← Book details Ƙayar Ruwa 2&3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 40 OF 113

Sashe 40

Ƙayar Ruwa 2&3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Ehh lallai Yarinyar nan ta cika makirar mace, wato ƙarayayyakin da ta shirya maka kenan, kai kuma saboda shashasha ne sakatare soloɓiyon namiji an shanyeka har ka hau ka zauna akan tsararriyar magana ta matarka. Banza uban wa yay sanadin auran na ku idan ba ni ba? Kai inda hankali da tunani akanka ma har ka zo kana waɗannan maganganun, wanne gata ne ban maka ba a duniyar nan Nazifi? Ina ce auranka na farko ni na maka lefe, amma shi ne yau akan mace zaka rufe ido kaci mutuncina, to bari kaji baka isa ka hana ni zuwa gidanka ba tun da har mahaifiyarmu na ciki, yara kuma da ta zugaka akan ka mayar da su yanda ta zo ta same su haka zata bar su".

Kaɗa kansa yay yana miƙewa tsaye. "Shikenan kar ki fasa zuwar min gida, Allah Iyam duk abin da nayi mata ita tajawa kanta kuma zan je na sami Malam na faɗa masa abin da ta zo tayi min a gida. Yaran kuma idan ma ba ki tafi da su ba zan kira ubayensu su zo su ɗauke su, tun da na samu nawa babu ɗan wanda zan ci gaba da riƙewa".

Yana gama faɗin hakan ya fice. A daren ranar ya kasa haƙuri sai da yaje har can gida ya samu Malam ya karanta masa duk abubuwan da suka faru, Malam ya kira Yaya ta waya yaci mutuncinta iya gwargwado, ya kuma tsawatar mata akan kar ta ƙara taka ƙafarta gidan Nazifi in ba haka shi da kansa zai ɗauki mataki. Wannan faɗa da Malam yay mata shi ya janyo jin cewa ta rabu da Nazifi ita da shi kuma sai ta Allah, ko mutuwa yay ba zata dubi in da iyalansa suke ba.

Bayan wani lokaci da faruwan hakan Iyam na ɗaki tana ta ƙwala kiran Zahra'u, wacca take falon ƙasa tana kallo kuma tana jin kiran amma taƙi amsawa tayi biris kamar bata ji ba.
Tun ranar da akai case ɗin Yaya na zuwa suyi dambe da Zahra'u Iyam ke fama da ciwon ƙafa, farko ba su tsammaci abun babba ba ne ashe ciwon ƙafarta ne ya dawo, dama ƙashin gwiwarta jona mata shi aka yi to shi ne ya daɗa gurɗewa yanzu.

Cikin wata guda da ɗoriya har ta rame saboda tsananin ciwo, kullum ita da Nazifi suna kan hanyar asibiti zuwa gashi da karɓar magunguna. Wanda in ya dawo sai ya barta da Zahra'u a tsammaninsa zata bawa mahaifiyarsa kulawar da ya kamata, nan kuwa bata bi ta kanta in dai ba yana gidan ba taga idonsa, magani ma idan taga dama tana shiga ɗakin zata ɓalla taje tayi floshing ɗin su ba zata bata ba.

Shiyasa Iyam ke shan wuya sosai, bata iya yin komai da kanta sai an taimaka mata, dama sau tari sai dai ta faɗo akan gadon ta rarrafa da jan ɗuwawu tayi abubuwan da zata yi, to garin wannan kifowar da take yi ne ta samu gocewar ƙashin kafaɗa. Tana ta so ta koma can gida Malam yace shi fa bai san zancen dawowarta ba ai bata ma fara gajiya da gidan Nazifi ba tukunna, Ita kuma Zahra'u har da kukanta akan a taimaka a bar mata Iyam zata dinga kula da ita ba zata bari iya ƴaƴanta su kwashe ladan su kaɗai ba, ai itama uwa ce a wurinta, kuma in suka ɗauketa kamar ba su yarda da ita ba ne, dama ga Nazifi ya rantse ya kuma ya rantse duk wacca ta zo masa gida a cikin Yayyunsa da Ƙannensa sai kotu ta raba su, to kuma haka dole ya haƙura duk sati biyu sai suke zuwa dubata sau ɗaya kuma in suka zo za su samu ranar Zahra'u ta gyareta babu ta in da zasu faɗi wani abu na cewa Iyam bata samu kyakykyawar kulawa a gidan Nazifi har a yarda da su.

