gaskiya na ke maka, ina saurayin Forida likitan nan na Abuja, to Mamarsa ce ta kira ni".

Dariya yay yace,"Sai ku yi magana da Hassanarki ai, lokacin da ku ka fara barin yarinyar zance sani nayi, wallahi ni dai gaskiya na ke faÉ—a muku ku daina munafurtata".

Haka muke ta hiranmu da shi cikin nishaÉ—i, hankalin yaran ma duk ba ya garemu suna baya suna vedio call da Ummani, shi kuma nan shafo cikina yake yana faÉ—in,"Daren yau zan samar da uku kyawawa".

Na doke hannun nasa ban biye masa ba na maida kallona kan titi. Don na fara tsoron yaran nan, kwanaki Ayman rutsa ni yay na gama shirya shi zasu tafi school wai sai na masa irin kiss da hug É—in da na ke ma Paapa, to ga Umarul Faruq nan ma daga na sumbace shi a goshi sai yasa min darun irin wanda na ke ma Paapa shima a lips.
Na waiga na dubi yaran, kallonsu na ke duk cike da so da ƙauna, kafin na maido da dubana ga mijina wanda na tsare da kallo har sai da ya kawo yatsu sai tsole min ido, ina dariya na sauke ido ina ƴar dariya, wayata na buɗe maimakon shiga whasapp ɗin da nayi niyya sai kawai na ɓige da kallon kaina a kan screen ɗin wayar, ni da Ajmal da Umarul Faruq da Ayman da Mahbub. Rayuwa kenan, Allah mai yanda ya so, ga shi dai yau ya haskaka rayuwar Hajiya Sa'ida, ya haska ni da hasken da ban taɓa zaton samunsa ba. Haƙiƙa ba ka fidda rai da duk abunda yake na Allah ba na wani bawa balle yace zai hanaka.

Na sauke numfashi, annurin fuskata na ƙara washewa, na faki idon yarana na kaiwa Mahbub kiss a kumatu, ya waro ido da cewan,"So kike muyi accident akan titi". Ina siririyan dariya na ce,"Ina sonka Mahbub, Ina sonka Miji na gari, Ina sonka ɗan aljannah, ina sonka Abu Ayman da Ajmal da Umarul Faruq, Allah ya ƙara mana lafiya da nisan kwana, ya dawwamar da mu a cikin farin ciki da jin daɗi har abada".

"Amin ya hayyu ya qayyum Ummu Ayman Wa Ajmal Wa Umarul Faruq Wa Sauma Wa Nasrin".

Ya faɗj hakan yana min ƙayataccen murmushin da ke nuna shimfiɗaɗɗiyar soyayyata a fuskarsa, tare da kamo hannuna ya riƙe yaci gaba da tuƙin a haka.
_______________________________
*_ALHAMDULILLAH! ALHAMDULILLAH! ALHAMDULILLAH! Dukkan yabo da godiya su tabbata ga ubangijin talikai majiɓincin al'amuran bayinsa...A yau 15-Dec-2023 na kawo ƙarshen labarin ƘAYAR RUWA Book 1-3, wanda na fara rubuta shi a ranar 1-Oct-2023, labarin da ya samu rubutu, wallafawa, ƙirƙira, tacewa daga gare ni Halimatus-Sa'adiyya H Zakariyya(Halima.hz), ina roƙon Allah nah da ya bani ladan faɗakarwar da nayi a ciki ni da waɗanda suka karanta ba ki ɗaya, sannan ya yafe mana kuskuren da na rubuta kuma ku ka karanta._*

*_Sannan ina miƙa godiya da gaisuwar ban girma na musamman gare ku Masoyana, waɗanda suka yi dafifi wajen sanya kuɗinsu su mallaki wannan labarin nawa, na sani tabbas ƙauna da cancanta ne yasa hakan, na kuma miƙa jinjinata a gare ku, tare da roƙon jalla wa'azza ya ninka muku abinda ku ka kashe, Allah ya faranta muku yasa wa halal ɗin ku albarka...Ina mana fatan samun dacewa a rayuwarmu, iyayenmu waɗanda suka rasu Allah ya jiƙansu da rahmarsa, wa'anda ke raye kuma Allah ya ƙara musu lafiya da nisan kwana, ya kuma sa suyi kyakykyawan ƙarshe mu da su baki ɗaya._*

*_Ba ya ga haka zan yi amfani da wannan dama wajen neman yafiyar duk wanda na ɓatawa bisa kuskure ko kuma cikin sani, tafiya ce da muka yita miƙaƙƙa, ɗan Adam ajizi ne, zai iya zamana na ɓatawa wani cikin tafiyar, ba fito na fito muka yi ba, ba cecekuce ba, koma dai ta ya ta kasance ina roƙon ku da a yafi juna don Allah, nima idan akwai wanda muka taɓa samun saɓani haƙiƙa ban riƙe shi ba, batu na yafiya ne kuma na yafe sai fatan Allah ya yafe mu gaba ɗaya._*

*_To ban sani ba ko zan ƙara fasowa nan gaba da wani sabon labarin, amma dai zai zama da kamar wuya gaskiya, dalili kuwa sau ɗaya na ke rubutu a shekara, to ban ce ba amma dai ku fi dakona a tafiyar team fitattu biyar na gaba wato next October 2024 idan Allah ya kaimu. Na bar ku lafiya, Halimahz taku ce domin ku ɗin nawa ne, ku ɗin mutane ne na musamman a gare ni, idan ba ku sani ba ku sani ina yi muku son so fisabilillah._*

*_Ƙofar aika saƙo gare ni ta lambar wayata a buɗe take gareku a ko da yaushe, sai dai don Allah kar aji ba daɗi idan aka samu jinkiri na bayar da amsa, kun dai san yanda al'amuran suke, dole sai mun dinƙi yiwa juna uzuri, uzuri yana da matuƙar daɗi a rayuwa, ko shawara na ta shi bayarwa na kance da mutum ka zama mai yin uzuri a rayuwa. Murmushi ɗauke a fuskata na ke cewa da ku Bissalam, Saduwar alkhairi._*

*Tauraro nawa za ku bawa labarin?*

Halimahz
07018098175
Chapter 113 · 0% Book details