← Book details Ƙayar Ruwa 2&3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 26 OF 113

Sashe 26

Ƙayar Ruwa 2&3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ni ban ma ko gaisheta ba na amsa da to kawai na wuce sama. idona har ba ya buɗewa da kyau saboda baccin da ke cikinsa, amma haka dole na yaƙe shi na fito na kama aikin. Ko kusa ban ji ina ɓacin rai dan zan yi aikin ba, hasalima annashuwa na ke ji a tare da ni, banda ma yanayi na gajiya da ramakon bacci dama ina da niyyar in gari ya waye na tambaye shi me zan dafa da za'a kai musu.
Shiga ɗakinsa ɗari fita ɗari sai na same shi yana waya da abokai da mutanen arziƙi yana gaya musu an masa haihuwa. Tun asubar nan bai koma bacci ba kiraye kiraye kawai yake yi, wasu kuma yana tura musu saƙo ta message. Ya kira Malam ma yace masa za'a kawo Sa a yanka ayi sadaƙa sannan kuma ayi sauƙar ƙur'ani wa yaran.

Naci wahala sosai wajen dafa naman kan saboda itacen ɗanye ne, da dukkan alama da gayya Iyam tasa aka kawo shi haka, ga Naman kan gari guda kan shanu manya huɗu. Iyam sai azalzata take yi akan nayi sauri kar rana tayi, shima ɗin kuma da nasa ƙwazzafar yana faɗin to na dama kunun in dafa shayi a fara kai musu, duk sai na bi na rikice aikin ma yaƙi yin sauri, ga ba damar ƴar aikin Zahra'u ta taya ni saboda tana ta gyaran wajensu, haka dole na rabu da naman na dawo kitchen na ɗora shayin sannan na dama kunun.

Atika ta shigo kitchen ɗin tana ce min,"Abba yace kije da sauri". Hmm yarinyar nan idan ta girma ban san ya zamu kwashe da ita ba, ko gaishe ni bata yi, magana ma idan tana min kamar wacca ta isa da ni ko kuma sa'arta. Sharewa kawai na ke saboda dai a zauna lafiya amma ko ranar nan ita da ƴar uwaratata sai da suka yi faɗa, ita Rumanan na ce mata kar ta ƙara yiwa Antynta rashin kunya in ba haka ba zata faɗa a islamiya a zaneta, ita kuma tace ai dai ta faɗawa Anty Amarya a cireta daga islamiyar a sauya mata wata.

Biredin da nake soyawa a cikin ƙwai na tsame na kashe gas na fita. Samunsa nayi ya shirya sai baza ƙamshi yake kamar sabon ango, don kayan ma da ya saka sababbi ne, bakinsa yaƙi rufuwa fuskarsa sai fitar da murmushi take yi, kallo ɗaya ba sai ka ƙara na biyu zaka san a tsananin farin ciki yake. waya ce kare a kunnensa yana cewa,"Ehh dama na ce ƙila baka tashi daga bacci ba ne, sai na maka text ta whatsapp".

"Ehh wallahi Ƴaƴa biyu ne duka mata, sai ayi musu adu'a don Allah". "A'a Amaryar ce ba uwar gidan ba. Ameen na gode sosai a gaida iyalin, sai anjima".

Ya aje wayar yana dubana da cewa,"Wai har yanzu ba ki gama ba? Kinga fa har na shirya zan tafi can, ƙarfe nawa yanzu tara fa, ace kuma har yanzu me shayarwa bata ci komai ba, kin san fa ƴaƴan za su sha nono duk su zuƙeta itama ta buƙaci abinci".

Numfashi na sauke na ce,"Kafin ka fito na gama, amma Nama ba zai samu yanzu ba ka turo a É—auka anjima. Kuma sai ka É—auko kula a wajenta da zan zuba biredin a ciki".

Na faɗa ina juyawa na fita. Can sai ga shi ya shigo kitchen ɗin, barinsa nayi da zuba soyayyan bireɗin ni kuma na ɗauko kwando ina saka kwanukan kayan abincin. Ya ɗauki wasu yay gaba da su nima ina biye da shi da ɗaya kwandon. Shi a shirin nasa ma tare zamu tafi, sai Iyam tace ina fa zai yiwu tafiya da ni, idan naje can me zanwa me jegon me zanwa yaran? Kawai na zauna na dafa abincin rana akai musu, kuma wataƙila ayi baƙi ƴan barka basa zo gida babu kowa ba, roƙonta na tari mutane da girmamawa kar su zo na nuna musu mugun halina dan dangin Zahra'u mutane ne masu mutunci, in kula kar jakin kishina da baƙin cin haihuwa yasa na ɓatawa miji girman da yake da shi a wajensu.

Babu yanda Rumana bata yi ba akan zata bisu Iyam ta hana, wai ai tunda ta iya munafurci yanzu to ta jira ni mu tafi tare, ita Atika ai uwar wajenta ce shiyasa zasu tafi da ita, Yarinyar ta ban tausayi sosai, tana tashi ta tambayeni akan ta shirya nace to ai makaranta tace Atika ma bata je ba Abbansu yace zasu je gano jarirai, nace to itama ta shirya ɗin, na dai fahimci duk wani da zai raɓe ni ya soni Iyam bata ƙaunarsa ko da jininta ne.
Sai kusan sha É—aya na sauke naman kan, na zuba a kulolin tsakiya har biyu irin na taron biki, sannan na dafa shankafa da miya da coslow itama kwano É—aya yace a dafa, ya turo Adamu ya É—auka kai musu, ni kuma yace na shirya da yamma na je.

