← Book details Ƙayar Ruwa 2&3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 61 OF 113

Sashe 61

Ƙayar Ruwa 2&3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Abbaa ya ɗaga kai a karo na biyu yaywa Major kallo na ƙurulla, sai kawai yaji kwarjinin mutumin ya dake shi, haka kuma nauyinsa ya kama shi, yay saurin ɗauke ƙwayar idonsa akansa yana me ƙara sunkuyar da kai ƙasa yace,"Ina sauraronka Ranka shi daɗe".

Major yaci gaba da cewa,"My son Salim na ɗaya daga cikin manema auren ƴarka a shekarun baya masu yawa da suka wuce, to kuma sai ubangiji ya ƙadarta cewa ba zata zama matarsa ba a wancan lokacin, shi ne a wannan karon ya turo mu gare ku da ƙoƙon bararsa yace a taimaka masa idan har wani bai riga shi ba".

Kan Abbaa ya É—aure, kafin ya kalli Baban su Safiyya yace,"Alhajin Allah ni ai har yanzu na kasa shaida É—an namu da kuke magana akai".

Baban su Safiyya yace,"Ehh to da yake a wancan karan ba mune muka zo ba gaskiya, amma ai ba zaka mance yaron da ya kawo kuɗin aure daga baya kuma aka karɓa da cewar ba zai iya jiran yarinya ta kammala karatun da aka ce masa ba, wanda kuma hakan ta faru ne duk ba da son ran zuƙatan kowa ba musamman shi yaron".

Abbaan yayi ƙayattacen murmushi da cewa,"Na tuna, na tuna hakan, to amma shi da yay wancan magana a lokacin baya ai ce na ke an wuce babin...".

Sai yay shiru kamar yanda duk suma suka yi shiru suna kallonsa. Zuciyar Major cike da fargaba da zullumin kar su ƙi amsar tayin su, don shi kansa ya kwaɗaitu wa ɗansa auren Sa'ida.
A lokacin ne kuma aka yi kiran sallar magriba, don haka duk suka miƙe Abbaa ya shiga gida Ummani ta zuba ruwa a buta guda biyu ta ba shi ya fita da ita, ta aika Yasmin wurin Umman su Hindatu ta ƙaro buta aka ƙara musu kafin Abbaan ya dawo ya karɓa masu sallaya, ita dai Ummani ganin yanayinsa na yanda yay sanyi kamar jikinsa ya mutu sai duk ta shiga damuwa da fargaba, tana tayi masa magana ma bai tsaya ya saurareta ba.

Don haka da sauri ta ɗauka waya ta kira Yashaik tace idan yana gida yay sauri ya leƙo gidan.
Ko a wajen sallah ma babu yanda Abbaa bai yi ba akan wani cikin su ya ja su sallar suka dage masa akan lallai shi ne zai ja su, haka yaja su sallar bayan sun idar kuma suka komo soron suka zauna, Abba ya amso fitila a cikin gida ya saka musu saboda soron yayi duhu a lokacin.

Bayan zaman nasu Alhaji Mukhtar yace,"Malam Salman na san kana tunani ne akan abun da ya faru a baya ko, to idan wannn ne kar ka damu, wallahi tallahi ko a baya Salim ba ya janye maganar aurensa da ƴarku ba ne saboda dalilin da aka faɗa, hasalima danne zuciyarsa yay ya haƙura a babu yanda zai yi saboda nuna masa da tayi na bata sonsa, shi kuma bai zai iya auran macen da bata sonsa ba, yana ganin idan ya nace aka yi auren zaman ba zai yi musu daɗi ba, saboda wannan dalilin a lokacin ya zo ya same ni muka yi magana ya faɗa min duk yanda suka yi da yarinya har ma ya fahimci akwai wanda ita take so, amma bai karɓi kuɗinsa don yay wulaƙanci ko tozarci ba, kum ahatta maganar da akayi a lokacin na cewa ya samu wata matar wallahi a lokacin babu wannan zancen anyi hakan ne duk don samun mafita".

