Sashe 96
Ƙayar Ruwa 2&3 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Muryan Nazifin ta fito tarr a cikin shirun da ya ratsa saboda ɗagawar muryar Malam. "Ban da masaniyar zuwan hukumar. Amma Malam yacca Sa'ida ta tsani yaran nan yanda ka san Annabi da kafiri, wallahi ban da ina da haƙuri babu namijin da zai zauna da macen da bata ƙaunar jininsa irinta, ba na son ace ina kai kararta shiyasa na ke barin takaicinta iya ni, kuma Malam ba ta ɗaukar yaran nan kwata kwata, ko nace ta ɗauke su sai taƙi, amma yau ta ɗauki yarinyar har ma da goyata ta fita da ita yin aiki"...
Sai Malam ya katse shi da cewa,"Da ta fita da ita aikin sai ta dafata ko ta soka mata wuƙa ko?". Yay maganar yana jifan Nazifin da mugun kallo.
Abbaana ya sauke nauyayyan numfashi yace,"Matsalar ka fito ka nuna ƙiyayyarka ƙarara kenan, ko kayi mummunan furuci, ita ƙiyayya ɓoyeta ake, magana kuma zarar bunu ce, ba komai duk ake gudu ba sai irin wannan ranar".
Malam ya dubi Yayan Zahra'un yace,"Kaga kuje zamu san yanda zamu yi da lamarin nan da kanmu, kuje kawai bama da buƙatar hukuma a ciki".
Ya kaɗa masa kai yace,"Ai ba zai yiwu ba ranka ya daɗe, lamarin kisa fa ya wuce duk inda tunaninka yake, idan ace ba'a gayyacemu tun farko mun sani ba shikenan, amma yanzu ba zai yiwu mu ƙyaleta ba duk da cewa suspect ce a wurinmu, idan muka barta ko da bata aikata ba zafin zuciya zai iya sawa ta zo ta aikata abun da ba daidai ba, ko kuma ta aikata ɗin an tafi an barta to gaba ma zata ƙara yi, so dole ne sai mun tafi da can wajenmu an shigar da bayanai duba da yanda ita uwar yarinyar ta shigar da ƙorafinta, sannan kaga su da suke ƙarar suna shaidu ita kuma babu wata shaidar nuni da cewa bata aikata ɗin ba, if ace ma da akwai zamu iya duba case ɗin iya nan mu gani idan na ƙyalewa ne mu ƙyale, to amma yanzu zamu tafi da ita ta bayar da nata bayanan suma su ƙara ba da nasu duk mu shigar a rubuce, anan zamu duba muga me ya dace ayi, a'a lamarin zai tsaya iyaka station ne ko kuwa da yiwuwar mu tura shi gaban alƙali".
Durƙushewa nayi na fashe da kuka sosai mai tsuma zuciyar duk wani mai imani. "Wallahi ba ni na kasheta ba, wallahi wallahil azim ban taɓa yunƙurin cutar da su ba, ban taɓa ba...".
"Kinga ki adana duk wasu kalamanki idan muka je can kya mana bayani, anan babu wani amfaninsu gareki...Amm ku sata a gaba muje".
Abbaana yace,"Yallaɓai a yanzu ne zamu iya shigar da tamu ƙarar na cewa bamu yarda da abin da ake tuhumarta ba ko kuwa sai kun gama shigar da rahoto?".
"Ehh da zarar mun gama jin bayanansu idan munga da yiwuwar zuwa gaban alƙalin to kuna iya neman lauyan da zai tsaya muku, koma dai me kenan zaku ji daga garemu acan station ɗin".
Yashaik yace,"Yallaɓai mu ta ɓangarenmu zamu iya shigo da likita cikin case ɗin don bincike kafin ayi jana'izar yarinyar?".
Ɗan jimmm yay kafin ya ɗaga kai yace,"Ehh zaku iya hakan ma dabara ce ta nemarwa kai mafita, da kuma sauƙaƙawa shi lauyan na ku idan har maganar ta kai gaban alƙali kenan".
