← Book details Ƙayar Ruwa 2&3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 48 OF 113

Sashe 48

Ƙayar Ruwa 2&3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Haka kawai kuma a lokacin sai na samu kaina da fashewa da kuka wanda na rasa dalilinsa. Shi kuma sai ya samu damar faÉ—in,"kin gani ko, kema kina so ki dawo gare ni amma taurin kai ba zai barki ba, ki faÉ—a min yanzu idan ba ki yarda na dawo da ke gidana ba waye zai aure ki".

Take na katse shi da cewa,"Wanda yake sona, ko an faɗa maka kowa irinka ne butulu ƙasƙantacce, haihuwar rashin arziƙi".

Sai yay ƙasa da murya yana faɗin,"Haba Sa'ida ban sanki da halin rashin kyautawa ba, ki taimaka ki dawo gidana ina da buƙatarki".

Na kalle shi da jajayen idanuna na ce,"Da dukkan alama a make kake, ko kuma ƙwaƙwalwarka ta samu matsala, ni zan dawo gidanka? Ka manta ni ce wannan mara wayewar, wadda bata jin turanci, wadda bata zuwa office, wadda bata iya soyayya ba kuma ƴar talakawa me satifiket ɗin sakandire, daɗin daɗawa Juya wacca bata haihuwa, Nazifi Bala Mai Kalwa mene amfanin mace irin wannan a gidanka? Menene abun buƙatar dawowarta gidanka?".

Sai kawai na fashe da kuka sosai da yin maganar tawa, na duƙa ƙasa na ɗebi duwatsu ina jifansa da su na zama kamar wata mahaukaciya, kuma ganin zan masa rauni yasa ya bar ni ya tafi yana faɗin in sake tunani. Ranar haka na koma gida duk a firgice babu irin tambayar da Ummani bata yi min ba na kasa bata amsa har yau.

Numfashi na sauke ƙirjina na bugawa sosai na ce da Yashaik,"Me ya zo yi?". Na faɗa da rawar murya.

Sai yay murmushi yace,"Kwantar da hankalinki, wai ya zo ne akan maganar yana so ya mayar da ke, na faÉ—a masa har abada to muna haka ne sai ga Imam ya zo, shi kuma kin sansa zuciya a wuya kawai ya rufe shi da duka, yay masa jina jina a fuska har ta kai dai ga mun tafi station, don da ace kuna tsakar gida zaku ji yo hayaniya a waje".

Idona ya cika da ƙwalla na ce,"Ku yi haƙuri Yashaik duk ni naja muku...".

Ya katse ni,"Kinga duk manta da wannan karɓi wannan".

Na sa hannu na karɓa envelop ɗin da ya miƙo min, ina ƙoƙarin buɗewa yace,"Bayan mun dawo Abbaa ya kira ni, wai anyi sallama da ke ya fita sai ya tarar da wani akan machine, yace masa aiko shi aka yi ya bawa Sa'ida. To gasu nan dai duka biyun takardar admission ne ɗauke da sunanki, duk Scholership ne da aka ɗauke miki ɗawainiyar komai tsawon shekarun da za kiyi karatunki ki gama, ɗaya University of Targu Mures ƙasar Germany, sun ba ki nursing studies, ɗayan kuma Scool of health ce Emirate za ki karanci Community Health..Ba'a san wanda ya kawo takardun nan ba Sa'ida amma kuma akwai phone number a jikin envelop ɗin na kira sai muka yi magana da shi Director na makarantar Emirate ɗin, yace Allah ne kawai ya kai sunanki wajensu kar muji komai idan zaki karatu to ki fara shirye shirye, babu wani abu da za kiyi komai an gama miki ko screening ba zaki yi ba...To mun yi magana da Abbaa shima yace Allah ne ya kawo miki, naji ta bakinki idan kina so shikenan, idan ba kya so shikenan".

