← Book details Ƙayar Ruwa 2&3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 87 OF 113

Sashe 87

Ƙayar Ruwa 2&3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Kwanansu biyar a can, ranar da suka dawo kuwa suna bawa Ummani labarin gidan, sai santinsa suke yi su maza ma kenan, Anty Shafa da su Anty Lubna da Maman Khairi duk sai lokacin suka ji rashin jin daÉ—in da Abbaa bai bari sun je tare ba, shi kuma yace ne da akwai Æ´an uwa acan ne sai a tafi da su, to ba za'ai rashin hankali ba kawai aje a tarewa mutum a gida, matarsa ma ba zata ji daÉ—i ba.
Abbayo na faɗin wallahi Matar Salim ɗin tana da matuƙar kirki, haka ta karrama su kamar ƴan uwanta, motsi kaɗan sai ta aiko yaranta su tambaye su ko suna da buƙatar wani abun, abinci kuwa har ci suka yi suka ture, yace kuma idan suka yi aiki suka gaji da kanta take zuwa tace musu ga babban falo can ta buɗe musu ko za su yi kallo, iya kwanakin da su kai sun mata shaida me kyau.

Da daddare na samu Abbayo ina tambayansa ya fasalin gidan yake, yace min babban gida ne flat ba bene, ɓangarena bedroom uku ne kowanne da banɗaki a ciki, sai falo biyu da kitchen, amma fa kowanne ɗaki tafkeke ne, Yace babu laifi Sale yayi ƙoƙarin yin kaya masu kyau don duk zubin kayan turkey yayi sai kallon ƙurulla ne ma zai sai za a gane b kayan ƙasar waje ba ne, kuma bedroom biyu dukka an zuba kaya a ciki, dama yanda muka yi da su nace idan sunje sunga bedroom yafi ɗaya su kirani su faɗa min sai na tura kuɗi ayi min na ɗaya ɗakin ko ba mai tsada ba, hakan kuwa aka yi da ike ina dashi kuma ina adani na tura dubu ɗari biyar nace sai ɗakin ya zama shi ne nawa wancan kuma masu tsadar sai ya zama nasa.
Abbayo har da tsokanata wai Kudrat ta fini kyau ita fara ce ƙal kamar ba ƴar ƙasar nan ba, mene mene ɗinsa dai, sai naji bala'in kishi da haushi ya kama ni har da guntuwar ƙwallana, ranar kuwa har fushi nayi da Salim yana ta kirana naƙi ɗagawa, yayo text nayi kamar ban gani ba.
_________________________
_Kuyi haƙuri don Allah wallahi banji daɗin rashin post na jiya ba, tafiya nayi garin sakkowa a mota na faɗi na yi buguwan ƙashi a hannu, duk yanda na so na ƙoƙarta wallahi abin ya faskara, naga adu'oin ku na gode sosai da sosai Allah ya saka da alkhairi._

*B3ƘR10FT5*
Fuska na tamke ina ce masa bana son irin wannan maganan kuma ya daina taɓa ni, ban aune ba kuwa kawai sai naji ya manna min kiss a saman goshi, nan fa na diririce nayi saurin ƙwace hannuna a nasa don a yanda na ke jinsa in ban wasa ba sai ya rungume ni.

Fuskarsa ya shafa tare da cewan,"Baby mu tafi, mu tafi kafin a samu matsala, wannan ƙamshin na ki zai iya sawa na aikata ba daidai ba".
Na kalla ƙwayar idonsa duk nema ya ke ya rikiɗe, ya ɗan ban tsoro ganin har rumtse ido yake yana cije fuska da kyau, kuma kawai sai jin iskar bakinsa nayi a gefen bakina yana faɗin,"Baby ƙamshin nan fa ya tayar min da sha'awanki, ina neman gaza controlling kaina wajen turmushe ki akan katifan can".

Furucin nasa yasa duk jikina ɗaukan ɓari, na watsa masa harara ina ƙara cin magani, da sauri nayi ƙofa shima yay saurin fuzgoni har sai da na gogi da jikinsa, numfashi kawai yake saukewa kan ya kuma manna min kiss a kumatu, kana yace,"Ni Onochie ya zan yi da raina, yanzu haka ina ganin soft lips ɗin nan zan bar su, Baby please ko kaɗan ne".

Ƙwacewa nayi na fice da hanzari, sai daga baya ya fito yana dariya wai ni matsoraciya ce mene don an fara lissafi daga ɗakin Yaya Al'amin, na harare shi kawai ban ce masa komai ba. A hanya muna tafe muna hira abinmu ta masoya, yawanci duk yana magana akan kai ni, yana tunanin ko a fara kai ni can gidana daga can sai ya kai ni wurin iyayensa ko kuma a fara kai ni ta wajensu in ya so idan ya dawo sai mu wuce daga can, ni duk ma yasa na kasa sakewa da shi yau ɗin, fagge muka je wurin da zan amso ɗinkunana, ba yanda ban ba akan ya bar ni naje na karɓo da kaina yaƙi, wai ba ya so na fita wani me ɗaukarwa kan zunubi ya kalle masa halal ɗinsa, na ce ai ban riga na zama ba sai ya sha murr kawai ya fice ya bar ni a ciki, ya jima sosai a shagon ɗinkin kafin ya dawo yana ce min,"Kin sa duk an ɗauka yaronki ne".

Ina murmushi na ce,"To ai zan tura masa kuÉ—in É—inkin".

"Na ara za ki biya ni kayana, kuma cash na ke so in doller ba Naira ba".