"Bari a saka mata hijabinta". Maman Yasmin ta faɗa yayin da take dakatar da tafiyarmu, hijab ɗin ta saka min sannan muka wuce, ɗan sanda ɗaya gabana ɗaya bayana. Zan shiga motar ƴan sandan Abbaa ya ce,"Babu bawan da ubangiji ba ya jarabrtarsa, taki kalar jarabawar kenan, me cikakken imani shi ke karɓar ƙaddara a duk yanda ta zo masa. Ki yi ta kiran Allah cikin zuciyarki da bakinki, sannan ki nutsu wajen yi musu bayani wanda ba za'a samu matsala ba ki ƙara dulmiya kanki a ciki, ba na so tsoro yasa kiyi musu ƙarya kin ji Sa'ida, ki faɗi dukkan gaskiyar da kike da ita, kar barazana ko tsawa ko duka su sa ki canja daga abin da kika faɗa da farko, babu abin da zai ƙwace ki face gaskiya. Zamu biyo bayanku yanzu, Allah yayi miki albarka ya kuma shiga lamarin".
Tun da Abbaa ya fara maganar kallonsa kawai nake yi ta cikin ruwan hawayen da ya cika a idona. To ban san ya zan fassara yanayinsa ba amma daga amon muryarsa zuwa yanayin da ban taɓa ganinsa a ciki ba, zan iya cewa wani al'amarin daban da ban tsammata ba zai iya faruwa.
Na fashe da kuka sosai, ƴan uwana ne kawai suka fito ganin tafiyata banda Yaya Imam da ya tsaya daga ciki, ina jin mahaifiyata na gunjin kuka, Safiyya ma na yin nata tana neman zabura ta shigo motar. Sai ga inspector ɗin sun fito shi da Yaya Imam da kuma Nazifi wanda har wa lokacin yake riƙe da gawar a hannu. Lokacin da motar zata ta shi Yaya Imam yace,"Ki bar kuka, daga nan zuwa bangon duniya su shigar da ƙara, kina da Allah kuma kina da mu Sa'ida, zamu tsaya miki ko da silar hakan zamu ƙare, nayi miki alkawarin bayan kukan mutuwar rashi da za ki iya yi anan gaba, to kin bar yin kowanne kalar kuka na ƙunci muddin ina raye".
Wani sabon kukan ya zo min, garin na kalli Yaya Imam ƙwayar idona ta shiga cikin ta Nazifi, nayi saurin rufe idona tare da kifa kaina a saman cinyoyina. Haka aka tafi da ni mutane sai kallona suke yi, nayi ƙoƙarin rufe fuskata kamar yanda Anty Naim tace min.
Muna zuwa can station ɗin na roƙe su akan su da su taimaka min nayi sallah, aka haɗa ni da ɗan sanda ya rakani zuwa banɗaki nayi alwala sannan ya dawo da ni ofishin insifecta, nayi sallolina na azahar da la'asar, na nemi taimakon a bani ƙur'ani duk ba a hanani ba, na ɗan yi karatu na mintuna uku sannan na ɗaga hannu sama ina faɗawa Allah, kuma lokaci ɗaya sai naji natsuwa tana wanzar min, dukkan wani tsoro na korewa daga zuciyata.
Sai da aka yi sallar magriba nan ma aka barni nayi sallah, sannan suka zo shigar da rahotona, aka yi min tambayoyi na faɗin dukkan abin da yake nan, suka kammala rubuce rubucensu bayan ɗan wani lokaci ina nan dai wurin zaune aka shigo da ita Zahra'un da Nazifi. Ita da ta shigar da ƙara ta bayar da nata bayanan sannan aka yi mata tambayoyi, bayan sun gama da ita shima ya bada nasa kana ɗan sandan yace suna iya tafiya zasu neme su daga baya.
