← Book details Ƙayar Ruwa 2&3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 14 OF 113

Sashe 14

Ƙayar Ruwa 2&3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ya faɗi hakan yana ɗora hannayensa saman cikinta ya shiga shafawa. Tana murmushi ta janyo towel ta goge hannayenta tare da juyowa ta fuskance shi, in da hannayensa suka koma kan ƙugunta. "Sannu da dawowa". Kafin yay magana ta ƙara cewa,"Amma Derling anya ayi haka kuwa, shikenan kuma sai ka dinƙa baro office ba zaka zauna kayi aiki ba, yanzu idan Babyn ya zo ya ke nan?".

Ta ƙarasa maganar a shagwaɓance wanda hakan ke ƙara narkar da zuciyarsa akan sonta don shi bai ganin hakan akan Sa'ida, idan ma tana yi to bai masa kyau kaman na Amaryarsa.

"Hmm Swty kin san yanda na ke azabtuwa da rashinki kusa da ni kuwa. Kinga da ban san in fita aiki nayi ta zumuɗin dawowa gida ba sai yanzu da na sameki. Balle kuma da tunanina ya yawaita akan ajiyata, ke dai madallah da ƙoƙarin samar min abin da aka kasa samar min shekaru da shekaru".

Shafo fuskarsa tayi tana cewa,"Ina sonka ne da yawa shiyasa nayi iyaka ƙoƙarina wajen ganin na sama maka farin ciki, kuma in sha Allahu ba tare da gajiyawa ba zan ta haifa maka yara har sai kace Swty sun isa haka".

"Godiya na ke Allah yayi miki albarka". Ya faɗa yana ƙara janyota jikinsa da cewa,"Ina son wannan kwalliyar. Kin san Unborn yasa kwalliyar na ƙara yi miki kyau sosai".

Tayi murmushi me sauti da cewa,"Wato ma É—anka ne ke sawa nayi kyau?".

Hannunsa na shafa cikinta yace,"Tukunna ma wai me ya kawo ki kitchen?".

"Ina ƙoƙarin ƙarasa girki ne na bada akai maka office ashe ma kana hanya. Ban ji daɗi ba da ka dawo ban gama ba, kuma kaga Sa'ida ma...".

Ya ɗan ɓata fuska cikin nuna rashin jin daɗi ya ce,"Haka zamu yi da ke idan na fita ki ke satar baro ɗaki kina shigowa aiki? Ko kin manta likita yace ki huta ne, Swty ke da Unborn Baby kuna da buƙatar hutuwa, don Allah ki daina takura kanki, ga ƴan aiki nan da za su dinƙa miki duk me kike so, bacin nan ga Babaa Zulai da su Mubina, Sa'ida kuma ai ƙanwarta tana wajenta akan me za ki damu kan ki da ita. Ki daina don Allah kinga ko wanka ba na bari kiyi da kan ki so ban lamunce da shigowa kitchen ba daga nan har ki haifa min farin cikina".

"Derling ni gaskiya bana so ne kake cin girkin ƴan aiki, ko su Mubina kishi na ke da su akanka. Ka bar ni na samu lada tunda na sami lafiya ai, yanzu bana jin wani ciwo sosai, haihuwan ma a sauƙi zata zo in sha Allah".

"Ni dai ki huta, idan ba kya so naci abincin ƴan aiki zan kira gida idan sun yi abinci suke aiko mana, idan kuma Sa'ida taji sauƙi shikenan".

"A'a Honey ya kamata fa mu bar Sa'ida ta huta haka da ɗawainiyarmu. Kaga babu daɗi kar ta zo ta ƙulla ce ni ka jawo min baƙin jini a wurinta".

Bai sake cewa komai ba ya kama hannunta ya riƙe suka fita a kitchen ɗin, tana ta roƙonsa akan ya barta ta ƙarasa ta kusa gamawa amma bai saurareta ba. A falo ya tsaya yana ƙwala kiran Marawiyya ƴar aiki, wacca ta zo da saurinta tana duƙawa gabansa. Yana kallonta da faman kanainaye jiki a mayafinta yace,"Ki ƙarasa aikin da ke kitchen, Idan kika ƙara bari naga matata a kitchen tabbas zan sallameki ne".

