Sashe 97
Ƙayar Ruwa 2&3 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Alwala nayi na fito ina tunanin ina ne gabas É—in, na É—auki waya na kira Safiyya ta faÉ—a min, itama har tana tambayana har yanzu Salim É—in bai shigo ba, na kashe wayana ba tare da na bata amsa ba don itama haushinta na ke ji, ina cikin gidan zata je ta wani tare wurin kishiyata.
Ina raka'an ƙarshe naji sallamarsa da kuma takun shigowarsa, ya ƙaraso ta ɓarin da na ke ya zauna a gefen gadon yana kallona. Duk da sallah na ke yi haka na haɗe rai daidai da lokacin da nayi zaman tahya, har na sallame ina jin kallonsa a kaina.
Bai min magana ba har sai da na gama tazbihi, da murmushinsa yana shafa tasa fuskar cikin zallar farin ciki da kuma annushuwa. Ni dai ban dube shi ba irin ban damu da zuwan nasa ba, sai dai fa ina kallonsa ta ƙasan ido, ya sauya daga kayan ɗazu ina ga ko da zamu taho ne ya canja, manyan kaya ne yanzu a jikinsa shadda dakakka irin kalar swizz less ɗin jikina blue, ya saka hula kalar aikin yayi kyau sosai dan kayan sun amshi jikinsa, shi kam kowanne shiga yayi yana yin kyau a ciki.
A tsammaninsa duk kunya ce ta hanani ɗagowa, nan kuwa bai san fushi na ke da shi ba da kishinsa, don me zai barni ni ɗaya, ita matan nasa ba jiddan walahairan suna tare ba. ya duƙo kai yana ce min,"Idan amarya ta idar ko zata iya bani aron kanta zuwa falo wajen ƴar uwarta?".
Yanda yayi maganar sai da gabana ya faɗi, haka na taushi kaina na daure ban nuna ba, sai naga ya tashi ya riƙe kafaɗuna ya miƙar da ni tsaye, kaina yana ƙasa still ban kalle shi ba, shi ya tallafo haɓata ya ɗago da fuskata, na sake kulle idanu don ji na ke kamar bana son ganinsa, bai kawo komai a ransa ba game da yanayin nawa yayi siririyar dariya yace,"Ko yaushe aka ɗauko wannan sabon salon ban sani ba, amma za'a yi min bayani ne muje mu dawo".
Ya faɗa yana riƙe da hannuna muka fita daga ɗakin yana gaba ina bayansa, zuciyata na ta ce min in koma in canjo mayafi maimakon hijab ɗin sallar da ban cire ba, don gani na ke na je a haka Kudrat zata raina ni, ko fa da nayi sallah yanzu sai da na roƙi ubangiji ya sassauta min zafin kishin da na ke ji, ya kuma hane ni biyewa ingiza uwar me kantu da zuciyata ke karanta min a cikin kai.
A falon muka tsaya ya saki hannuna ya wuce ya nemi waje ya zauna, Kudrat ma na zaune a kujeran da ke fuskantar shi da ƙaton hijab ɗinta ta duƙunƙune alamar sanyin daren na ratsata, kuma da gani ma daga bacci ya taso ta.
Salim ya shafo fuskarsa yana cewa da ita,"Sorry fa na barki da jira, na tadda tana sallah ne, hope babu laifi ko?".
Tana murmushinta na bata da matsala da yanayinta da ke nuna gajiya tace,"Ni na isa nace kayi laifi? To koma ba sallah take ba dan ka jima ai ba zaka yi laifi ba balle sallah guda".
Sai ta dube ni daga inda na ke tsaye, da zolaya tace min,"Sisi Nah idan nayi bacci anan to ki tabbata ke za ki É—auke ni ki kai ni É—aki".
Tun kallon farko da na mata na ɗauke sai yanzu da ta ƙara magana tukunna na kalleta a yatsine, kamar wata sauna wawiya sai murmushi take yi hankalinta kwance, lamarin dai ba daraja sam, an miki kishiya kina ta faman sakin baki da tusa kai. Sai da ya dube ni yace,"Wai sarauta kike ji da ita ne? Please have a seat my dear".
A fakaice na harare shi tukunna na taka sannu a hankali, zan zauna kusa da shi sai ya girgiza min kai da cewan,"Koma kusa da Æ´ar uwarki". Haka na koma na zauna kamar yanda yace ba don rai ya so ba, sai don kar na yarfa kaina gaban kishiya.
Na sunkuyar da kai zuciyata na zillo cikin yanayin da ban taɓa tsintar kanta a cikinsa ba, ko lokacin da Nazifi ya taramu kamar haka ni da Zahra'u ban tsinci kaina a yanayi na jin ciwon zuciya irin haka ba, ko kuma duk amarya tafi uwar gida kishi ne ban sani ba dai, don kishin da na ke ji a yanzu yafi wanda naji a sanda Nazifi ya ƙara aure.
To su wai su Ƙabilar haka suke babu zuciya a ƙirjinsu ne? In ba haka ba miji ne ya haɗamu ta kuma san maƙasudin zaman wai amma sai ta dafa ni tana cewa,"So'ida ki saki jikin ki, indai ta ɓangarena ne insha Allah baza ki samu wata matsala ba, ni matsayin ƴar uwa na ɗauke ki, kuma ƙanwata kuma ƙawata, Sofiyya ta shaida min duk irin kyawun halinki, ta faɗa min ba ki da wata matsala. Na miki alƙawarin zan zauna da ke da zuciya ɗaya kaman wacce muka fito ciki ɗaya, ina fatan kema haka daga gareki, sai dai kuma ɗan sabani na yau da kullum wanda yau da gobe ta gaji haka, kin san ɗan adam ajizi ne ni dai na san ko da zan ɓata miki sai dai bisa kuskure, amma bayan wannan insha Allah za ki ji daɗin zama da ni, ba yabon kai ba ne amma ni na san wacece kuma duk wanda ya zauna tare da ni zai san ni ba mutunce me matsala ko sonta ba".