Tun fara maganar tasa kallonsa kawai na ke yi na kasa rufe bakina haka na kasa ƙifta idanu, ba zan iya tantance yanayin da na ke jina ba amma tarin tunanine fal a cikin kaina. Ta ina zan soma?....
*B2ƘR23FT5*
Yashaik ya katse gajeran tunanin da na tafi akan wanda ya zama silar wannan babban tagomashin da na samu. Yes na yarda Allah ne ya ba ni to amma ta dalilin wa? Tun farko fara kalaminsa na cewa wani ne yaje gida ba a sansa ba Safiyya ce kawai ta faɗo raina, sai dai kuma anya Safiyya zata yi suprising ɗina ta haka? In har ita ce to lallai asubar fari zata kira ni don tana da wutar ciki, duk da suprise ne zata kasa haƙuri sai ta kira ni ta tona kanta.

Maman Yasmin dai sai murna take yi baki yaƙi rufuwa, hannu ta ɗaga sama kawai tana godiya ga Allah, Yashaik yace,"Autarmu ba ki farin ciki ne?".

Nayi figigit na ɗaga ido ina dubansa da fuskata wacca murmushi ya wanzuwa a samanta. "Ina farin ciki sosai Yashaik, kawai dai na rasa ta yanda zan kwatanta murnata, ban san yama zan yi ba, abun da ban taɓa tsammani ba ne Yashaik".

Sai kawai hawaye ya sakko min bisa kuncina, hawayen farin ciki masu sanyi da sanyaya zuciya.
"Yashaik amma ka faÉ—a min gaskiya wane yay min hanyar samun admission É—in nan? Ni dai ku na ke kawowa a raina kai da Yaya Imam domin kune ku ka dage akan lamarin karatuna, wanda ko da yaushe cikin shige da ficen yanda za'ai na samu gurbin karatu kuke yi. Na kasa yarda da cewar dalilin wani daban da bamu da haÉ—i da shi na samu, ku É—in ne dai Yashaik domin kune jigona".

Ya murmusa da cewa,"Kin san idan mune kai tsaye ba zan tsaya ja miki rai ba zan faÉ—a miki gaskiya, amma na san idan kika ji daga bakin Abbaa za ki fi gasgatawa, yanzu dai ta shi ki wuce kar ki makara".

Kai na girgiza cikin wani irin yanayi na nuna tsantsar farin ciki da jin daɗi na ce,"Yashaik makarantar yau kuma ai ta mutu, da ma voluntry ne saboda haka suyi haƙuri".

Na faɗa ina miƙewa nayi ƙofa, Maman Yasmin tace,"Ehh lallai ne sannu hamshaƙiya, ki kwanar min a gida ba za ki min aiki ba za ki wuce, to dawo ki min wanke wanke, ni babu ruwana da wata Auta".
Ta faÉ—a da sigar tsokana, ni dai ina dariya kawai na fice don Alla Alla na ke na ganni cikin gidanmu, don na tabbatar ba mafarki na ke yi ba.

A soro na samu Abbaa ya fito zai wuce kasuwa shi da Yaya Imam wanda ke riƙe da ledar kayan Abbaa da yake fita da ita. Kawai a lokacin sai naji tamkar na rungume Abbana, amma duk da haka na kasa controlling kaina na faɗa jikin mahaifin nawa kunya tattare da ni, yayin da naji wani irin abu ya tsarga min a dukka ilahirin jikina, tabbas na sani ƙaunarsa ce, soyayyarsa ce, tausayinsa ne.
Shima muryarsa na bayyana amon tsananin farin ciki naji ya É—ora hannunsa saman kaina yace,"Ko ranar É—aurin aurenki ban ga farin ciki da murna irin haka a tare da ke ba Likitata".

A kunyace na zame jikina ina durƙusawa na gaida shi. Ya amsa min as usual yana saka min albarka, Yaya Imam ma na gaida shi. Sai Abbaa yace,"Lafiya ba ki tafi makarantar ba?".