"Kayi haƙuri Alhaji hakan ba zai ƙara fauwa ba".

Kamar zai duƙa ya ɗauki Zahrau sai ya fa tuna ba Sa'ida ba ce da yake rarumarta farat ɗaya, wannan da nauyinta sosai da har ƙirjinsa ke ciwo idan ya ɗauketa. Suna shiga ɗaki ya zaunar da ita kan gado. Ya wuce ya ɗauko magungunanta ya kawo ya bata da kansa kafin ya shiga mammatsa mata jiki wai alallai tayi aiki ta gaji. Ita kuwa tana yi masa wani irin kallo ta kwanta kan gado tana janyo shi jikinta.

"I am missing you Derling". Ta faɗi hakan wanda tuni jikinta ya fara tsuma domin sun jima ba'a je ga majiyar daɗi ba, tun satikan baya da jini ya ɓalle mata har akai tunanin ma ko ɓari ne amma da suka je asibiti sai likita yace da Nazifi ya ɗan barta ta huta, to tun sannan duk son Nazifi da ayi harka itama duk sonta sai dai su haƙura, dama ita ta fishi naci da ƙulafucin abun, gwara shi ma yana samu a wurin Sa'ida wanda hakan ke sosa ranta.

Cikin wani salo na kashe jiki tace da shi,"Honey wasa kawai, ina kewarka da yawa".

Lokaci guda kuma ta sauya labarin yanayin na su, ta birkita Nazifi ya rikice, shifa baƙaramin godiya yake ga Allah ba da ya ba shi Zahrau matsayin matarsa, Nazifi yana matuƙar bala'in son kasancewa da ita ko da yaushe.
Yana iya rantsewa bai san daɗin aure ba sai da ya sameta, domin duk wasu wasanni na tarwatsa ƙwaƙwalwa da jin kamar zai mutu sai da ya mallaketa ya san su, ita ce kawai take masa irin yanda yake buƙata, amma ita Sa'ida ko da yaushe a cikin jin kunya take da rashin sanin irin abubuwan da zata masa wanda za su fasa kwakwalwarsa, har ta barsa da tunani idan ya fita office ya kasa sakat sai ya dawo gareta.

Sai yanzu ya daina ganin laifin wata Malama da ke lecture tana cewa mata namiji yana tsananin son mace me kunya, ki zama me kunya da zarar an zo ga abin nana ki nuna masa ba ki san wata aba kunya ba, ki zama fitsararriya a wajensa idan aka zo harka, yauwa ina nufin karuwar gidan Oga.
Kuma tun da ta gama yi masa wasannin sai ɓacin rai ya maye gurbin baƙin cikinsa,saboda tunawa da yay yau zai koma wajen Sa'ida.
_____________________________________
*Gwarazan Labarai na ƙarshen shekarar 2023 masu ma'ana.*

*KWANTAN ƁAUNA*
Nana Haleema

*ƘAYAR RUWA*
Halimahz

*LOKACI NE*
Oum Mumtaz

*FARGAR JAJI*
Aisha Yabo

*WASA DA RAI*
Fadila Yakubu

Ɗaya ₦500
Biyu ₦800
Uku ₦900
Huɗu ₦1000
Biyar ₦1200

*Biyan Kuɗi Ta*👇🏻
6314170140
Fidelity Bank
Sa'adiyya Zakariyya Haruna

*Shaidar biya ta👇🏻*
09061794195

*Godiya tare da adu'an fatan alkhairi ga wanda suka sami damar mallakar littafanmu, son So fisabilillah🥰*