Abbaa ya sake jinjina kai kafin yace,"To da wannan da wannan, don bayanin da ka min yanzu shi ne nake so na tambaya. Sai dai duk da haka akwai wani hanzari ba gudu ba, ƴata ba budurwa ba ce yanzu bazawara ce ita, wataƙila kuma bai san da hakan ba ne".

Baban su Safiyya yace,"Ya sani Malam Salman, ya san komai, sannan shima ɗin ba wai saurayi ba ne da aurensa, bayan aure ma har da arziƙin yara uku...".
[2/2, 07:47] Hlm: *B3ƘR03FT5*
Abbaa yay shiru yana nazarin kalaman na su, ba zai ƙi tayinsu ba, domin shi kansa ko a wancan lokacin Salim ya kwanta masa a rai, yafi gamsuwa da shi fiye da duk waɗanda suka zo neman auren Sa'ida, shiyasa ko a lokacin ya yarda ya amince aka karɓi kuɗinsa bisa sharaɗin da ya gindaya na cewar sai ta kammala makaranta, kuma ko a sanda suka zo karɓar kuɗin su bai ji daɗi ba fiye da adadin kalmomin baki, ba wai rashin jin daɗi na sun wulaƙanta su ba kan karɓar kuɗin ba, a'a rashin jin daɗin Ƴarsa ta rasa yaron kirki, yaro me nagarta kamar Salim, yaga haƙiƙanin soyayyar ƴarsa a ƙwayar idon yaron, haka ya tsinci raunin rasata a muryarsa, kuma gamsu ɗari bisa ɗari da irin shaidun da mutane suka yi akansa, ba tare da sanin iyalinsa da kowa ba ya ɗauki ƙafa yaje har garin Anambra state domin yayi kyakykyawan bincike akan yaron da iyayensa kuma duk suka samu shaida mai kyau, dama tsoronsa ɗaya bawa ƙabila auren ɗiyarsa.

To a lokacin da ace shi irin mahaifin da ke tilastawa É—iyansa abin da yake so ne ko da basa so, to da lashakka Sa'ida bata isa ta auri wani miji bayan Salim ba, to sai dai babu yanda zai yi shi uba ne me son farin cikin Æ´aÆ´ansa kuma me son dukkan abin da suke so ko da shi ba ya so in har wannan abu bai kaucewa shari'ar musulunci ba.

A yanzu tarin tambayoyi ne a ransa to amma zai bar su bincikensa ya ba shi amsa, akwai dai damuwa da fargaba a tare da shi. Major ya katse tunaninsa cikin magana me taushi irin ta dattijon arziƙi, yace,"Malam Salman Safiyya ita ta tabbatar mana da babu maganan wani akan ƴarka, bisa wannan dalili muma muka ga ya kamata muyi gaggawan zuwa kar mu makara. Kuma ni da kaina ina baka tabbacin insha Allahu my Son zai kula da ƴarka ba zai ci mutuncinta ba, yaƙini na ke baka akan hakan saboda na san waye yarona".

Da irin waɗannan maganganun Major ya ƙarfafawa Abba gwiwa. Wanda har Abbaa ya dinga jin zuciyarsa na buɗewa da yarda gami da farinciki, sai dai ba zai zama me fatan lamarin ya kasance ba har sai yayi istikara ya kuma sa Sa'ida tayi istikara itama.

Abba yay nisa sannu a hankali ya fara magana da cewa,"Tom ni babu abin da zance sai Allah ya zaɓa mafi alkhairi wa yaran namu. Sannan kamar yanda na faɗa muku ne Ƴata ba budurwa ba ce bazawara ce, saboda haka ni ban da hurumin da zan mata zaɓi kai tsaye domin kuwa shari'a ta bata damar yiwa kanta zaɓi".

Alhaji Mukhtar ya jijjiga kai da cewan,"Wannan haka yake Malam Salman, magana ce me kyau kayi".

Abbaa ya sake cewa,"To madallah, saboda haka ku faɗa masa cewa ya zo ya fara samuna domin ina da buƙatar na gana da shi kafin na basa damar ganawa da ita ƴar tawa su sasanta kansu".

