Sashe 36
Ƙayar Ruwa 2&3 Complete Hausa Novel · about 7 min read
Ana haka Imam ya ƙaraso, da ƙyar ya iya tsayawa ya kashe machine ɗinsa saboda tafarfasar da zuciyarsa take yi musamman na ganin Nazifi a ƙofar gida, ƙofar gidan ma har yana kai yatsa ƙirjin Yashaik ya nuna shi. Ko maƙulli bai tsaya cirewa ba ya tafi da sassarfa yana zuwa ya damƙi hannun Nazifi da ke nuni da Yashaik, ya barƙala shi yana faɗin,"Wallahil azim ko Sa'ida ka nuna da yatsa a gaban idona sai na karya ƙasusuwan hannunka...Ka zo da abin da muka umarceka ko kuwa sai na sassaɓa maka kamanni tukunna ka shiga hankalinka ka bi umarninmu".
Maganar yake gaba ɗaya ma ya mance da ya barƙale hannun Nazifi, sai da Yashaik ya taɓa shi tukunna ya sakar masa yana dukan ƙirjinsa tare da tankaɗa shi baya. Hayaniyarsu ta fito da Abbaa wanda ya leƙo cikin dattakunsa yace,"Sa'id kaga ku shigo daga ciki saboda maƙota da jama'ar unguwa".
Imam na kallon Abbaa yace masa,"Mu shigo da shi ciki?".
Abbaa yace,"A'a ku barsa dolensa ma zai shigo da ƙafafunsa, ai da sauran tunani akansa da har ya gane ya zo da ƙafafunsa na marasa mutunci".
Abbaa da Yashaik suka shiga ciki, yayin da Imam yake ma Nazifi wani mugun kallo da cewar,"Ka ci sa'a da kaga yanda zan maka ɗaukan saman ka, kuma ka shigo mana gida a gadarance sai kaga yanda zan kwarfe ƙafafunka ka baje a ƙasa".
Ya faɗa yana shige ciki ya barsa tsaye sanƙanƙan. Zuciyar Nazifi na jin wani ƙullutun baƙin ciki, shi babu babban takaici ma a wurinsa sama da irin yanda suke masa magana da nuna isa. Yay murmushin leɓe ƙasan ransa yana maimaita furucin Abbaa _,"Zai shigo da ƙafafunsa"._ shikenan zai gani shi da su waye a sama, itama kuma Sa'idan zata ƙwammaci kiɗa da karatu akan maganganun da ta faɗa masa, ba dai zata same shi gida ba ne.
Juyawar da zai yi sai ganin Malam yay ya sauka a daidaita sahu, ido waje yake kallon mahaifin nasa da son sanin manufar zuwansa. Har Malam ya ƙaraso ƙofar gidan bai ɗauke ido akansa ba haka bai iya cewa komai ba, mamaki ya ƙamar da shi cike da tsoron abin da ya kawo mahaifin nasa. Sai da Malam ya shiga soron gidan kana ya ɗago murya da ce masa,"Ban kai ka ganni ka biyo bayana ba ne mara mutunci da bai gaji arziƙi ba, ni dai nayi danasanin haifarka".
Ya haɗiye yawu yana rissinar da kai tare da bawa Malam ɗin haƙuri. Ashe da dalilin Abbaa na cewa zai shigo da ƙafafunsa, amma kuwa Malam bai kyauta masa ba domin ya so ya nunawa Abbaa cewa bai isa ba yayi kaɗan. Ba don ya so ba ya taka ƙafafunsa cikin soron cike da baƙin ciki da takaici.
Ina kaɗa miya a kitchen na jiyo sallamar Malam ɗin na taso da sauri na fito, ƙasa na duƙa ina masa sannu da zuwa, ya amsa gaisuwata yana saka min albarka tare da adu'a wadda naji daɗinta sosai har cikin raina.
Nayi masa iso ga ɗakin Kaka na ce,"Bismillah ka shiga". Sannan na wuce Nazifi wanda nayi tamkar ma ban taɓa sanin me zubin halittarsa ba, na tofa masa yawun bakina a ƙafafu ya san da cewar ƙyamatar ma ganinsa na ke. Kitchen na koma na ci gaba da aiki, bayan kusan minti goma sha Yaya Imam ya shigo ɗakin Ummani ya same mu da cewa,"Tashi ki je ana nemanki".
Na miƙe gabana na faɗuwa na saka hijabina na bi bayansa. Na shiga da sallama na nemi waje na zauna da girmamawa a gare su, Nazifi na tsakiya Malam sai zazzaga masa masifa yake yana zaginsa. "Dilla Malami tashi kaje ka ɗauko abun rubutu, kuma ka haura mintuna biyu za ka sha mamakina".
Yana ƙunci haka ya fita, Malam yana ta bani haƙurin abubuwan da suka faru, yana faɗin shima ba zai taɓa yarda da komawata gidan Nazifi ba, kuma ban kyauta masa ba da na kasa yi masa kallon mahaifi wanda ba zan iya kai masa kukana ba. Nazifi ya dawo da takarda da biro ya zauna gefe da ni, kamar an watsan wuta haka nayi saurin ja baya da shi don ko kusa ba na son ganinsa ma balle jinsa kusa da ni.
Abbaa yana dubansa yace,"Kaga darajar mahaifinka fa kaci har ka ɗauka mintuna masu tsayi haka a cikin gidana. Ban da haka niyyata kana shigowa su Imam su saka rubutun da baka so kuma su fitar da kai cikin ƙalilan ɗin mintuna".
Kansa ya É—ago ya kalli Abbaa yace,"Abbaa ba na son sakinta, zai fi kyau a sulhunta mu...".
