Sashe 30
Ƙayar Ruwa 2&3 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Sai da naga dai an gama shirya ni da gaske tafiya zamu yi sai kuka kamar daga cikin gidanmu za'a ɗauke ni, Nasihan da Hajjo ke ƙara min ita ta sake karyar min da zuciya, hatta Maman Khairi da Maman Yasmin sai da suka yi hawaye, na ce a bani waya na kira Abbaa, kaman kuwa yana jiran kiran nawa shima don bugu ɗaya ya ɗaga, na ce masa gani yanzu za'a wuce da ni can gidana, nan yay ta min adu'a yana ƙara jaddada min nasiharsa gare ni, muka yi sallama da shi sabon kuka na ƙara zuwar mini.
Sai da su Gwaggo Abula suka fara fita kafin Umman su Safiyya ta fito da ni kaina na ƙasa. Falon Sir aka kai ni, a can na tarar da Salim ɗin shi da Kudrat, dukkanmu Sir ya haɗe yay mana faɗa da nasiha, nasiha me tsuma zuciya. Daga nan aka kai ni can wajen Maa wannan karon kuma da gani sai shi ne, Itama tayi mana nata adu'oin irin na kowacce mahaifiya ta ƙwarai, musamman shi da take faɗa masa ya zama me adalci tsakaninmu, kar ya taɓa bari wani abu da zai haddasa ƙabilanci a tsakaninmu ya afku. Har Maa aka rako mu compound tana riƙe da hannuna ita ta saka ni cikin mota, su Hajjo na ta yi musu godiya da irin karramawar da aka yi mana.
A motan da na ke Mama A'i ne da Hajjo sai Gwaggo Abula da Safiyya, ɗaya kuma su Maman Yasmin ne a ciki, ɗayar kuma Salim da iyalansa. To a motar ma tun ina kuka har na gaji na daina, na biyewa hirar da ake, yo tafiyar ba ta minti goma zuwa talatin ba ce, awa uku ne babu kaɗan, zuwa sha ɗaya na dare dai mun isa, Kamar dole Salim da rigima dai da yay haƙurin.
Naji ƙaran shigowar message a wayana, ina dubawa na ga lambar Lubabatu ne, mamaki ya mamaye ni ita kuma message da wannan daren haka? Me zan mata? Ni fa bana ƙaunar wani iri na Nazifi Bala Mai Kalwa ya ƙara gifatawa a rayuwata, Tun ban buɗe ba kuwa nayi regretting bata lambar tawa, sai dai ko da na duba saƙon magana yake akan.
_"Don Allah ki yafe min Sa'ida, hakkinki ba zai bar ni ba, ban da idon da zan zo gaban ki na fuskanceki na nemi yafiyarki, don Allah ki ce kin yafe min, na gode sai naji daga gareki, ba ni da waya ne a hannu"._
Tsaki nayi na goge message ɗin, can kuma sai zuciyana tace na mayar masa da amsa tunda shi bai da hankali bai san menene aure ba, kar ya zo ya ƙara turo min saƙo mijina ya gani ya rikita min zama ya tashi hankalin farin cikina.
_"Idan ba so kake ka ƙare rayuwanka a gidan yari ba to kar ka ƙara turo min saƙo, domin kuwa mijina ba zai ƙyale ka ba. Yafiyata ka jira mu haɗu a kotun Allah gaban alƙalin da ba ya zalunci"._
Mun isa Delta State lafiya, na shiga gidana da ƙafar dama, wata faɗuwar gaba da ban ji ta ba tun ranar ɗaurin aure sai yanzu ta ziyar ce ni, jiki a sanyaye fuskana na rufe haka na tako cikin falona, Umman Batula na faɗin shiga da Bismillah, suna biyo min ayoyin da zan karanta, kai yanda ake tayi da ni fa kamar auren budurwa b abazawara ba.
Suna kai ni cikin É—akina duk suka watse aka bar ni daga ni sai Safiyya. Ganin har lokacin ina hawaye ta daki kafaÉ—ata tace,"Beb wannan hawayen ya isa sai kace wacce ta auri wanda bata so? Bafa auren farko bane na biyu ne balle kice min kina tunanin first night, haba mun fa girma Beb".
Ta faɗa tana ƙyalƙyalewa da dariya ta shakiyanci.
Sai kuma ta tsuke fuska taja tsaki tace,"Allah ya isa da mai kalwa ya same ki a banza, ina ma É—an uwana ne ya aureki tun farkon farko ba mai kalwa ba shege matsiyaci".
Sai ta sake sakin fuska tace,"To ya za'ayi da ƙaddara ce Allah ya riga ya rubuta. Ke ki kwantar da hankalinki ki kwashi soyayya, wallahi Salim ba shi da matsala na san kin sani, ki cire batun fargaban zai sameki wani ya riga shi shiga hanyar, yo dama ai a yanda ya ganki ya ce yaji ya gani har sai da ya amso ki hankalinsa ya kwanta. Anty Kudrat kuwa zan ta nanata miki sauƙin kanta ya wuce tunaninki, matar nan dabance, don ni ko yau aka ce an samu matsala to wallahi Beb ke zan fara ɗorawa ayar tambaya".
