← Book details Ƙayar Ruwa 2&3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 95 OF 113

Sashe 95

Ƙayar Ruwa 2&3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Safiyya kuka take na goyata ya ɗaukota, bacci tayi a bayana Safiyya kafin ta farka kuma daga nan...". Kukan da yaci ƙarfina ya hana ni ƙarasa me na ke son cewa. Ita kuma tana cewa,"Daga goyo sai mutuwa, ya za'ai haka abu kamar shiri. Kinga gani nan zuwa gidan". Ƙit ta kashe wayar ina jinta kafin kashwewar tana faɗin,"Anty ba ni aron maƙullin motarki".

Anty Naim tace,"Amma abun da matuƙar ɗaure kai, to dama yarinyar bata da lafiya ne ko me?".

"Wallahi ban sani ba, ni dai na goyata kuma na sakkota babu rai".

"Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un, lallai kin shiga tsaka mai wuya, tabbas kina cikin garari me fitar da ke sai Allah. Amma kwantar da hankali bi'izinillahi Allah zai yayyafawa bala'in sanyi. A hankali nace,"Amin".

Rufe bakina kenan sai jin muryar Yaya nayi ta shigo ɗakin tana zage zage, na buɗe ido a wahalce da duk suka ƙanƙance, gayyarsu da na gani ita ta tsorata ni yawu me azaba ya wuce a maƙoshina.
"Ai yanda kika kashe mana Æ´a muma sai mun ga bayanki". Maganar da suke yi kenan suna É—ure É—uren ashar suna neman rufe ni da duka, Anty Naim tayi saurin tashi ta kareni. Yayan ta fallawa Rumana mari tace da ita,"Don ubanki fice kafin kema ta kashe ki". Yarinyar na kuka ta fita tana waigowa ta kalle ni.

Kun san ance sarkin yawa yafi sarkin ƙarfi, duk yanda Anty Naim ta so ɓoye ni sai da suka tureta suka fizgo ni. Ba zata iya da su ba haka ta fita da sauri wai tana ƙwalla kiran neman taimako, To waye zai taimake ni a cikin gidan nan? Ban da muryar da zan ɗaga na ce ta dawo ta ƙyalesu suyi yanda zasu yi da ni. Anty Fati ta fizgoni na miƙe Fati ta kawo hannunta zata mare ni nayi saurin kawar da fuskata. Kan na farga kuma Zahra'un ta shiga dukan cikina tana wallahi sai dai idan ta kasheni itama a kasheta.
Ana haka sai muryar Nazifi naji yana cewa,"Yaya ku zo, Ke Fati kamo Zahra'un ku fita".

"Ai Nazifi ka bari mu raunata shegiya".
"Malam ne ya zo".

Jin hakan sai É—akin ya zama kamar anyi ruwa an É—auke yay tsit, shi ya zo ya fizge Zahra'un wacca ke ta abubuwa kamar me iska, ficewa duk suka yi. Anty Naim ta dube shi tana gaida shi, ni kuma tuni na rikice da ganin nasa tsaye kaina yana jifana da wani irin kallo na me zan miki na huce.
har yanzu Iman na hannunsa, hawayen da suka ƙafe tun ɗazu suka gangaro, ban iya ɗago kaina a jikin bangon ba nake ce masa,"Kar ka yanke hukunci cikin fushi, don Allah kar yarda da zancen zuciyarka".

A ƙalla ya kai cikakken minti ɗaya kafin ya buɗe baki yace da ni,"Ki sakko ƙasa, jiranki ake kar ki ɓata min lokaci". Yay maganar da wata irin murya yana juyawa.

Ni kuma na dubi Anty Naim nace,"Kiyi haƙuri kin zo gidan namu babu yanda yake".

Ta kamani tana zaunar da ni tace,"Sa'ida ai ni lamarin duk na rasa ta cewa".

Miƙewa nayi a dabarbarce zan fita, sai ta dakatar da ni wajen ruƙo hannuna, ɗankwalina da ke ƙasa ta durƙusa ta ɗauko ta ɗaura min wanda ni ban ma san babu ɗankwalin akaina ba. Rumana na kuka sosai ta riƙe Anty Naim tana ce mata,"Don Allah kar ki kai musu Antyna, kar ki kaita don Allah, Ƴan sanda ne suka zo, kuma Iyam tace tafiya za'ayi da ita".

