Sashe 103
Ƙayar Ruwa 2&3 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Yaranta ta sakar min su kamar nawa, ko daga baya sai da ta tambaye ni wanne suna na fi so suke kirana da shi na ce mata Mommy ɗin ma yayi ina so, ga yaranta a nutse ba rashin ji, wai irin ma idan ɗa yay ba daidai ba kishiya ta tsawatar masa kiga uwarsa na cin magani ko a hau rigima, inaa ai ita kawai kece uwarsa idan ma zama za ki akan yaro indai laifi yayi ba zata ji haushi ba. Abinci kuwa bata yarda wai muci abinci daban daban ba, a plate ɗaya zata zuba mana musa hannu muci mu ƙoshi, a wurin ta ma na koyi hakan, don farko idan nayi girkina kawai ina zubawa ne na ci, to ita kuma da ta sauke ko da safe ne zata zo tace min na taho muci abinci, tun banci yau da gobe dai da bata gajiyawa da min bismillah ba har na zo ma nima bana iya girki ba da ita ba, idan bata gida na dafa zan aje mata tunda ita aikinta kullum ne, week end ne kawai bata fita. idan damuwarta ta ɗakko ni zata zo ta zayyanawa tana cewa Momin Rofi'a bani shawara, ko Momin Rofi'a abu kaza nace yayi in yi?. Saboda yanda Rofi'a ɗin ke maƙale min kawai ta koma ce min Momin Rofi'a amma da Sisi Nah take cewa, Rofi'a ɗin ma yanzu a wurina take don tuni ta tattaro min kayanta tace mu ƙarata can. Idan baƙon sani ne ma kai zaka ce ko ni ce uwar yarinyar.
Haɗin kan kuwa da muka samu ba ƙaramin daɗi yaywa Mijinmu ba, dalilin hakan har kyauta yake yi mana, yace kyautan kun haɗe min kanku ne kuna zaune lafiya, yay tayi mana godiya. To mu kanmu mun fi jin daɗin yacca muke zaunen, ba fa mu san mu ƙule a ɗaki ba, a'a uzuri ne kawai ke kai ki ɗaki sai in bacci, amma falo muke yada zango, in kallo ne ayi in hira ce ayi, ayi wasa ayi dariya ba cin muutuncin juna ko ɓatawa juna.
To ni da banda Æ´an uwa ma a garin, ita da take da su sun koma kamar Æ´an uwana idan suka zo gidan, sai su zo kai tsaye su taho wurina su ce wurinki muka zo Momin Rofi'a.
Gaskiya da farko na so na bawa zaman namu matsala, ina iyakar yina wajen ganin na danne kishina amma sai na kasa, har ta kai ga wata rana lokacin watana guda, Salim yay tafiya ya dawo ni kuma naje kai Isioma asibiti taji ciwo a makaranta garin lilo, to dawowan da zai yi a wurina zai sauka, ai kuwa ina zuwa na tarar da shi can ɓangarenta ya baje yana cin abinci suna hirarsu, wannan abin ya ƙona min rai, zuciyata ta sosu, don me a ranata? Duk da dawowan bagatatan yay ai sai ya jira na dawo tukunna na samar masa da abincin da zai ci, mayunwaci ne shi da ba zai iya riƙe yunwar har na dawo ba, ko kuma idan ya zauna a ɓangaren nawa kashe shi za'ai? Haka na cilla musu ledan maganin Kudrat na min magana naja tsaki na fita.
Ai kuwa ranar na dinƙa masa banbami na tayar masa da hankali akan kar ya ƙara cin abincin kishiya a ranar shigata, ko kuma ya tafi zuwa wajenta, fuskarsa ta nuna ɓacin rai sai dai sam bai biye min ba, hasalima haƙuri ya shiga bani yana lallashina, amma na fututtuke masa na ɗaura gaba da shi, har ina cewa ni sai ya raba mana gida, haka muka zauna da shi har ya koma ba na masa magana, girki ma sai in yi inci kayana ni ɗaya.
Kuma tun wannan lokacin na ɗaukewa Kudrat kai itama na daina sauraronta har yaje ya kuma dawowa, acewata ai ita ta haɗa ni da mijina. Sai bayan dawowar tasa ne yaga bama mu'amala da juna, ya saka ido yaga idan tayi min magana sai dai na gaggaya mata magana ina faɗin makira munafuka macuciya, ranar kuwa ashe ya jini muka gauraya da shi a ɗaki, ranar naga ainihin Salim na san kuma wanene soja, na kuma san asalin kalmar tsayayyan namiji a gidansa, don nuna min yay akan matarsa bai ƙi ya sallame ni ba, kai ni ban ma taɓa tsammanin zan sake kwana a gidansa ba wallahi, har ya fita a ɗakin jira kawai na ke ya dawo yace na kwashe kayana na bar masa gida, ashe fitan kiranta yay itama ya haɗamu a falo yaci mutuncinmu gaba ɗaya tun balle ni, ita kuwa duk ta ruɗe hankalinta ya tashi akan yanda ya hayayyaƙo min, tayi ta basa haƙuri tana ba laifina ba ne nata ne, haka ta dinga kare ni a wajensa har sai dai da gaske faɗan ya koma kanta, kuma ta amshe sai haƙuri kawai take basa.
Yay fushi da ni fushin gaske, zan yi abinci yaƙi ci, in magana ya shareni, a zo bacci kamar ba mata da miji ba. Na shiga damuwa matuƙa, sai a lokacin na ke jin rashin kyautawar abinda nayi, to Allah na tuba mutumin da ke hidimta min, yake nuna tsananin so da kulawa, ya wanzar da ni a daddaɗar duniyar da na rasa a baya, ko bai ce kar na tada fitina a gidansa ba ai bai kamata ba ni a karan kaina.
