← Book details Ƙayar Ruwa 2&3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 92 OF 113

Sashe 92

Ƙayar Ruwa 2&3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Da kuka sosai aka fito da ni daga cikin gida, kowa adu'a yake min Allah sa na shiga kenan sai mutuwa zata raba, Allah yasa sa'a ce ta kiraye ni, Allah ya kaɗe tsautsayin dare da rana da yini, tarin adu'oin da suke ta fitowa daga bakin ƴan uwa da abokan arziƙi kenan, sai lokacin na buɗe fuskata na yiwa Maimuna da Hassana sallama, da ma su ƴan asibitinmu tun ɗazu suka wuce.
Muna tsaye ƙofar gidan kamar ba zan tafi ba Abbaa ya fito Ummani na biye a bayansa, shi ya karɓi hannuna daga hannun Gwaggo Abula ya kamani ya kai ni bakin tsadaddiyar motar da za'a ɗauke ni, ina ta faman sharan ƙwalla ya shigar da ni ciki, ya kama hannuna muka yi musabaha yana daɗa saka min albarka da tarin adu'a, Ummani ma ta miƙo nata muka yi musabaha, zuciyata naji ta tsinke ganin mahaifiyata na goge hawaye, shima Abbaan kansa dauriya kawai yake amma naji a muryarsa, ya rufe ƙofa yana cewa da Abbayo su kori yara daga bakin motar ana daɗa ɓata lokaci, haka muka bar ƙofar gidanmu, Allah sarki Rayuwa kenan, aure babu inda ba ya kai mutum, ni yanzu ina na taɓa hangowa kaina ma garin da za'a kai ni.

Ina ta kuka Maman Khairi da Maman Yasmin na ta lallashina, Safiyya na gaba tana ce musu su ƙyale ni kukan munafurci ne. Zuwanmu airpot Salim ya kira wayan Safiyya ta bani, yana ta ban haƙuri na rashin samun space muyi waya, nace masa babu komai, yace na kula masa da kaina kuma idan akwai wani abu na kira shi, da haka muka yi sallama ina ce masa zamu shiga jirgi, yay mana adu'an a sauka lafiya.

A cikin jirgin na sake muna ta hira, muna ta shan dariyar Maman Khairi da ke buga mana ƙauyanci, awanmu uku da minti talatin da uku muka sauka a filin jirgi na Anambra International Cargo Airport, lokacin da muka sauka muka tarar da har anzo ɗaukarmu da wasu tsala tsalan motoci na gani na faɗa, dama ina sakkowa a jirgin na yiwa Salim text na shaida masa mun sauka, muka shiga mota ɗaya, ɗaya kuma ƙannensa ne mata da maza a ciki waɗanda suka zo tararmu, gabanmu da bayanmu duk motar sojoji ce, yau ni Sa'ida da ban iya turanci ba ya zan yi, to duk daga yare sai english a bakinsu, Maman Khairi da Maman Yasmin aka yi tsilli tsilli da idanu sai aikin yaƙe baki da suke ta faman yi, har dariya na so yi amma haka na cije, Sisters ɗinsa kamar za su cinye ni saboda murna, da ƴar ƙaramar ƴarsa Rofi'at yarinyar kamar ƴar turawa, bama ta kama da shi gaba ɗaya sai dogon hancinsa da ta ɗakko, naji kishi ya kama ni kar da da gaske Abbayo yake Kudrat ta fini kyau, to idan kuwa haka ne me Salim ya gani a tare da ni?. wata cikin Sisters ɗinsa me suna Apunanwu har sai da ta lotsa yatsanta cikin dimple ɗina tana faɗin zan sammata.

*B3ƘR12FT5*
Mun yi tafiya me nisa kafin mu kai ga ƙauyen Aguata, kaf ɗinmu ba wanda bai gaji ba duk da a mota muke, Safiyya kuwa da ke ta saba ce mana take babu nisa ga shi ma har an zo. Masha Allah a arean gidajen da suke duk gidan su Salim yafi girma, kyau da kuma tsari. Kusan gari guda sai da muka fito a mota Safiyya ke ce mana ai family house ne, shima Salim ɗin banda yanayin aikinsa da anan zai tare, don ƴaƴa da jikoki kaf anan suke zama idan aka yi aure sai in mata, to da ke ma a matan Ummansu ce kawai tayi aure a wajen ƙabilar su amma sauran duk auren ƙabila ne.

Ba wai don zuwanmu ba haka gidan yake baibaye da sojojin da ke tsaron gidan a ko da yaushe, kun san an ce masu abu da abunsu, ga uba ga ɗa dukka masu babban rank ai dole. Tun fakawar motarmu a haraban gidan wasu suka zazzo taranmu, Safiyya tuni ta falle ina gani ta kwasa a guje tayi jikin wata mata, ni kuwa ina tsaye kaina a ƙasa, ƴan uwa duk sun yo kaina ana ga bride ɗin Onochie, abinda na ke iya fahimta kenan daga abinda suke cewa don duk da yare suke magana.

Wata dattijuwa ce ta kama hannuna, muna gaba su Maman Khairi na bayanmu, sai kuma wasu daban da ke ƴan waƙoƙinsu daga gefenmu suna rawa irin tasu. A wani tafkeken falo muka yada zango, ban da kar nayi ƙarya sai na ce falon yay girman gidan gaba ɗaya, ashe nan ne main falo na kowa da kowa, falon ya ƙawatu da kujeru na alfarma ga adon mafitai irin na su da aka ƙara ƙawata haɗuwan falon da shi, arziƙi dai yana inda yake, amma kai da ka shigo gidan ka san an aje doller.