Nima ta kamoni tana cewa,"Anty kar kije, kar ki je Anty".
Fita kawai nayi fuuu tamkar iska ce ke hankaɗa ni, wanda bai sani ba kuwa zai iya cewa ga mahaukaciya nan, Anty Naim ta biyo ni da sauri tana riƙe ni saboda nema na ke na faɗi a matattakalar na gangara wajen sauka.

A falon na tarar da mamaki da akasin sa, nayi matuƙar kaɗuwa da police ɗin da na ke gani, sai dai fa yanda na gansa da sauran mutanen da ke a falon ba ƙaramin amsawa zuciyata tayi ba wanda ta kai ga har sai da na kai hannu na dafe ƙirjina.
Shine tsaye a tsakiya rungume da yarinyar da ta mutu, sai ita Zahraun na kan kujera Inna da Marawiyya a kusa da ita sun riƙeta alamu ife ife take faman yi, su kuma tawagar Iyam duk suna tsaye ƙofar ɗakinta. Daga gefe Malam ne a tsaye hannayensa harɗe ta baya kansa sunkuye a ƙasa, sai Abbaana shima a kusa da Malam ɗin ƙwayar idonsa cak a kaina. Na girgiza sosai da ganinsa don ban san da zuwan nasu ba, can kujerar bayansa Ummani ce zaune ta rufe fuska da mayafi da gani ka san kuka take yi, har da su Yashaik da Yaya Imam.

Daga bakin ƙofa kuma ƴan sanda ne guda biyu tsaye masu baƙin kaya, sai ta ɓarin da su Abbaa suke wani ɗan sandan ne amma shi wandonsa ne baƙi rigarsa kuma sky blue.
Iyam tayo kaina ta cakumo ni daga hannun Anty Naim ta hankaÉ—a ni gaban É—an sandan wanda naji ta kira da Usman. Kafin ta fara kora bayanin,"Don Allah kuyi mata hukunci daidai da abin da ta aikata, wanda ya kashe a kashe shi ne. Ta kashe jaririyar da bata ji ba bata gani ba".

Malam ne ya doka mata tsawa da cewa,"Jummai ya isa! Kar na ƙara jin bakinki a wurin nan idan ba haka ba ranki zai yi mummunan ɓaci".

Kana ya kalli ƙofar ɗakinta yace da yaran,"Ku kuma kafin na ƙifta ido ku fita ku bar gidan nan, kar wacca tayi gangancin da minti ɗaya zata cika mata a gaban idona, kun sanni sarai zan saɓa muku".

Sum sum dukkansu suka yi hanyar fita cikin sauri.
Idona ya kai kan Zahra'u da ke kuka tana faɗin,"Yaya itace ta kasheta, Yaya ka ƙwatarwa ƴata hakkinta". Tayi maganar da ɗan sandan kusa da su Abbaa.

"Saka mata ankwa". Furucin da Yayan nata yayi kenan, nima kuma yana kallona cikin ɗaga murya wanda har sai da naji tsoro ya ce,"Ke bada hannunki". sai ɗaya daga cikin ƴan sandan da ke tsaye bakin ƙofa ya tako ya zo gareni, ya buɗe ankwar yana cewa na ɗago hannayena. Muryar kukan Ummani ta cika falon da faɗin,"Don Allah a fara bincike tukunna, ku fara bincike amma tabbas Sa'ida ba zata kashe rai ba, ba zata kashe jaririya ba, ajalin yarinyar ne yazo ta hannunta amma ba ita ta kasheta ba".

Yanda take maganar a ruɗe take. Ta taso da hanzari zata zo wajena Abbaana ya riƙeta. Sai ta sake fashewa da kuka tana faɗin,"Abbaa kar ka bari su tafi da ita, yarinyar nan sharri aka yi mata wallahi".