Ai kuwa naji jiki da ɗauke min kan da yay, wancan karan ai ni kaɗai na ke gabata shi bai tsaya biye min ba. Naga ba zan iya da shariyarsa ba sam, ranar yana bacci na rungumo abina ta baya ina saukar da hawayena masu zafi a gadon bayansa, muryana ya fito da sautin tausayi da nadama ina faɗin,"Mahbub kayi haƙuri don Allah ba zan ƙara ba, ka yafe min laifin da na aikata, zan zama me kiyayewa insha Allah".
Yi yayi kamar bai san ina yi ba, yay kamar bai farka a baccin ba, sai da yaji ina kuka haiƙan sannan a hankali yace min,"Ba sau ɗaya na faɗa miki ba, ba biyu ba, amma kika take maganata. Ba na so So'ida, ba na son haifar da rigima wannan shine last da zan maimaita miki".
Rungumesa na ƙarayi ina cewa,"Kayi haƙuri anyi farko an kuma yi ƙarshe".
Juyowa yay yana ce min,"Kinga ko a musulunce zargi bai da kyau, idan kika biyewa zugar shaiÉ—an kuma yana raya miki abubuwa kina É—auka shikenan ya buÉ—a miki hanyar rashin samun natsuwa da kwanciyar hankali, ga shi ki kwasarwa kan ki zunubin zargi".
"Kayi haƙuri Mahbub ba zan ƙara ba i promise you". Na faɗa ina daɗa lafewa a jikinsa.
Washegari da kaina naje na sami Kudrat ɗin da niyyan bata haƙuri, amma matar nan ta inda na ƙara yarda da pure heart ɗin da take da shi rufe min baki tayi, alamu na bama ta so taji maganar, ta janyo ni na zauna kan kujera, ƙoƙarinta kawai sai ta kawar da batun sai take ta ɗakko min zancen bikin sister ɗinta, zamu je can zamu kwan biyu tunda Paapa(Salim) bai gari lokacin. Wallahi ba ƙaramin kunya naji ba, sai abun ya ƙara min ciwo, duk da haka sai da na bata haƙuri, amma hakan take ce min ita bata san ma anyi ba, idan ma anyi ta manta, nima in yi haƙuri don Allah. Tun daga lokacin ne kuma na sauka daga kan keken ƙayar da shaiɗan ya nemi ya ɗora ni akai, muka koma zaman mu lafiya.
Æangaren Family É—in Salim tsakanina da su sai adu'ar samun aljannah, sun É—auke ni tamkar Æ™abilarsu haka kuma sun mayar da ni kamar É—iyar su, dama Kudrat ta taÉ“a faÉ—a min haka Familyn Salim su ke wajen mayar da inlaw kamar su suka haifeta. Ku san ko da yaushe sai an kira anji ya muke, idan yau ni aka kira bayan mun gama gaisawa za'a ce na kaiwa Kudrat É—in, haka itama idan ita aka kira za'a ce ta kawo min duk dai dan aji ya zaman namu yake. Idan ba ya gari kuwa an dinÆ™a mana aiken abubuwa ba wai don babu a gidan ba, tsaban kulawa ne kawai, da zarar yau ya É—auke Æ™afa Sir zai kira mu da kansa kowacce yace mata ga kuÉ—i nan ya tura mata. Æangaren Æ™annensa kuwa ni ban san wani rashin kunyan Æ™annen miji ko rashin ladabi ba irin na hausawa, yanda suke girmama Yayansu haka muma suke girmama mu, ba su kaÉ—ai ba hatta Yayyunsa cikin girmama juna muke da su, Babban Yayansa Chibuzo kuwa mutumin nan ya mayar da mu tamkar iyalinsa, da yake bamu da nisa da su shima duk wani aike da zai wa iyalinsa zai sa a kawo mana, musamman Yaran duk abinda ya siyawa ƳaÆ´ansa to sai ya siyawa Æ´aÆ´an Salim.
Ni dai sai kewa ta gida kawai da ta zama dole, banda ina da iyaye a raye ai zai mance ne ma da garin Kano. Iyayena duk sanda muka yi waya da su tambayan farko ya kuke da abokiyar zamanki kafin ya kuke da mijinki zai biyo baya, kuma wannan na san dan sun san yana sona ne banda matsala da shi, ba kuma mayin sallama sai na kaiwa Kudrat sun gaisa musamman Abbaa, kafin yanke kira zai ce min kaiwa Kudrat, ba ƙaramin daɗi suke ji ba da sakamakon canjin da na samu.
Ƙarshe ma Abbaa sai karɓan lambar Kudrat yayi, sai dai naji tace,"Momin Rofi'a ɗazu muka yi waya da Abbaa yace yana gaida ke". Har na ke mamaki ganin fa ni bai kirani ba amma ita ya kirata.
Wata rana kuwa muna cikin kallo sai ce min tayi,"Da safe mun yi waya da Ummani, tana cewa aiken me zata saka a mota a kawo mana nace mata daddawa da kuka".
Ba shiri na juyo ina kallonta nace,"Amma kuwa kin cuce mu, aike tun daga kano mu ƙare a daddawa da kuka". Tana dariya sosai tace,"Idan ba zamu yi amfani da shi ba sai mu koma sana'arsa, za ki kyau da me siyar da daddawa, a bakin gate Paapa zai mana banch".
Na kira Ummanin ina cewa ni ban yarda da wannan batun ba, sai ce min tayi ai bani tace zata kawowa ba Æ´arta zata kawowa.