← Book details Ƙayar Ruwa 2&3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 37 OF 113

Sashe 37

Ƙayar Ruwa 2&3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ko kusa ba na fuskantar kyara ko hantara a cikin gidanmu ba, ba ya ga sabuwar soyayya da tsantsar kulawa ma da iyayena da Yayyuna ke ba ni, ko da yaushe cikin nuna damuwarsu gare ni suke na me na ke da buƙata, motsi kaɗan me na ke so, hatta mahaifiyata ba ta so ma na ke aikace aikace. Umma da yaranta ne ma suka so su saka ni gaba da habaici da yada magana wai na kaso aurena saboda ina so nayi yawon zawarci irin na ƴan iskan mata, wani sa'ilin kuma su ce rashin haihuwa yasa aka sako ni, ni dai bana taɓa daga kai na dube su haka ban taɓa nuna na san suna yi ba, Ummani ma bata taɓa bi ta kan Umman ba duk da irin maganar da take yada mata me zafi wai ai da ban kaso aurena na fito ba saboda yanzu dai babu wanda zai aure ni sai dai na ƙare a haka tunda bana haihuwa, kuma ga shi ma ban da karatun boko mazan yanzu kuwa wayayyiyar mace suke aure, saboda haka ya kamata ta saka ido akaina saboda kar na fara yawace yawacen banza don ranar nan ma taji wajen masu shayi ana faɗin daga mutuwar aurena ko gama idda ban yi ba na fara yawon iskanci.

Aikuwa ran Ummani ya ɓaci da maganarta, suka kama hayaniya har sai da Kaka ya fito ya tsawatar musu, Ummani tace to lallai fa yaywa Umma tsakani da ni babu ruwansu da zaman da na ke yi a gidan, su ɗauke ido akan ƴarta idan ba haka duk abin da tayi mutum shi ya siya da uwar kuɗinsa, a daren ranar kuwa Kaka ya tara dukka gidan Iyaye da Ƴaƴa ya jawa kowa kunne, yace duk wanda ya kuma ɗaga ido ma ya kalle ni ya furta kalaman bazawara sai ya bar gidan, Abbaa ma yace duk wanda bai ɗauke idonsa akan ƴarsa ba lallai zasu yi rigima ta ban mamaki, to tun sannan fa na samu salama a wajensu, babu ruwansu da ni nima babu ruwana da su, Umma ko magana ma bata min idan na gaida ita sai ta min banza, saboda haka kwata kwata ma na daina ko zuwa ɓangarenta, iyakata wajen Umman au Hindatu.

Hankalina ya kwanta bani da wata damuwa, daga na ci sai na kwanta sai hira da mahaifiyata, wanda hakan ke ƙara kawar min da duk wani tunani da zai iya fama ciwon da ke a zuciyata, hatta Safiyya da suka zo ita da Hassana Tijjani sai da suka min tsiyar wai har na fara kumatu, kuma wanne man bleaching na ke shafawa, wanda kuwa duk ya san batun mutuwar auren sai yace Allah ya saka min, da can bai san bana haihuwar ba sai yanzu da yay kuɗi shi ne zai juya min baya.

Abbaa kuwa watana ɗaya ya fara bani ƴan kuɗaɗe ina ajiyewa duk sanda ya fita ya dawo, yace da zarar na kammala iddah sai na koma makaranta na ci gaba da karatuna kafin Allah ya kawo mijin aure, ni kuwa a zuciyata babu wani lissafi na aure, ai tuni na gama faɗawa zuciyata na gama yin aure kuma, buri na bai wuce rayuwata ta inganta ba, na koma makaranta nayi karatu sosai na samu gogewa nima na zama cikakkiyar mace ƴar zamani mai ji da kanta, sannan na samu aikin yi me gwaɓi wanda zan tallafawa mahaifana da su kan su Yayyuna da sauran al'ummar musulmai.

Wata rana muna zaune Yaya Al'amin ya zo yana faɗawa Abbaa cewa akwai scholership na school of nursing jigawa, abokinsa ne suke bayarwa yay masa magana yace zai yi magana a gida idan an yarda sai ya karɓawa ƙanwarsa, Abbaa dai yay shiru bai ce komai ba ni kuwa ina ta murna, bayan kwana biyu da maganar hakan sai Abbaa ke cewa a'a ba ya so nayi nisa, in ace dai nan school of nursing ne ta kano kusa kusa sai ya bar ni na tafi, amma shi ba ya son in da zanje na zauna ba zai samu kwanciyar hankali ba.

Makaranta dai kowacce iri ce indai a kano ce to za'a sama min na je, wacca zan ke zuwa ina dawowa amma ba ta kwana da zan yi nesa da su ba.
Ranar da na fita a iddah Yaya Imam ya zo da zancen cewa ya tambaya min wata makarantar islamiya anan farkon layinmu zan ke zuwa ina koyarwa kafin na koma makaranta, nayi murna sosai da sosai nayi ta masa godiya, a washegarin ranar kuwa na fara zuwa.

Da ɗan kuɗin albashin da suke biya muka ja jarin kunun aya ni da Ummani, Abbaa ne ma yaje har makarantar almajirai ya samo almajiri bisa izinin Malaminsu, idan aka taso su ƙarfe goma zai zo ya ɗauka kular ya fita titi kafin ƙarfe ɗaya ya ƙare har ya dawo, kuma Alhamdulillahi sosai ake ciniki Allah kuma ya saka mana albarka, da kuɗin sau tari ma ake cefane idan Abbaa bai da kuɗi.

