← Book details Ƙayar Ruwa 2&3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 106 OF 113

Sashe 106

Ƙayar Ruwa 2&3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Myy ba mafarki kike yi ba, zahiri ne, kuma a zahirin ma kina riƙe da takardan gwajin da ya bayyana kina ɗauke da ciki, kina ɗauke da halittar yarona a cikinki Myy, kin zama BabynBaby".

To kukan da ya zo min na menene? Kawai dai naji saukar hawaye kafin fitar sautin kuka ina damƙar gaban rigarsa na shiga girgiza kai ina cewa,"Mahbub ciki fa! Cikin haihuwa da ake samu a haifi yaro?, Mahbub ta ina zan same shi? Ni fa bana haihuwa, Mahbub akan rashinta na wulaƙanta, aka tsangwame ni, aka goranta min, aka daina sona, na rasa farin ciki da jin daɗi, 11years ban taɓa ɓatan wata ba ban taɓa ɓari ba, ko a mafarki ban taɓa ganin na haihu ba, sai da aka sauya min suna na koma Juya, Mahbub Dr ba result ɗina ya baka ba, ba nawa ba ne ka mayar mishi ya bani nawa, ka manta a America ma sun duba ba su ga ciki ba, kar mu yarda da wannan ba namu ba ne".

Na ruƙo fuskarsa ina ƙara girgiza masa kai. "Kar ka yarda, ka daina murna Mahbub, ba na so ka saka rai kuma a zo a datse maka farin cikin da aka saka ciki wanda ba zai tabbata ba, ban da ciki, banda ciki Mahbub, ni ɗin Juya ce haka suka faɗa".

Na faɗa da murya me raunin da ke taɓa zuciya, ina fashewa da kuka sosai me ban tausayi.

[2/2, 07:47] Hlm: *B3ƘR17FT5*
Salim ya rumgume ni, hawayena na ta sauka a bayansa, a hankali yake shafa kaina zuwa bayana, kuma cikin natsuwa ya shiga faÉ—a min tausasan kalamai da suka samar min da natsuwa. Haka na zame daga jikinsa, ina kallonsa da murmushin farin cikin da ba zai misaltu ba nace,"Nima zan zama uwa Mahbub, zan haifa da kaina, zan amsa cikakken sunan mahaifiya, ka tayani godiya ga Allah Mahbub".

Sai sabon hawaye ya sake min shatata, na miƙa hannu na janyo mayafina na yafa, na nemi taimakonsa ya sakko da ni akan gadon. Sallayar da ke kan durowar gefe na ɗauka ya shimfiɗa min, na fuskanci alƙibla na yi sujudu shukur, na jima ban ɗago ba hawaye kawai na ke ina miƙa godiyata ga Allah mai girma da buwaya, mai yin yanda yaso abisa dukkan komai.
Sai na samu kaina da kasa ɗagowa har sai da Salim ya ɗago ni, dole na shiga ruɗa ni, domin abinda ban taɓa tsammanin zan samu ba ne, kuma rabon da na cire rai da shi tuntuni.

Ko bayan aurenmu da Salim na nuna masa damuwar rashin haihuwata sai dai shi ata ɓangarensa ko da yaushe yana faɗa min tausasan lafuza ne na kwantar da hankali da ƙara miƙa lamura ga Allah gami da yin tawakkali da duk yanda mutum ya riski kansa a ciki, balle ma ni Rofi'a kawai da suka mallaka min halak malak ta ishe ni wallahi, sai ga shi kuma ashe ina da rabon samun nawa na kaina.