Ni kuma aka shaidawa su Abbaa za'a tsare ni nan da zuwa gobe su gama bincika bayanai. Iyayena da Æ´an uwana suka kasa tafiya, Ummani har lokacin kuka take yi, Safiyya ma haka wacca ke ta kirayen waya, haka Malam ma shi da Yayan Shago, har aka shigar da ni cikin sel duk suna tsaitsaye, bayan an rufe kuma suka juya suka tafi kowa jiki a mace.
Ina zaune cikin bayan shafe tsayin wasu lokuta, nayi nisa cikin tunani sai naji an ƙwanƙwasa ƙarfen sel ɗin. Na buɗe ido sai naga Abbaa tare da ɗan sanda, na taso da sauri na zo na tsaya bakin wajen.
ÆŠan sandan yace da Abbaa,"Minti goma muka baku".
Abbaana ya zauna ƙofar sel ɗin ya buɗe kwanon abinci yace na zauna nima, daga bakin ƙofar na zauna shi kuma yana saka hannu cikin kwanon abincin.
"Daure ko babu yawa ki ci abinci kin ji. Ba na so ki kwana da yunwa".
Ba na jin bakina zai ji ɗanɗanon wani abinci, haka babu buƙatar abincin a cikina. Amma saboda Abbaana haka na buɗe baki yana zuro hannunsa ta ƙarfen yana saka min ina ci, ban daina amsa ba har sai da ya barni da kansa.
"Bari a siyo miki lemu ki sha ko". Ya faɗa yana lalubar aljihunsa wanda na san babu ko naira biyar a ciki, na riƙe hannunsa ina girgiza masa kai na ce,"Abbaa na ƙoshi ai".
Ya miƙe yana faɗin,"Bara to na ɗauko ruwan kinga na manta shi can kan kanta".
Yana tafiya ya dawo jikinsa sai rawa yake yi, kamar yanda sai da ya fara cin abincin a ɗazu haka yanzu ma sai da ɗan sandan yace ya fara shan ruwan duk kuwa da pure water ne. Lokaci na cika ɗan sandan ya cewa Abbaa lokacinsa ya ƙare, Abbaa yace min,"Kar ki hana kanki bacci, kuma ki yi min alƙawarin ba za ki kwana kina kuka ba, sauran pure water ɗin guda biyu kiyi alwala cikin dare kiyi sallah. Sai mun dawo zuwa goben idan Allah ya kaimu".
ka ina ji ina gani Abbaa ya tafi ya barni, duk da tun ɗazu yana ta ɓoye min hawayensa amma a yanzu ina ganin yacca yake sa hannu ya share su, gefe ɗaya kuma bayan ruɗani da tashin hankalin wannan case ɗin, na kassa tantance wani yanayi na daban da ke tare da shi wanda tun a gida naga hakan, sai dai zance ɗan iya cewa kamar me shirya wani abun.
*B3ƘR14FT5*
Na sauke numfashi bayan fitar Safiyya, ɗakin na bi da kallo, masha Allah ya haɗu sosai ga shi ƙatoto, kuma funitures ɗin sai suka yi tamkar daga waje aka kawo su ba haɗi na gida ba, wadrobe ɗin ma irin me zugewa ce gaskiya Sale yay min matuƙar ƙoƙari, ana siyan wadrobe da gado ma kawai na miliyan guda amma shi kaf set ya haɗa min na alfarma, duk da banga kujerun ba amma na san suma sun haɗu.
Ina zaune shiru shiru Salim bai shigo ba, zuciyata ta cika fal da kishi da ɓacin rai, ban da tabbacin yana wurin matarsa, to amma in ba can ɗin ba ina ya zauna bayan ya san an kawo masa ni ɗaki, rumtse ido nayi ina jin ciwo a ƙasan raina, nayi ƙwafa na tashi a raina ina ƙudurtar in har na idda sallah bai shigo ba to zai zo ya tarar da ƙofa a rufe ne, sai yay zaman nasa can wajan makiran matansa ɗin da ni ban wani yarda da ita ba.