****Yaran duk sun fita hayyacinsu tamkar wasu marayu marasa galihu, yanda ka san basu da uwa ba su da uba a raye, zaune suke a falo sun yi jungum jungum, kana ganinsu kasan muguwar yunwa ce ke ƙwaƙularsu kuma ba su da yanda za su yi, kallo ɗaya ba sai ka ƙara na biyu ba za su yi bala'in baka tausayi, rabon su da abinci tun guntun biredin da suka samu suka ci da safe, shima Abbansu ne ya rage ya kira su suka ɗauka ba don bai san ba su ci ba sai don ƙara musu.

Iyam ta fito a É—akinta ta samesu tana cewa,"Kun duba kitchen É—in babu sauran garin kwaki?".

Atika ta buÉ—e ido ta kalleta a wahalce tace,"Babu fa na faÉ—a miki, tunda Anty Sa'ida ta tafi kinga an kuma kai wani abu cikinsa ne, idan kina da kuÉ—i ki aika a siyo mana indomie kawai, ai akwai sauran gawayi a baya, kuma gaskiya ki faÉ—awa Abbaa kawai Anty Amarya ta cire girki da mu tun da bata son bamu, sai muke yi da kanmu ko Anty Faty ta dawo nan".

Ta faɗi hakan tana matsar ƙwalla tare da dafe cikinta. Rumana dai na gefe bata iya cewa komai ba sai kallo da ido, ko da yaushe haka take bata da bakin magana, yarinyar ta rame sosai duk tayi ƙashin wuya tayi baƙi saboda wahala. Iyam ta zauna kan hannun kujera ta rafka tagumi, can kuma ta miƙe tayi ɗakinta tana cewa,"Bara mu gani".

Ɗakinta ta wuce tana faman laluben kuɗi, duk kuwa da cewa ta san ba ta da ko da sile, amma tausayin yaran yasa duk ta kiɗi me, ita ba ma ta kanta yunwa kam har ta saba zama da ita, Nazifi bai damu da bata kuɗi ba yanzu saɓanin da kullu yaumin naira dubu biyu zuwa uku sai ya ɗauka ya bata duk sanda zai fita, idan ma ya mance bata mantawa Sa'ida kan bi shi ta karɓo ta bata duk da a lokacin tana tsaka da tsangwamarta, to in ace da kuɗin da sai suke samu suna siyo wani abin suna ci da rana.

Wata huɗu kenan da tun bayan sakin Sa'ida al'amura suka canja a cikin gidan, ga ɓangaren masu son zuciya ba za su faɗi gaskiya ba amma tabbas shi kansa gidan da yana magana zai faɗi cewa anyi rashin nagartacciyar mace.

Zahra'u irin rayuwar hutun da ta taso a gidansu ita take yi a cikin gidan, bata son yin duk wani abu da zai wahalar da ita, girki kuwa dama ita ko a gida ba yinsa take ba sai ma da za'ai aurenta ne Yayar Mamanta ta takura akan sai ta shiga catering school, a babu yanda zata yi shi ne taje ta koyi girki, kuma ita babu wani abu da take ƙiwan yi sama da girki, balle da taga tana da uwar kuɗinta miji ma ya sakar mata ATM saboda haka kashewa cikinta kawai take da ciye ciyen order, hatta shi kansa tafi yi masa ordern abinci ta juye a flask a zuwan ita tayi, dama tana da chef ɗinta a hannu duk ranar da ta tashi zata ce da ita ga abincin da za'a mata zuwa yamma a kawo mata.

Tafiyar Sa'ida babu jimawa ƴan aiki suka yi tafiya ƙauye kuma har yau ba su dawo ba, ita kuma ganin akwai su Atika yasa bata damu kanta ba don dama bata shiri da yin shara da sauran ayyuka. Ita abin da ta sani taci ta kwanta ta danna waya, ranar da take da fita aiki ta fita, yarinya tayi kuka ta bata nono ta sha, idan goyo ya kama ta sauka ta miƙawa Kakarta ita, share share da wanke wanke da goge goge kai duk wani aiki na cikin gidan ta tattara shi ta barwa Rumana da Atika, yaran basa hutawa sam domin kuwa duty ta raba musu, da zaran Nazifi ya fita idan weekend ne zata tsawatar musu akan su yi aikinsu da gaggawa kafin ya dawo daga masallaci, idan kuma working days ne nan ma ba zata taɓa ko tsinke ba har sai yaran sun dawo a makaranta suyi aiki, idan ranar zata fita aiki zata ce musu idan ta dawo ta tarar ba su gyara wuri ba sai ta sumar da yaro.

Batun abinci kuwa dama ba'a magana, ba ko da yaushe suke samun ci ba har na safe kuwa, gwarama na dare wannan ta kan basu kullum shima kuma saboda Nazifi yana gidan ne, amma da safe in suka shirya za su wuce makaranta zata kaɗa musu worning da cewa kar su kuskura su nunawa uban ruƙonsu basu yi breakfast ba, dama ta faɗa musu ba ubansu ba ne uban ruƙonsu ne dan haka ko Abbaa da suke ce masa kar ta ƙara jin sun kira shi da haka, suke faɗa masa irin sunan da sauran suke kiransa Baba Ƙarami, idan nasa yaran sun tashi za su ke ce masa Daddy.
Chapter 37 · 0% Book details