Ina ta ɗokin na karɓi waya na sanar da Ummani ashe tuni Kudrat ta riga ni isar da albishir, Ummani tsaban farin ciki sai da ta ɗauke wuta a sanda ake faɗa mata, domin su kansu iyayena sun fidda rai akan haihuwata, ganin a wannan auren ma cikin shekara ta uku babu wani labari, na su zaton ina daga cikin waɗanda Allah ya rubuta basu da rabon samun haihuwar ne har su koma gare shi. Ina daga zaune kan sallayar na kai hannu saman cikina, farin ciki na ke yi haka kuma mamaki na ke yi, wai ɗan mutum ne a cikina, sai yanzu ma batun rashin yin period ya zo cikin kaina, ni duk wannan kumburin cikin da na yi wallahi ce na ke tumbi ne kawai, don har tsokanata Kudrat ke yi da shi kansa Salim ɗin, to abunda bamu sa ran samu ba ne shiyasa cikinmu babu wanda ya kawo batun ciki a ransa, don har ina ta cewa zan nemi maganin rage tumbi, a lokacin ma har Maman Yasmin na faɗawa take cewa to ai na zama Hajajju ina cikin hutu da jin daɗi ai dole na yi tumbi.

Aunty Adamma da Mama A'i suka shigo fuskoki washe cike da murna, barka suke ta min, Kudrat kuwa faÉ—i take ai sai na bata tukwici zamu bar asibiti, na ce,"To Madam ai in bayarwar zan yi Paapa zan bawa".

"Noo ban yarda ba woo Mommy, ki bani kawai in ba haka ba kin san dai na san ai na ATM na ki yake".

Dariya nayi sosai, bata barni ba a dole sai da nasa Salim ya tura mata 10k idan mun koma gida zan ba shi, tunda wayata na can. Ni fa banji kunya ba sai da aka sanarwa da su Maa, duk sai naji kamar na nutse, yo ina ta murna kaman zan shiÉ—e ina na tuna wata jin kunya ma lokacin da muke magana da Ummani da Abbaa.
Sai da na ƙara kwanaki biyu a asibitin kafin aka sallame mu, wallahi har a sa'ilin gani na ke kamar daga baya za'a zo ace result ɗin ba nawa ba ne, ko kuma na tashi a bacci naga mafarki na ke yi, sai dai babu ko ɗaya daga ciki rabon nawa ne da gaske Allah ya ba ni, bayan tarin wulaƙanci da gorin da na sha a baya, idan na tuna sai na yi murmushi kawai a fili na furta,"Yau ga Juya zata juye nata rabon".

Naji ƙwarin jikina sosai kuwa don asibitin babban asibiti ne sun iya kula da mutum.
Maganar farin ciki ba a batunta ta ɓangaren ƴan uwa da abokan arziƙi, Family ɗin su Salim kuwa ka rantse karon farko kenan da Salim zai samu haihuwa, ashe su haka suke farin ciki da tarairayan mace idan tana da ciki ko da kuwa haihuwa ta ɗari zata yi, sai da na zama kamar wata ƙwai ɗanya saboda yanda ake ririta ni tun balle me abu da abunsa mijina abin ƙaunata.

Ƴan uwansa haka suka dinƙa zuwa yi min sannu, sai kowa ya zo an ce masa ciki ne sai yace au da ciwon ƴan gayu na ke aka sa su tasowa suyi tafiyayya.
Yara kuwa ko da yaushe suna tare da ni suyi ta kallon cikin suna faÉ—in,"Mommy yaushe za ki bamu Baby?".

Rofi'a kam ai ko bacci zamu yi yarinyar nan kanta na kwance kan cikin wai kar a ƙwace mata Baby, idan ranata ne yana wajena sai fa in tayi bacci ne zan mayar da ita ɗakin su Foridat ta kwan a can, dama haka muke da ita ko da yaushe ita tafi son bacci a wurina, Kudrat tace,"Ke kike shagwaɓata shiyasa take miki abinda taga dama ai, ke ƴa mummuna amma ki ta wani faman ji da ita".

Na ce,"Ehh komai za'a faɗa a faɗa, baƙin ciki kashe maƙiya".