Na gaji sosai ina so na kwantar da haƙarƙarina, na ce masa naje gobe kawai sai ya kama faɗan shi ba ya son musu, kuma kar na ɓata masa rai, ko na manta ƴaƴansa zan je gani da na ke faɗin ba zanje ba. Nace masa ni fa idan yana tunanin ina jin haushin haihuwar yaran nan yama daina, domin kuwa ni zuciyata tas take babu tsatsa, idan kuma ba zai cire zargin hakan a ransa ba to yaci gaba da ɗaukar alhakina.
Da Yamma na shirya muka tafi Asibitin ni da Rumana, na tarar an ƙara cika wanda ke shaida dai ita ɗin yar gata ce, don har wata likita ma naji tana cewa amma wacca ta haihu nan ta gaban goshi ce. suma kusan ƴan uwan Nazifi duk suna nan, asibitin dai sun mayar da shi kamar wajen taro su kawai ake gani. A waje na tsaya muka gaggaisa da ƙannnen nasa da Yayyensa, kana na shiga ɗakin.

Sallamar da nayi babu wanda ya amsa sai nayi musu uzuri da hayaniyar da ake tayi hakan yasa basu jini ba, sai bayan na shiga ne na ajiye kayan abincin tukunna Innarta ta lura da ni tace,"A'a Sa'ida sannu da zuwa, tun É—azu kuwa na ke ta zuba idon ganinki".

Na amsa da yauwa ina tambayarta ya jarirai suka kwana. Tayi min nuni da wajen zama tana ce min ƴaƴan nawa an fita da su Kakansu ya zo, nace mata tom ga dai abincin dare can na zo da shi. Tayi min sannu tare da godiya sosai tana ta faɗin an barni da ɗawainiya, sannan ta juya garesu tana gabatar musu da ni, na kula kusan duk ɗinsu ba waɗanda muka bari jiya ba ne. Haka suka bini da wani irin kallo na raini da ƙasƙanci, ai suna ganin na saka hijabi har ƙasa ga niƙab da safa ga ni duk a koje, haka kuma suna jinjina ni ce kishiyar Zahra'u.
Babu me niyyar min magana, ni kuma girmansu yasa na gaishe su sai dai babu wanda ya amsa min sai ɗauke kai da suka yi, ina ji suna ƙusƙus Allah masanin me suke cewa a zuciyata ni kuma ina nanata "Wallahulmusta'anu ala ma tasifun, hasbunallahu wani'imal wakil, la'ila ha'illa anta subhanaka inni kunta minazzalumin".

Me jegon ma haka na daure nayi mata magana to ni ban sani ba ta amsa ko bata amsa ba, ci kanki dai bata ce min ba kamar ma bata san ina wurin ba. Rumana ta dame ni da cewa Anty ina jariran na doka mata tsawa akan ta ƙyale ni ai tana ji aka ce an fita da su, Atika ta zo wajen tana ce mata jariran Antynta masu kyau, ita kuma ance Antynta ba zata haihu ba. Rumanan ta ɗago ta kalle ni, tabbas yarinyar yanzu tana sona bilhaƙƙi da gaskiya, sai in kuma shaiɗan ya kuma buga mata ganga, don yanzu ko wani ya ɓatan rai to sai tayi kuka musamman ma idan taga Nazifi yana min faɗa, sai tace ita bata so Abbansu na yi min faɗa.

A sanyaye tace da ƴar uwartata,"Nima Antyna zata haihu ai in sha Allahu". Tana faɗar hakan na girgiza kaina ina murmushi me ciwo, na ce da ita ta tashi su fita daga waje sai ta girgiza min kai, haka na tilastata ta fice tana matsar ƙwalla, ni kuma bana son ƙara jin bakin Atikar ne saboda zuciya zata iya ɗibana na daki bakin yarinyar.

Kiran Ummani ya shigo wayata, bayan mun gaisa na ke ƙara tambayarta jikin Abbaa tace wallahi yaji sauƙi sosai in kwantar da hankalina, gobe ma ake sa ran basu sallama. Ban dai yarda ba sai da naji muryan Abbaan tukunna, saboda na kira da safe ce min tayi bacci yake yi ni kuma sai nake tunanin ko jikin nasa ne ya dawo, tun da ko a jiyan kana ganinsa ka san ƙarfin hali yake yi, don niyyata ma da zan fito can zan wuce Yashaik yace kar na je.
Ummani tace na bawa Zahrau wayar na ce ko ta bari kawai idan ta koma gida sa zo mata barka, tace a'a na bata ɗin dai kafin ta zo. Na miƙe na isa gaban gadon na miƙa mata wayar, ta bi hannuna da kallo na ce mata,"Babarmu ce zata yi magana da ke".

Karɓa tayi babu sakin fuska, kuma da mamakina sai naji tana magana da Ummani cikin ladabi da girmamawa, har tana tambayar jikin Abbaa, sai naji daɗi da hakan don nayi tsammanin zata wulaƙanta min uwa ne yanzu mu kwashi ƴan kallo, ban san me Ummanin tace mata ba naga tayi murmushi tace,"To Mama ai sai su zo har gida ma su gaishe ki". Sannan kuma naji tana jero in sha Allahu Mama, kafin ta koma jera to to, da haka na san aduo'i ne Ummani ke bata don na san wacece mahaifiyata, bayan gama wayar tasu har godiya nayi mata ko ba komai ta darajarta min Uwa.
Chapter 26 · 0% Book details