Muryan Abbaa da Allah É—aya ya san me yake cikinta yace,"Na sani Sa'adatu, Na sani Sa'ida ba ta aikata abin da suke tuhumatarta da shi ba, sai dai lamarin a zargeka da kisan kai babba ne wanda a halin yanzu ba zamu iya yi mata komai ba. tun da har shi mijinta ya yarda ta aikata to babu me yarda da ba ta aikata É—in ba, mu bar hukuma tayi nata aikin, mu kuma zamu kwana muna gayawa Allah da shi ne shaidarta, Allahnta shi kawai zai kawo mata mafita".

Idona a kansu dukka, a raunane suke maganar, sai naji na bar tausayin kaina na koma tausayinsu. Kallon ɗan sanda nayi babu musu na ɗaga hannayena biyu a haɗe na miƙa masa.
Sai Anty Naim tace,"Ku tsaya! Ankwa! Asaka mata ankwa kamar ya? Ina shaidar cewa tayi kisan kan da kuke tuhumarta?".

Yayan Zahra'un ya É—aga mata murya da faÉ—in,"Wacece ke da za ki hana hukuma yin aikinta, ba ki da hurumi a wannan lamarin saboda haka ki koma gefe".

Ta dube shi tace,"Idan da hadasi akanka zaka san cewar ina da hurumi akan lamarin da ya shafi maƙociyata. Ba zan yarda da wannan cin zarafin da ake neman yi ba. Zargi ne kuke yi, baku da tabbacin ta aikata".

Ya nunata da bindigar hannunsa yace,"Malama ki iya bakinki, hukuma ba sa'arki ba ce".

Safiyya ce ta faɗo falon tamkar an jefota, turus tayi daga nesa tana bin hannayena da ke cikin ankwa da kallo, haka har ta ƙaraso gabana cikin girgizar al'amarin. "Ankwa suka saka miki Sa'ida? Tafiya za su yi da ke? Mene hujjarsu na kin kashe mu yarinya?".

Sai kuma ta damƙi kafaɗata da iya ƙarfinta tana jijjigata cikin ɓacin rai take faɗin,"Tun yaushe na gaya miki ki nisanci taɓa mata yara tun da bata so, sau nawa na faɗa miki kar ki ƙara kallon ko da inuwar ƴaƴanta ne, ke me yasa ba kya jin maganata ne, me yasa idan na ba ki shawara ba kya ɗauka? Yanzu ai ga irinta nan, garin nunawa ƴartata ƙauna suna miki ƙazafin yin kisa".

Sai ta juya tana kallon ɗan sandan tana cewa,"Cire mata wannan abar da ku ka saka mata". Tayi maganar cikin ƙarajin murya tana neman ta warci maƙullin.
Ganin ta ruɗe tana neman itama sanya kanta cikin matsala sai Abbaa yace da Maman Yasmin ta kamota, Maman Yasmin da Anty Naim suka ruƙota tana fiffizgewa tana faɗin,"Abbaa wallahi sharri suke mata, ɗan sanda ƙarya ne kar ku ci mutuncinta, na rantse da Allah ƙarya suke mata sharri ne ba zata aikata ba, Abbaa dama akwai abin da baka sani ba gama da zaman Sa'ida a gidan nan, zan maka bayanin komai Abbaa a wannan karan ka tsaya ka saurareta".

Maganar take yi tana kuka sosai tamkar ita aka ce tayi kisan, ta faɗa jikin Ummani ta ƙanƙameta tana cewa,"Nazifi sai Allah ya kamaka, haƙƙinta ba zai barka ba sai Allah ya saka mata da gaggawa, wallahi sai rayuwa ta wulaƙantaka akan baiwar cutarwa da ka yiwa Sa'ida, ka jira yi lokaci talala ne yanzu duniya take ma".

Muryar Malam na fidda ɓacin rai tsantsa yace,"To wai ni matsalar cikin gidanka ma me ya kawo hukuma cikinta? Su waye shaidun gani da idon cewar tayi kisan har akai gaggawar gayyato hukuma? Yarinya dai gata nan a hannunka babu ƙwarzanen komai, to da me tayi amfani ta kashe maka ƴa? Ko haka ɗaya ku ke neman ɗora mata laifin da bata ji ba bata gani ba".
Chapter 95 · 0% Book details