Tasa dariya da cewa,"Ayi dai mu gani in tusa zata hura wuta, da Baby ya zo zamu ƙara juyawa mutum baya aradu".

Nima ina dariyar na ce,"Kar ki manta hajajju kullum ciki azkar muke, kuma bakinmu li'ilafi da yasin ko da yaushe, kinga kuwa haka zaku buga ku barmu, kuma indai muni yasin a fuskar Æ´aÆ´anki ya tare".

Cikin wasa da raha muke zancenmu, ni dai Kudrat ba kishiya ba ce a wurina ƴar uwa ce, kuma har zuciyata haka na ke jinta, don ƙwarai da mata za su daure a danne kishin zuciya to za'a zauna lafiya tsakanin kishiyoyi, ba faɗa ba tashin hankali, to ba kowacce mace ba ce kamar Kudrat musamman a wannan zamanin tunda ko a iyayenmu na da ai zamu gani, lafiya suke da kishiyoyinsu sai kaga har a rasa banbance ƴaƴan wance da wance tsabar haɗin kai. Kuma zuciyar kowa fess ake zama ba wadda ma ke tsayawa sauraron zugar mutane, Sai dai fa duk da hakan muma don mun samu jarumin miji ne tsayayye a cikin gidansa, mijin ƙwarai da bai nuna banbanci tsakanin iyalinsa, mijin da bai fito ya nuna fifikon wata ba, shiyasa na ke jinjinawa Mijina domin ya cika namijin ƙwarai.

Sai da naji daÉ—in jikina sosai babu wani ciwo da ke takura ni sannan Mama A'i ta koma gida. Ita da taji daÉ—in zaman ma so tayi har sai na haihu, Abbaa yay ta faÉ—an to zaman me zata yi, bacin ma makaranta zan koma. Ni kuma gani nayi zaman me zan yi dama tunda lafiya ta samu, ba wani wahalallan laulayi, saboda haka na yanke shawaran komawa makarantana, ranar da Mama A'i zata koma sai da naji kamar na bita, rabona da gida tun dawowarmu daga saudiyya.

Tsaye na ke gaban madubi ina duban kaina, Salim da ya fito daga toilet ya tsaya ta bayana ya rungumeni yana tusa hannayensa cikin rigata ya shiga shafa cikina. Ina kallonsa ta cikin madubin na ce,"Ranka ya daÉ—e Sir".

Yay min cizon wasa a wuya kafin ya amsa,"Na'am ranki ya daÉ—e Momin Unborn".

Nayi murmushin da ya zarce har zuciyata saboda daɗi. Na kai hannu saman kansa ina cewa,"Godiya ga Allah da ya bani ɗaya tamkar ya dubu, mijina abin sona abin alfahari da tunƙahona, jarumin da ya fi dukkan maza, gaishe da kai jigona, matakalar kwanciyar hankali da farin cikin iyalinsa, Allah ya bar mana kai ya faranta maka, ya bani ikon sanyaka farin cikin da nima kake sanya ni a ciki".

"Thank you for the praise Momin HuÉ—u". Ya faÉ—a yana manna min kiss a kumatu. Na juya idanu da faÉ—in,"Mahbub ko goma aka bani wallahi ina so, zan yi murna in farin ciki, ba zan ji wahalan kulawa da su ba, ba zan kasa tarbiyantar da su ba, Mahbub Æ´aÆ´a Rahma ne kai ka faÉ—a min da bakinka, kawai dai idan suka zama huÉ—un to haihuwa tare da kai".

Siririyar dariya yay da cewa,"Ni in haife su ta ina Myy?".

Hannu na kai na zungure shi ina faÉ—in,"Ta nan, haihuwan na zuwa zai buÉ—e".

"Ohhh kiji daÉ—in cewa na buÉ—e da yawa ko, ko da yake na fanjama neman maganin maza, in tsuke irin yanda kike tsukewa kina sawa na fita a hayyacina".
Chapter 106 · 0% Book details