Murmushi nayi ina masa godiya, Calido ya biya da mu yace min yana jin yunwa, nima dama yunwar na ke ji, ai kuwa tunda muka shiga ido ya dawo kanmu, É—aiku ne ba su tofa albarkacin bakinsu akanmu ba, har da masu satan ido su É—auke mu vedio Æ´an bani na iya a social media. KuÉ—i ya kashe sosai a abincin da muka ci, ni da aka yi bill ma sai da na kallesa na ce kuÉ—in fa sun yi yawa Salim, sai ce yay zai zare a sadakina da za'a harhaÉ—a masa gudunmawa, wannan kuÉ—in ogansa ne yake ta bushasha da su.

A hanya ya tsaya yay siyayyan kayan dubiya masu yawa, ya bani yace sai na kaiwa mara lafiyan, naji daɗi ƙwarai yau yanda yake ta min sai naji na ƙara son abuna tare da fatan Allah ya barmu tare, Zuwanmu asibitin Murtala na kira jikar Baaba Mai Ƙosai, ita ta zo ta rakani can inda suke kwance, ban wani jima sosai ba a wajensu na fito saboda na bar Salim a mota yana jirana.
lokacin da muka yi sallama da Baaba Mai Ƙosai wacca ta rakoni tana ta min godiya, ina tafe kawai naji an faɗo jikina an rungume ni, na kalla matashiyar budurwar da ke maƙale da ni ina sa hannu in jayeta a jikina, har ga Allah ban gane wacece ba sai da ta ga nayi mata kallon ƙurulla sannan tace,"Anty Sa'ida Rumana ce".

Ni da ta faÉ—i hakan ma sai ta saka ni a duhu, sai daga baya kuma na gane baki buÉ—e na ke kallonta kafin nace,"Rumana!". Sai ta É—aga kai da sake cewan,"Ehh Anty Sa'ida, Rumanki fa".

Mamaki ya ƙara kamani, lallai girman ɗan mutum ba wuya. "Rumana ke ce kika zama ƴan mata haka, Ya akai kika gane ni?".

Kawai sai naji tausayin yarinyar ya tsarga min, na sake rungumeta kafin ta zame a jikina tana cewa,"Anty Sa'ida ko a mafarki naji muryanki sai na gane, balle kuma na ganki duk da kin sauya, farko ban ganeki ba sai da na tsaya dai naji muryan da kyau kuma matar da ta rako ki tana faɗin sunanki, Anty Sa'ida naga kin ƙara yin kyau sosai kamar ba ke ba".

Wato har ga Allah ban tsammaci zan ƙara ganin iri iri Nazifi ba a duniyata har kuwa na koma ga Allah, ko fatan haɗuwa da wani na nasa bana yi, Murmushi nayi ina shafa kumatunta nace,"Me kike yi anan?".

Da yanayin tausayi tace,"Ai mun daÉ—e anan asibitin, an kwantar da Iyam bata da lafiya".

Nace, "Subhanallahi, Allah ya sawwaƙe".

"Anty Sa'ida ban san gidanku ba ina ta cewa zan zo, watarana ma na biyo hanya sai ban gane ba".

Na É—an murmusa na ce,"Ayyah, ya school to".
"Alhamdulillahi, yanzu ina jss 2 amma ba wancan makarantan da kika san muna zuwa ba, Jakara special primary school na ke zuwa yanzu, mun bar gidan Baba Ƙarami tunda jimawa".

Haba ni dai nayi mamakin yanda na ganta yarkace yarkace, a raina sai da nace kamar ba yaran Alhaji Nazifi ba, ashe sun koma gaban iyayensu, Allah masanin dalili. Muna hakan sai ga Atika ma ta iso, itama ta girma yaran duk sun zama ƴan mata ƙirji ya fara fitowa, itama muka gaisa da ita, sai dai ita ɗin ta kasa sakewa da ni sai satar kallona da take yi, Rumana kuwa ta maƙale min a jiki tana ta min surutu.
Maganan Rumanan ta katse min gajeran tunanina,"Anty yaushe za ki dawo gidan Baba Ƙarami, naji ance za ki iya dawowa".

Lallai yaro yaro ne, Rumana kuma na daga cikin mahaukatan yara, ni kuwa idan ba gawata ba me zai mayar da ni gidan Nazifi, ko da ike ƙarshen hauka na wurin me mafarkin zan koma gidan Nazifi. Mun gama magana da su ina cewa su yiwa Iyam ɗin sannu, zan wuce sai naji suna ga Mama nan, na ɗaga kai na hango Yaya na tahowa, yanda take tafiya bugujin bugujin kamar wadda aka tarewa duk matsaltsalun duniya akanta ita ɗaya, kuma har ga Allah ban shaidata ba saboda yanda ta zaftare ta rame, duk ta fita a hayyacinta, tun kafin ta ƙaraso na ɗauke kai nayi kaman ban ganta ba, ita kuwa baki buɗe ta iso gabanmu tana dubana sama da ƙasa, mamaki bayyane ƙarara a saman fuskarta tana tafa hannu tace,"Wa idanuna ke gane min, Sa'ida!". Ta faɗa da muryan da ya fito da sautin murna.

Wani yatsinen kallo nayi mata, fuskarta a sake ta gaida ni,"Sa'ida Ina yini". Na amsa mata babu yabo babu fallasa, sai naga jikinta duk yay sanyi, kamin ƙifta ido sai ga saukar hawaye saman kuncinta tana ce min,"Sa'ida na jima ina cewa zan zo gidanku sai dai abubuwan da ke ta faruwa yau da gobe na kasa samun dama, ashe da rabon anan zamu gana, kin ji labarin muna nan ɗin ne?".

Furucin nata sai ya bani dariya, wai naji labarin suna nan, to ko naji na zo nayi musu me?
Kaman ta gane zancen zucin da na ke yi ta sake cewa,"Wallahi ni dai sai naji nauyin ganinki, amma ina nan tafe gidan na ku".
Chapter 87 · 0% Book details