Major shi ya fara cewa,"Tom shikenan zai zo É—in in Allah ya yarda, muna godiya".

Gaba ɗayansu kuma sai suka shiga yima juna godiya kafin suyi sallama su miƙe zasu tafi, Abba ya shiga ciki ya karɓo leda wurin Ummani yazo ya kwashe kunun ayar da ruwan ya zuba musu a ciki ya raka su da shi har mota. Kamar yanda suka ji daɗi suke ta godiya da irin karramawar da Abbaa yayi musu haka shima ɗin yake ta godiya a gare su. Bayan tafiyar su ya wuce masallaci bai dawo cikin gida ba sai da yayi sallar isha'i.

Ya shigo a lokacin Ummani na daga ciki tana lazimi, yay É—akin nata ya zauna daga bakin gado, kuma zuwan nasa yasa Ummani idda lazimin nata tare da juyowa ta fuskance tana nazarin yanayin fuskarsa kafin tace,"Abbaa lafiya dai ko?".

Abbaa na duban labulen É—akin kamar me son karanta wani abu a jikinsa yace da ita,"Ehh to lafiyar zamu ce".

Furucinsa nasa yasa gabanta faÉ—uwa, ta É—aga hijabinta ta cire tana aje carbi ta tashi daga kan dardumar ta dawo kusa da shi ta zauna. "Wani abu ne ya faru? Shi Alhaji Babangidan me ya kawo shi kuma mene haÉ—insa da su mutanen?".

Ganin duk ta ruɗe Abbaa yay murmushi yana me ɗora ƙafarsa ɗaya akan gado ya fuskanceta, fuskarta ya shafo tare da cewa,"Kwantar da hankalinki matata ta kaina, Sa'adatun Salmanu ba komai ya kawo su ba face alkhairi".

Ummani ta sauke doguwar ajiyar zuciya tana karayar da kai kafin tace,"Yanzu naji batu, amma da hankalina gaba É—aya a tashe yake, wallahi ka ganni tun da na zauna Allah na ke ta faÉ—awa, to ai Alhamdulillahi tunda ba wata matsala ba ce, amma me ya kawo su?".

Abbaa yace"Zuwan na su akan Sa'ida ne".

Cikin mamaki Ummani tace,"Sa'ida kuma? Na shiga duhu me ya faru da Sa'idan?".

"Kinga samu nutsuwa don Allah, zuwa suka yi da batun aurenta...".

Bai ƙarasa ba ta katse shi,"Kamar ya ban gane ba, shi Alhaji Babangidan ya zo maka da wannan zancen kuma ka tsaya sauraronsa? Ya manta mahaifin ƙawarta ne shi ko kuwa ya manta akwai aminta tsakanin matarsa da ni? To ban da ma mutuwar zuciya ina shi ina zuwa neman auren Sa'ida fisabilillahi, kuma kai bai ji kunyarka ba ma".

Tayi maganar cikin Firgicin da ya bayyana a muryarta zuwa ƙwayar idonta da ta fito waje. Wannan yanayin nata da kuma maganar da tayi sai ya bawa Abbaa dariya.
Aifa ran Ummani ɓace ta miƙe tana faɗin,"Dariya na baka kenan, to ba zai yiwu ba wallahi, yanda ya zo ya tafi ya tafi kenan babu wani aure tsakaninsa da Sa'ida, hauka ake yi?".

Abbaa yace,"To idan Allah ya ƙadarta faruwan hakan fa? Kuma ina ga ai ba haramun ba ne don ya aureta".

"Allah ma ba zai ƙadarta hakan ba ubangiji ai ya san daidai, kuma nima ai ban ce haramun ba ne sai dai ai akwai duba a lamarin, kuma ya ce ko ka faɗa masa babu wurin shigarsa?".

Abbaa na yin wata dariyar ganin duk tayi kicin kicin yace,"A'a na dai ce masa ya dawo gobe ya ganta, tunda yace yana so a ba shi dama ya shiga jerin zaurawanta ya fara kafa gwamnatinsa da wuri".
Chapter 61 · 0% Book details