Yanzun ma banɗaki take ta so ta shiga zata yi kashi ta kasa lallaɓawa ta sakko, shi ne take ta faman kiran Zahra'u amma taƙi zuwa, duk ƙoƙarin da take na riƙe kashin abun ya faskare sai sakinsa tayi a wajen. Ai fa kawai sai ta fashe da kuka tana jin wani irin ciwo a zuciyarta, yanzu har ita matar ɗan da ta haifa zata ke wulaƙantata haka? Kuma ta rasa dalilin da yasa ta kasa ɗaukar wani mataki, duk yunƙurin da tayi na ganin ta nunawa Zahra'u iyakarta sai taji tamkar an danneta, haka ta rasa ta ina tsoron Zahra'u da shakkarta ya samu muhalli a zuciyarta, Surukarta fa! Isan ba ta isa da ita ba ai ta isa da ɗanta ko?
Har dare tana zaune cikin kashi, ga wani azababben ciwon ƙafa da ke damunta, ga uban yunwa don tun shayin da Nazifi ya kawo mata bata ƙara sa komai a cikinta ba, ta rasa yanda zata yi gaba ɗaya.

Bayan dawowar Nazifi É—akin mahaifiyar tasa ya fara shiga domin dubata, sai dai me? shima tun daga falo É—oyin kashi ya bugi hancinsa, sai dai bai kawo cewar uwar tasa ce tayi ba. Daga kwance ya sameta ya kunna fitila yana kallonta kwance kamar mara rai, ya tafi da sauri gareta yana kiran sunanta. Sai da yaje bakin inda take ya ankare da dama dama É—in da tayi cikin kashi. Ya furta,"Subhanallah Iyam ya aka yi haka?".

Kamar zata yi kuka cikin murya mai ban tausayi tace,"Wallahi Nazifi matsuwa nayi ne".

"To amma me yasa ba ki ƙwalawa Zahra'u kira ba, ina wayarki saboda irin haka fa na ce kike barinta kusa da ke ko da zaki kirata bata nan ƙasa sai ki kira wayarta, kuma ita ya akai yau ban sameta anan ɗin ba?".

Iyam tayi wani murmushi me ciwo da cewar,"Wayar ce Nazifi ban an in da na wurgata ba, yau ko ƙararta ma banji ba".

Da matuƙar tausayin mahaifiyar tasa yace,"Bari na kirata ta wanke miki, sannu in sha Allahu kin kusa samun lafiya, likita yaje kawai a fita da ke ƙasar Germany".

Ya faɗa yana ƙoƙarin fita ta tsayar da shi. "Ƙyale Zahra'u Nazifi, kai dai Allah maka albarka da ɗawainiyar da kake yi akaina, yanzu dai kai taimaka min ka raka ni banɗakin sai na gyara jikina".

Kawai a ɗan wannan furucin nata sai ya fahimci da akwai wani abu, don kamar ma muryarta da alamun tsoro a ciki, anya kuwa Zahra'u na kula da ita? Anya tana cika alƙawarin da ta ɗaukar masa kuwa?

Baki ya buɗe zai yi magana ta girgiza masa da cewa,"Nazifi bana so na shiga tsakaninka da matarka ka rabu da sha'aninta kawai, amma dai dole ka haƙura Faty ko Lubabatu wani ya dawo nan wurina da zama don gaskiya ni ɗaya na san a halin da na ke ciki. Matar babu abin da take min a bayan idonka, duk wani rawar jiki daka ga tana yi akaina wajen nuna min so da kulawa to a gaban idonka ne, makira ce ta ƙarshen ƙarshe, Zahra'u idan kasa ƙafa ka fice ko waiwayowa ɗakin nan bata yi, Nazifi matarka halin da nake ciki ma bata duba ta bani abinci ba haka nake yini na kwana da yunwata, kuma banga laifinta ba wannan ɗawainiyar ba kowa zai iya ba sai wanda ka haifa ɗin".