"Abbaa ai ba zan iya zuwa ba ne yau, dama ina ta cewa Allah yasa baka fita kasuwa ba, Abbaa Yashaik ne yake faÉ—a min wata magana da na kasa gama yarda da ita sai naji daga bakinka duk da shima na san ba zai min wasa ba".

Yace,"Yanzu muke zancen na ki ai da Babarki, dama ina ce sai kin dawo daga makarantar ne, muje to cikin, sai kika ga rabo daga Allah ko?".

Yanda ƙarashen zancen nasa ya fita da wani irin emotion sai naji idona ya cika da ƙwalla, ni kuwa wanne irin rashin kyautawa na yiwa Abbaana, ashe haka na hana shi farin ciki, ƙwarai ba zan yafema kaina ba tun da har na zaɓi farin cikin Nazifi fiye da na Abbaana, kuma Allah ya isa tsakanina da shi da ya riƙe min hakkina na kuɗin makarantata da Abbaa ya bani ya hana ni, ai dama ba kyauta na ce na basa ba, idan da ya bani hakkina da yanzu wata maganar ake a karatuna, amma babu komai ga shi Allah yay min sauyi mafi alkhairi.

Muna shiga ciki na samu Ummani na wanke wanke, tana ganina sai naga itama fuskarta cike da annurin da ya wadatu da farin cikin da ba zai misaltu ba. Na faÉ—a jikinta ina cewa,"Wai duk ya na ganku cikin farin ciki, kar dai da gaske ba mafarki na ke ba".

Ta tsame hannunta cikin ruwan kumfa tana cewa,"Ai ko mafarkin ne yi adu'a ya zama tabbatace Sa'ida, wannan Al'amari ba zamu so ya tsaya iyaka mafarki ba, jiya ni da mahaifinki kasa runtsawa muka yi saboda farin ciki, wallahi ido biyu muka kwana muna ta adu'a don gani muke kamar mafarki ne ko kuma saƙe saƙen zuci ne da ba'a rabo da shi tun da an saka lamarin karatun na ki a rai".

BuÉ—ar bakina zan magana Yaya Imam ya zunguro ni ganin Zainab Æ´ar wajen Baba Tijjani ta taho. Muka yi shiru dukanmu ba don komai ba sai don dai ka san irin mutanen da kake tare da su dole ya yi takatsantsan.
Muka shiga ɗakin Abbaa, ina maƙale jikin Ummani Abbaa ya kira sunana da cewa,"Sa'ida kinga lamarin ubangiji ko, wallahi yanda ake ta kai komo a karatun nan na ki shiru har na fidda rai na ce ƙila ba ki da rabo, ƙila Allah bai rubuta burina zai cika akan karatunki ba, ashe tuni Allah ya amsa adu'a, lokaci ne kawai zamu jira kuma ga shi ya zo, Allah Allah yasa alkhairi ne".

Duka muka amsa da amin yayin da na ce,"To Abbaa wai shi wanda ya kawo takardun waye?".

Abbaa yace,"Wallahi ban san shi ba Sa'ida, don kansa ma a ƙasa ni ba zan iya shaida shi ba, ga mahaifiyarki nan da na karɓo envelop ɗin na dawo wullar da shi nayi ce na ke irin shashashun samarin nan ne masu aiken wasiƙa, sai ta dage akan cewar a dai duba a gani, shi ne fa da Sa'id ya shigo na ce ya duba ya gani sai yake cewa ai wai takardun makarantarki ne. Na ce ina ai ba zai yiwu haka kawai bamu san mutum ba ya zo ya kawo takarda yace wai ya samar miki makaranta, mu ai ba iyayen banza da wofi ba ne, to sai kuma ga wani ɗan kati a jiki ya ɗauka ya kira lambar sai wanda ya ɗaga wayar yake cewa shi ko menene wani abu dai dareta ne ko?".

Ni da Yaya Imam muna gajeriyar dariya muka ce,"Ehh Abbaa director".
Chapter 48 · 0% Book details