A ƙasa na so na zauna sai dattijuwan da ta ruƙo ni tace a'a bisa kujera zan zauna, ai fa lokaci guda sai na zama wata abar kallo ko kuma in ce na zama ƴar gata, shigowa kawai ake ana ganina ana yaba irin kyan da nayi, sai ce suke shi dai Onochie ya iya zaɓo mata masu kyau. Ni fa in har za'a dinƙa faɗin kyan Kudrat to lallai sai zuciyata ta motsa da wani bala'in kishi da haushi, har ji na ke kaman dan cin mutunci ne ma Salim ya aure ni, in ba haka ba yana da matarsa me kyan da kowa ke faɗa mene na zuwa ya auro ni, wannan ma ai wulaƙanci ne, ji nayi ma na daina missing ɗinsa na sa sai haushinsa.

Salima ƙanwarsa wadda suke cewa Chiagozie, dama ita mun taɓa magana ta waya da ita ranar ta kira shi tana roƙonsa ya sauya mata new phone kuma pocket money ɗinta na makaranta sun ƙare, ta ƙaraso riƙe da dukka yaransa ukun, Ƴar ƙaramar ta ɗazu da suka je ɗakko mu ita ta fallo da gudunta ta haye saman cinyata tana cewa Yayyunta,"Here is our new Mommy".

Ni dai murmushi kawai na ke yi mai cike da burgewa, lokaci ɗaya naji yaran sun shiga raina, masha Allah kyawawa da su dukka kai baka ce haihuwar ƙasata najeriya ba, dama ya taɓa faɗa min Foridat miskila ce ko a yanzu ma ita ta noƙe daga baya, su kuwa biyun duk sun maƙale a jikina, Isioma ma kuwa dama yace akwai surutu faɗa suke da shi ma akan yawan maganarta, na ke ce masa ai nafi son yara irin haka muma muna da Walida, yace ba zan gane surutunta ba sai na shigo gidan, ile kuwa tun yanzu ga shi na gani, ta sake da ni tana ta bani labari Paapa yay musu sabbin kaya na biki, shima yayi sabo iri ɗaya shi da Maama, kuma Maama tace musu idan sun ganni suyi hugging ena suyi min peck a kumatu, ina son su da yawa, kuma sai ta faɗawa Maama Big Sis ta ganni bata gaishe ni ba.
Dukka haka muka sa dariya, ta maƙale wuyana tana ce min,"New Mommy i love you so much, you are so beautifull".

Na kama kumatunta ina ce mata nima ina sonta kuma ai ta fini kyau ma, zata sammin nata kyan, tace ai Paapa ne itama ya sammata. Haka ne kuma duk cikin yaran ita tayo kamansa, biyun dai sai kama ta jini ina ga su kamannin mahaifiyarsu suka yi, Salima ce ta kwashe su tana su bar ni na huta, Rofi'at har da kukanta sai an barta a wurina, ita kuma Isioma na cewa sai ta faɗawa Paapa an ɗauketa a wurin New Mommy, zai sa bindigansa yay shooting ɗin mutum, ina kallo Salima ta talle mata ƙeya ni dai nayi dariya, ina ƙara jin sha'awan yaran.

Nan aka barmu kowa ya watse, ina ta baza ido ma na ga shigowan Safiyya ba ita ba dalilinta, Maman Yasmin ta zunguro ni na dubeta, yanda take da fuska abin ya bani dariya, a hankali tace,"Ke mun kawo kan mu, yanzu mu ta ina zamu fara musu bayani baki babu turanci balle yaren da suka fi ji, wannan shi ake kira da kasassaɓa ina zaman zamana na ɗebo ki na kawo ki zanji kunya".

Maman Khairi tace,"Kin san ni da tsarguwa ni ta É—azu ma da taje ta rungumeta sai naji kamar zaginmu tayi, ko yaren ne me yanayin zagi oho".

Dariya nayi da ce musu,"To ai Safiyya tana nan, kuma Umma ma na nan". Suka ce,"Ohh tou da sauƙi". Maman Khairi na faman kalle kalle take cewa,"Ohh wuri kamar ba'a ƙasar nan ba, mu dai yi shiru kar wannan abar CCTV ta naɗe ƙauyenci mu ta nuna". Nima sai na ɗaga ido ina ƙarewa falon kallo, ta bakin nata ba za'a rasa CCTV ba kam, musamman a gida irin wannan, Maman Khairi da mugunta ta bushe da dariya tana cewa ita wallahi zuwan su Gwaggo ta hango za'a buga diramar ƙauyanci.

Natsuwa muka yi jiyo takun tafiya. Kaina na ƙasa na ke jiyo muryan Safiyya na ta kwara bayani da harshen da ba na ɗaukar komai a cikinsa, ni duk tsayin lokacin da muka ɗauka da ita ma ban taɓa tsammanin ta iya wani harshen ba bayan Hausa, kawai dai na yi mamaki sosai lokacin da muke makaranta yanda kaf makaranta babu wanda ya kaita iya turanci, balle ga shi ta gwamnati muke yi, lokacin har ga Allah ba ƙaramin kishi na ke ba, ashe da dalilin dalilai ba bahaushiya ba ce zuryan, da take ce min suna zuwa hutu Anambra ce na ke ko dai irin ƴan uwa na kalen dangin nne da su, gene ɗin Baba yafi yawa a jikinta shiyasa ba zaka taɓa cewa ita ɗin ruwa biyu ba ce.
Chapter 92 · 0% Book details