Ran Nazifi ya ɓaci zuciyarsa na tafarfasa ya fita ya bar ɗakin. Ƙwala kiran Zahra'u kawai yake cikin amon tsanin ɓacin rai tun daga ƙasa har ya hau sama. Garam ya banka ƙofar ɗakinta wadda ta firgita ta juyo tana dubansa da cewa,"Innalillahi Honey lafiya?".

"Ashe ba ki da mutunci, ke ɗin dama ba ƴar arziƙi ba ce? Ashe wulaƙanta min mahaifiya kike yi, mahaifiyata Zahra'u za ki ke hanawa abinci? Sannan bata da lafiya ki kasa sauka wurinta kike kulawa da ita kina taimaka mata? Dama ashe ganin idona yasa kike mata abubuwan da ba zan zargi kina cutarta ba, kin san a halin da na zo na sameta kuwa yanzu? Uzurin bayan gida ne fa ya kamata kuma tace ta kira ki kina jinta kika ƙi zuwa gareta, Zahra'u mahaifiyar tawa kika ma wannan wulaƙancin?".

Juya idanu tayi ta É—auke kai, lokaci guda ta sha mur kafin ta jiyo cikin É—aga murya ta katse shi da faÉ—an da yake faman mata.
"Kaga Nazifi Dakata! To ni ɗin dama bautar mahaifiyarka na zo yi ne, gaskiya ni ba zan iya wahalar nan ba, haba komai sai dai ayi mata hatta wanka wannan sai an taimaka mata to ni ba zan iya ba, ka ɗaukar mata masu aiki ko ka maida ita gidan mahaifinka ni kam ba zan kashe kaina da bauta ba, kuma wallahi in har ka ɗauko wata cikin ƙannenka da sunan su dawo nan da zama su kula da ita wallahi sai dai in ka sallame ni".

Ta faɗi hakan ta raɓa shi ta fita a ɗakin, barin Nazifi tayi da sakakken baki wanda ya bi bayanta da kallo da maɗaukakin mamaki, gaba ɗaya sai yaji abun wani gingirin gin domin tun da yake zaman aure matarsa bata taɓa ɗaga masa murya ba, haka bai taɓa umartata da ta yiwa mahaifiyarsa abu taƙi yi ba. Amma yau yaga zahirin wacece Zahra'u a cikin kalamanta da ƙwayar idonsa da sonta ya rufe ganin duk wani kuskurenta.

Ficewa yay ya sauka ƙasa da sauri ya koma ɗakin Iyam jikinsa sai rawa yake yi, Yana son mahaifiyarsa so yake ya rabu da ita lafiya. Yana shiga da kansa ya kamata ya shiga da ita toilet yay mata duk abin da ya dace sannan ya fito da ita. Abincinsa ya ɗauko ya zauna gabanta yana bata tana ci, haka tana ci tana zubar hawaye shi kuma jikinsa duk yay bala'in sanyi ya mutu, a zahiri ma ba zai ce ga tunanin abin da yake cikin ransa ba amma tabbas yana jin wani ɗaci a ƙasan ransa.
__________________________________
*Gwarazan Labarai na ƙarshen shekarar 2023 masu ma'ana.*

*KWANTAN ƁAUNA*
Nana Haleema

*ƘAYAR RUWA*
Halimahz

*LOKACI NE*
Oum Mumtaz

*FARGAR JAJI*
Aisha Yabo

*WASA DA RAI*
Fadila Yakubu

Ɗaya ₦500
Biyu ₦800
Uku ₦900
Huɗu ₦1000
Biyar ₦1200

*Biyan Kuɗi Ta*👇🏻
6314170140
Fidelity Bank
Sa'adiyya Zakariyya Haruna

*Shaidar biya ta👇🏻*
09061794195

*Godiya tare da adu'an fatan alkhairi ga wanda suka sami damar mallakar littafanmu, son So fisabilillah🥰*
Chapter 40 · 0% Book details