Yaya Imam yace,"Ka san Allah ka bar ganin Malam a zaune anan idan ka kuma musu da abin da mahaifinmu yace zan jaka waje na farfashe bakinka, na lura yanda ka raina naka iyayen haka ka ke ganin zaka raina na kowa".
Yay maganar yana tasowa daga inda yake zaune yay tsaye akansa, ni dai ban kallesa ba ban kalli inda yake ba, amma ina da tabbacin yanda na tsorata da amon muryan Yaya Imam É—in haka shima ya tsorata wanda shine dalilin fara rubutunsa akan takardar babu shiri.
Yana gama rubutawa ya kallo inda na ke ya kira sunana da muryar da tayi kama da masu neman taimako. Ƙin ɗagowa nayi tamkar ban ji kiran ba, sai da Malam yace,"Sa'ida karɓi".
Na ɗago ina bin takardar da yake miƙo min da kallo, kafin na kai hannu na karɓa. Kuma wai saboda bai da cikakkiyar kunya har yana faɗa min,"Ba da son raina na sake ki ba, ki sani zan iya maida ke a kowanne lokaci".
Ni dai idona na kan farar takardar da ke É—auke da rubutun cewa _"Ni Nazifi Bala Mai Kalwa na saki Sa'ida Salman saki biyu"._
"Na sake ki saki biyu, da sauran igiyar aurena akanki".
Ya ƙara faɗa min da baki yana miƙewa zai fita Yashaik yace masa,"Butulu kawai wanda bai san mutunci ba mutunci bai raine shi ba balle halacci. Tun kana tsummanka baka da komai ka addabi rayuwar yarinya sai da ka aureta hankalinka ya kwanta, kuma kai ne yau ka wanko ƙazaman ƙafafunka a gaban idanun mutumin da ya dinga tallafar rayuwarka da jarin sana'a ka sakar masa ƴa, kai a ganin ka kaine da riba ko?, to bari kaji Sa'ida itace da riba domin tun farko daman taimaka maka tayi ta aureka ba don kun dace ba, kuma da sannu zaka girbi abin da ka shuka don Allah ba zai barka haka ba sai ya saka mata".
Fuskarsa ta nuna yaji zafin maganar, ya tsaya yana duban Yashaik yana sauke numfashi. Abbaa ya doka masa tsawa da cewa,"Dalla can fice ka bar min gida kafin nasa a fitar da kai".
"Ta zo ta kwashi kayanta da wuri".
Ina saurin buɗar baki nayi magana Kaka ya riga ni da cewa,"Kai ne matsiyaci kai kayanta suka dama, ba ta biɗar ko tsinke a wannan tsiyataccen gidan naka, ka adana su domin amfanin wataran...maza ɓace mana da gani".
Yana fita Malam ya shiga bawa su Abbaa haƙuri, Abbaa yana babu komai, shima yana cewa fatan wannan abu mara daɗi ba zai shafi zumuncinsu ba, Abbaa yace zumunci ai sai tsakanina da kai Malam Bala, amma babu matarka babu matata, haka babu ƴaƴanka babu ƴaƴana. Kuma ka jawa ɗanka kunne ko da wasa kar yay gigin sake bibiyar ƴata idan ba haka lallai ba zai ji daɗina ba.
Kaka yana kallona yace,"Tashi kije".
Na fita ƙafafuna a matuƙar sanyaye, da gudu na shiga ɗakin Ummani na faɗa jikinta, kawai sai na fashe da kuka sosai, kukan da na rasa na farin ciki ne ko kuma akasinsa. Ummani ta karɓi takardar hannuna ta karanta a hankali ta furta kalmar innalillahi wa'inna ilaihi raji'un, kafin ka shiga lallashina tana cewa,"Daina kuka, in sha Allah wannan rabuwar taku alkhairi ce gare ki mara misaltuwa, in sha Allahu ba za kiyi kukan zawarci ba sai dai ma ganin ranarsa tun da har gidan aurenki ya tauye miki abubuwa da dama".
Ni dai kuka kawai na ke yi, cikin idona babu wani abu da ke haska min face dukkanin rayuwar da na shafe tare da Nazifi tun daga ranar farkona na siyan rake a wajensa har zuwa wannan rana da ya miƙo min takardar sakina a gaban mahaifina. A hankali na furta,"Allah na roƙeka kasa ƙarshen jarabawar kenan".
__________________________________
*Gwarazan Labarai na ƙarshen shekarar 2023 masu ma'ana.*
*KWANTAN ÆAUNA*
Nana Haleema
*ƘAYAR RUWA*
Halimahz
*LOKACI NE*
Oum Mumtaz
*FARGAR JAJI*
Aisha Yabo
*WASA DA RAI*
Fadila Yakubu
Ɗaya ₦500
Biyu ₦800
Uku ₦900
Huɗu ₦1000
Biyar ₦1200
*Biyan KuÉ—i Ta*👇ðŸ»
6314170140
Fidelity Bank
Sa'adiyya Zakariyya Haruna
*Shaidar biya ta👇ðŸ»*
09061794195
*Godiya tare da adu'an fatan alkhairi ga wanda suka sami damar mallakar littafanmu, son So fisabilillah🥰*
#TeamFitattuBiyar
[2/2, 07:47] Hlm: *B2ƘR18FT5*
Tun daga wannan rana da na karɓi sakina a hannun Nazifi na shiga wani sabon babin rayuwa. Ni kam sai dai nace Alhamdulillahi don bana wani fuskantar ƙalubale da zan ce gwara zaman uƙubar gidan aure akan zaman zawarcin da nake yi a gidanmu, duk da a baya naji tsoro sosai duba da yanda na ke jin mutane na kambaba tashin hankali da musibar da ke cikin zawarci.