Ni dai kallonta kawai na ke yi, cikin raina tunani kawai na ke yi akan sabuwar rayuwar auren da zan fara a karo na biyu, shin ya zama zai gudana tsakanina da Salim? A yanzu ni dai ba za'a kira ni mara ilimi da rashin wayewa ba, haka ba za'a kalli kayan da iyayena suka zube min a cikin gidan ba a goranta min da ɗiyar talakawa, fatana na samu ɗorewar farin ciki, sai dai a ko da yaushe ina hangen wani nakasu da na ke tare da shi, nakasun rashin haihuwa wanda shi ne maƙasudin lalacewar zaman aurena, ban sani ba, ban kuma san ta ya wa'annan ahalin za su karɓi lamarin ba, shin za su nuna min banbanci ne ɓaroro da matar gidan da ta riga ta ƙyanƙyashen ƙwai ba ɗaya ba ba biyu ba? Ko kuwa za su zama masu goranta min ne da hantarata kamar waɗancan?, duk ba wannan ba shi wanda ya ɗakko ni ya aje ya rayuwar tamu zata tafi da shi idan muka haura wasu shekaru ban samar masa da haihuwa ba, ko kuma zai mayar da ni bora ne soyayyarsa, mutuntawarsa da darajartawarsa na ga uwar ƴaƴansa? Ban san ya ubangiji ya tsara rayuwata ba, wataƙila ina ɗaya ne daga cikin bayinsa da ya jinkirtawa haihuwa ne, ko kuma ina daga cikin waɗanda bai rubuta suna da rabon samun haihuwar ba har su koma gare shi.
Safiyya ta kalla agogo sai ta miƙe ta ɗauki mayafinta da jakarta tana ce min,"Sai ki yi ta aikin tunani da hawaye kin ji, ke da ba ki jin shawara, ni dai zan wuce sai da safe, wajen Anty Kudrat zan tafi, babu ke ba zan iya kwana cikin su Hajjo ba".
Na gyaɗa mata kai kawai, ai dai tare zamu kwana da ita a cikin gidan na matuƙar jin daɗin hakan. Har ta nufa hanyan fita sai ta dawo ta sake zama kusa da ni tace,"In yazo yaga kina wannan kukan ba zai ji daɗi ba fa, zuciyansa zai so su duk ki saka shi a damuwa, dan Allah ki daina ki saki jikinki komai zai tafi dai dai da izinin Allah".
Sai kuma ta dungure min kai tana faÉ—in,"Munafuka me kukan gulma, nan da anjima sai dai in jiyo na tashi, to earpiece zan saka ba zan kawo É—auki ba".
[2/2, 07:47] Hlm: *B2ƘR15FT5*
Cikin dare ciwo ya tasar min, tun ina dauriya ni ɗaya abu har yaci tura, gurnani na ke ina nishi ina wani irin miƙa, da kwance na ke kan benci haka har na faɗo ƙasa ban sani ba, malelekuwa kawai nake yi har ta kai ga na fara mawahalcin kakari kamar zan yi amai.
Ɗan sanda da ke tsare da ni ya leƙo yana buga min tsawa tare da faɗin na ishe su na kiyaye na natsu.
Ina kuka cikin ƙarfin hali na ce masa"Ka taimaka min da ruwa".
Sai ya ƙara doka min tsawa yana cewa,"Ba za'a bayar ba".
Kaina na jinginar da bango ina ta sauke numfashi wanda ma sai na matse hancina na buɗe baki kafin nan na samu na shaƙi iska. Juya kaina nayi ga bakin ƙofar, idanuna a rufe ina ta so na buɗe su amma sunƙi buɗuwa, murya na fita da ƙyar na ce,"Ka taimaka min don girman Allah, ina da ruwa a cikin nan ka yiwa darajan Allah ka hasko min fitila na duba".
Ni ban sani ba ashe ya hasko É—in, sai ji nayi yana masifa cikin É—agawar murya yana cewa,"Ba za ki É—auka ba ne na kashe fitila ta".
A rikice na ce,"Yi haƙuri ban san ka kunna ba, idona bana gani don Allahu ku taimaka min".
Na faÉ—a cikin ruÉ—ewa ina lalube da hannu.
Hasko fuskarta yay, ya tsaya na ƴan sakanni yana kallonta kafin yasa maƙulli ya buɗe ƙofar ya shigo. Naji shigowar tasa amma ban san ta ina yake ba, sai jinsa nayi yana cewa,"Me ya sami idon na ki?".
Na dinƙa ɗaga murfin idona yaƙi buɗuwa sam, tsoro da tashin hankalin da na ke ciki suka ninku, take na fara tari babu ƙaƙƙautawa, sai ji nayi ina tofar da wani abu mara daɗin ɗanɗano a harshe. Naji ɗan sandan ya furta,"Subhanallah, ba ki da lafiya dama ba kiyi bayani ba tun ɗazu".
Ba zan iya magana ba a halin da nake kam, ni dai taimako kawai na ke buƙata a lokacin, a bani maganin da zan sha zuciyata ta bar zafin da take yi, haka kuma a buɗe min idanuwana da suka kasa buɗuwa, sannan a bani in sha ruwa, fitarsa naji, take na shiga ambaton Allah ina kuka ina roƙonsa da ya buɗa min idanuwana, kafin na koma kiran sunan Abbaana.
Can sama sama naji mutane akaina ana magana amma ban san me suke faÉ—a ba, kafin naji kuma an kinkime ni can nesa nesa naji ana batun asibiti.
*Ƙarfe Bakwai na Safe.*
Abbaa ya fito daga ɗakinsa yana kiran sunan Ummani, ta fito daga kitchen da sauri ta iso gabansa da leda baƙa a hannu. Miƙa masa tayi cikin sanyin yanayi tace,"Don Allah ko na sako mayafina na bika, ina so naje naga ya ta kwana".
Abbaa yaja numfashi ya sauke, hannu yasa a aljihu ya ɗauko kuɗi. Tsohuwar ɗari biyu ce ya nuna mata yana cewa,"Ki yi haƙuri naje ni ɗaya, kinga ko ni ɗaya wannan ba zata kai ni ba balle har mu biyu, dole nima sai dai nayi rabi tafiyar ƙafa rabi ta mota".