Murmushin yaƙe na mata ina knodding mata kaina, ba ma zan iya ce mata komai ba, ita da taga zata iya dogon bayanin kanta, ƙarƙari dai ba zan yarda da kalaman yaudarar kai ba, kishiyar zan yarda da ita? Ni zata rainawa wayo, wato na saki jiki da ita sai na gama sakankancewa ta shiga ta fita ta raba ni da miji ta raba ni da gida, to ai ba yau ne farau ba, na zauna da ita a baya na gani, kuma na saki jiki da ita ban ji daɗi ba daga ƙarshe, saboda haka ba zan ƙara maimaita kuskuren da ya gabata ba, ta ciki na ciki na sani, idan tana ganin ta iya taku ne to nima yanzu na yi gogewar da sai dai na ɗorata a layi.
Idon Salim akanta yace,"Zabiya tun ban yi nawa magana ba har kin ida na ki jawabin ko".
Nima dai a raina na ce ƙila ko tana da matsala a kanta ne, idan ba me almatsutsan ka ba kawai ki fara sakin baki da magana wa kishiya, ai kya bari miji yay nasa tukunna.
Kudrat ta rumtse ido tace,"Allah ya baka haƙuri".
Gyaran murya yayi wacce ta dawo da ni daga duniyar ɓacin ran da na tafi, na ɗago na kalle shi muka haɗa ido ma sake ɗauke idanuna, lokaci ɗaya na ke jin zuciya ta tana harbawa sosai.
"Muyi salati ga Annabin mu".
Ya faɗa a kamilan ce, dukka muka yi salatin kafin ya sake cewa,"Alhamdulillah, Cikin hukuncin Allah gashi ya nuna mana wannan rana wacce dukkanmu ba muyi zaton zata zo ba, komai muaƙaddari ne na jalla wa azza. Ku sani ban yi auren nan domin na cutar da wani ɓangare a tsakaninku ba, dukkanku matana ne, kuma soyayya ce tasa na aure ku, kyawun hali da ɗabi'a yasa na zaɓi na shimfiɗa rayuwa ta dindin tare da ku, kowacce da irin matsayin da take da shi a zuciyata, kuma kowacce ina ganinta da girma a idanuna, ina fatan kuma yanda Allah ya haɗamu rayuwa anan duniya, haka ma ya haɗamu a aljanna. Kudrat ke ce babba a cikin gidan nan, akwai karin maganar da ke cewa idan babba yaja girmansa yaro komai ƙanƙantarsa bai isa ya tsinka shi ba, Amma idan babba ya zubar da girmansa yaron duk ƙanƙantarsa zai bi ta kansa ne ya wuce. Kin san shi girma ko na ce mutunci tamkar madara ne, indai ta zube babu yadda za'a yi mata dole sai dai a haƙura da ita. Abinda na ke nuna miki a nan shine da kija girmanki matsayinki na babba a wannan gida, don Allah ki riƙe So'ida tamkar ƴar uwarki, in kinga tayi wani abu ba daidai ba ki sanar da ita ko da zata ji haushinki. Abinda taga kinyi shi zata yi, in taga kin gyara kin ɗauke ta kamar ƴar uwa itama haka zata ɗauke ki. In kuma taga kin ɗauketa akasin haka itama haka zata ɗauke ki. Don Allah ba na son tashin hankali da ƙananun maganganu a cikin gidana, yau ko da ni ne nayi ba daidai ba azo a same ni a faɗa min kar a riƙe ni a zuciya, ko ace dan nayi wata yanzu na canja babu wanda ya wuce kuskure a rayuwarsa. Babban abinda na ke so a gareku shine haɗin kanku, hakan shine kawai zai saka kuji daɗin zaman gidan, nima kuma naji daɗi nayi farin ciki, ba fata nake ba a wayi gari iyalina sun zama shashashai, dukkan ku masu ilimi ne, kuma daga gidan tarbiyya ko wacce take a cikinku, gidan mutane masu dattako. A kori shaiɗan a kuma kori zugar mutane da ta zuciya don Allah, ku toshe kunnenku kar ku bari wata zuga tayi tasiri a zuciyarku musamman ta ɓangarenki Kudrat, ke ake ganin anwa kishiya ke abokai za su yi tururuwan ganin sun zugaki sun wargaza miki rayuwan aurenki, don haka ki kula ki kuma kiyaye, na san banda matsala da ke in har ba ke kika canja ba".
Ina kallonta ta gefen ido, kai take girgizawa cikin gamsuwa da maganarsa, kafin ya maido da batunsa kaina. "So'ida ke ce ƙarama, ke ce baƙuwa a wannan gidan, gidana gidan zaman lafiya ne da kwanciyar hankali da farinciki, ki kula ki kuma kiyaye, kar naji kar na gani, ba zan lamunta da zuwar min abinda zai tarwatsa farin cikin gidana ba. iyalina ba me fitina ba ce, don Allah ki bata girman da take da shi, kar ki kalle ta matsayin kishiya ki kalle ta matsayin ƴar uwar ki kuma yayarki. Bana son jin ko wanne tashin hankali ta ɓangarenki ba zan ɗauka ba ina daɗa maimaita muku gaba ɗaya".