#TeamFitattuBiyar
[2/2, 07:47] Hlm: *B2ƘR06FT5*
_Hohoho wani girkin sai wajen macen da ta san kanta🥳 yo ai idan ana faɗar kalmar ƙamshi da ɗanɗanon girki sai dai mu ce a garzaya Spicerite.ng. Amarya da Uwar gida me kuke ta jira har yanzu ku ka kasa hargitsa tunanin Oga da kasa natsuwa har sai ya baro aiki ya dawo gida ya kwashi girki? Hajjaju na ce to ai ƙamshin kaɗai ma ya isa ki mallake Oga da shi, wannan sabon sirrin mallaka ne na ke baki😉amma fa idan kin inganta girkinki kawai ta hanyar amfani da kayan ƙamshin da ke ƙarawa girki armashi aji ƙamshin abinci har a maƙota😋, wai wai wai daɗi mazaƙwai ba Oga ba kaɗai hatta baƙin da suka zo suka ci girki sai sun ƙara satar hanyar dawowa don kawai su sake cin haɗaɗɗen girkin da aka yi amfani da sinadaran girki na spicerite.ng...wato spicerite.ng lamba ɗaya a fagen sarrafa maku kalolin ganyayyaki masu ƙara lafiya domin ƙawata girkinku💯...ba anan kaɗai ba kazalika sun sauƙaƙa maku hanyar sarrafa kayan girki da dama, irin su garin ɗan wake wanda ruwa kawai za ki zuba masa, niƙaƙƙen yaji, garin alala da ƙosai, niƙaƙƙen daddawa, garin kuka, kuɓewa da dai sauran su. Amarya da kike so kiyi zarra a cikin gida Uwar gida ta kasa gane da me kika mallake Oga maza tuntuɓi wannan lamba 08147302739 domin fara girki da kayan ɗanɗanon abinci na spicerite.ng ko kuma ki aika da saƙo ta shafin su da ke instgram @spicerite.ng._
__________________________________
"Ke dakata!".

Ummani ta tsawartar min da maganar da na ruɗe ina yi. Kafin a hankali kuma ta shiga faɗa min kalaman kwantar da hankali kaman yanda ta saba a ko da yaushe, tare da ƙara faɗa min cewa na dage da adu'a komai me wucewa ne. Sai da ƙyar na samu na iya tsayar da kukana, muna gama wayar na kwanta kan gado saboda yanda naji kaina na bala'in sara min, baccin ma sai ya gagara zuwa kamar yanda na ke so ta ƙarfi da yaji ya ɗauke ni.

Ina cikin juyi cikin tunane tunane wayata tayi ringing, ganin lambar Safiyya nayi saurin É—agawa, tana jin yacca nayi sallama a sanyaye ta danna ashar da cewar,"Wato sun kuma guma miki ko?".

Na ce,"Hmm Safiyya lamarin nan fa kwata kwata babu sauƙi". Nan na kwashe duk abin da ya faru a ɗazu na faɗa mata, ta dingi zage zagenta da cewa,"Wai ke ba zaki iya nunawa Nazifi ƴar daba ba ce ke, ki nemi abu ki ce zaki sassara shi idan bai sawwaƙe miki ba, haba wannan bala'i na kullum yaƙi ci yaƙi cinyewa, haihuwa ke za ki bawa kan ki ne. To wallahi ki nunawa Nazifi ke mahaukaciya ce, kuma har mahaifiyar tasa ki bar ɗaga mata ƙafa yanzu idan ya so ko mai zai faru ya faru kin dai ji me na faɗa miki ko, mata ƴar bala'i da miji a raye tazo gidan ɗa ta tare saboda dai ta hana ki sakat".

Nayi shiru ina jin sabbin hawaye na sakkowa ta gefen idona.
"Ni dai shawara na ke ba ki Beb, ki nemarwa kanki mafita tun wuri wallahi, ba zai yiwu kici gaba da zaman wannan ƙasƙantacciyar rayuwar ba, haba Miji yay maka, Uwarsa ta maka da ƴan uwansa, yanzu ta kai ta kawo ma lamarin ya haɗa har da kishiya. To wallahi gwara tun wuri ki zama mahaukaciya a cikin gidan nan, kiyi haukan da za ki hana kowa kwanciyar hankali, rashin mutunci waye bai iya shi ba, idan ma baka iya ba a wannan zamakin koyarsa kake, don haka ki daina barin miji yana taka ki son ransa Beb".
Chapter 14 · 0% Book details