Sashe 43
Ƙayar Ruwa 2&3 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Ni dai duk a hargiste na ke ban san me yasa ganin nasa ya ɗaga hankalina ba na ke jin kamar irin ƴan iskan mazan nan ne suka biyo ni, haka na tsaya ina ta sauke numfashi ya kawo hannu zai taɓa fuskata na bige hannun nasa ina faɗa masa cewar kar ya soma wannan gangancin idan ba haka ba zan masa ihu na tara masa jama'a.
Na faÉ—a masa hakan ina faman huci wanda shi kansa sai da yay mamakin yanayin nawa.
Nace ya bani hanya na wuce sai ya kama faɗin wai dama zai gaya min ne Iyam tana asibiti watanta guda a kwance babu yanda take, yanzu haka ma anata cuku cukun fitar da ita ne za'a yi mata aiki wai ƙashin kwankwasonta ne ya samu matsala. Kaina a ƙasa na ce,"To ni mene nawa a ciki?".
"Ba za kije ki dubata ba?".
"Bisa wacca alaƙar da ke tsakani?".
"Tsohuwar matar É—anta mana, kuma surukarta".
Na galla masa harara zan wuce shi don magana da shi ma ɓata lokaci ne a wajena na lura bai da hankali. Sai kawai ya kama cewa,"Sa'ida na zazzo gida Babanki yaƙi saurarena, kuma ya hana ni na ganki, dama so na ke mu zauna ni da ke muyi magana ki sanar musu cewa kina so a mayar da aurenmu, ina so ki dawo gidana ko saboda Iyam Sa'ida, na miki alƙawarin babu abin da zai ke haɗa ni da ke kiyi rayuwarki irin wadda kike so, ba zan takura miki ba, ba zan ci zarafinki ba, kawai ni dai ina so ne ki bawa Iyam irin kulawarki".
"Amma dai baka da hankali da isassan tunani ko, kai wanne irin daƙiƙi ne da ka kasa lissafin rayuwa tsakanina da kai ta ƙare".
Nayi maganar cikin doka tsawa ina zare idanu kamar wadda ta fita hayyacinta.
Sai ya shiga takowa zai matso gabana na kuma waro manyan idanuwana ina dakatar da shi da faɗin,"Na rantse da Allah inci ɗaya ka ƙara tsakaninmu sai na ɗauke fuskarka da gigitaccen mari, kuma ka fita a rayuwata kar ka ƙara nuna ka sanni ko tsautsayi ya kawo ka ƙofar gidanmu".
Haka kawai kuma a lokacin sai na samu kaina da fashewa da kuka wanda na rasa dalilinsa. Shi kuma sai ya samu damar faÉ—in,"kin gani ko, kema kina so ki dawo gare ni amma taurin kai ba zai barki ba, ki faÉ—a min yanzu idan ba ki yarda na dawo da ke gidana ba waye zai aure ki".
Take na katse shi da cewa,"Wanda yake sona, ko an faɗa maka kowa irinka ne butulu ƙasƙantacce, haihuwar rashin arziƙi".
Sai yay ƙasa da murya yana faɗin,"Haba Sa'ida ban sanki da halin rashin kyautawa ba, ki taimaka ki dawo gidana ina da buƙatarki".
Na kalle shi da jajayen idanuna na ce,"Da dukkan alama a make kake, ko kuma ƙwaƙwalwarka ta samu matsala, ni zan dawo gidanka? Ka manta ni ce wannan mara wayewar, wadda bata jin turanci, wadda bata zuwa office, wadda bata iya soyayya ba kuma ƴar talakawa me satifiket ɗin sakandire, daɗin daɗawa Juya wacca bata haihuwa, Nazifi Bala Mai Kalwa mene amfanin mace irin wannan a gidanka? Menene abun buƙatar dawowarta gidanka?".
Sai kawai na fashe da kuka sosai da yin maganar tawa, na duƙa ƙasa na ɗebi duwatsu ina jifansa da su na zama kamar wata mahaukaciya, kuma ganin zan masa rauni yasa ya bar ni ya tafi yana faɗin in sake tunani. Ranar haka na koma gida duk a firgice babu irin tambayar da Ummani bata yi min ba na kasa bata amsa har yau.
Numfashi na sauke ƙirjina na bugawa sosai na ce da Yashaik,"Me ya zo yi?". Na faɗa da rawar murya.
Sai yay murmushi yace,"Kwantar da hankalinki, wai ya zo ne akan maganar yana so ya mayar da ke, na faÉ—a masa har abada to muna haka ne sai ga Imam ya zo, shi kuma kin sansa zuciya a wuya kawai ya rufe shi da duka, yay masa jina jina a fuska har ta kai dai ga mun tafi station, don da ace kuna tsakar gida zaku ji yo hayaniya a waje".
Idona ya cika da ƙwalla na ce,"Ku yi haƙuri Yashaik duk ni naja muku...".
Ya katse ni,"Kinga duk manta da wannan karɓi wannan".
Na sa hannu na karɓa envelop ɗin da ya miƙo min, ina ƙoƙarin buɗewa yace,"Bayan mun dawo Abbaa ya kira ni, wai anyi sallama da ke ya fita sai ya tarar da wani akan machine, yace masa aiko shi aka yi ya bawa Sa'ida. To gasu nan dai duka biyun takardar admission ne ɗauke da sunanki, duk Scholership ne da aka ɗauke miki ɗawainiyar komai tsawon shekarun da za kiyi karatunki ki gama, ɗaya University of Targu Mures ƙasar Germany, sun ba ki nursing studies, ɗayan kuma Scool of health ce Emirate za ki karanci Community Health..Ba'a san wanda ya kawo takardun nan ba Sa'ida amma kuma akwai phone number a jikin envelop ɗin na kira sai muka yi magana da shi Director na makarantar Emirate ɗin, yace Allah ne kawai ya kai sunanki wajensu kar muji komai idan zaki karatu to ki fara shirye shirye, babu wani abu da za kiyi komai an gama miki ko screening ba zaki yi ba...To mun yi magana da Abbaa shima yace Allah ne ya kawo miki, naji ta bakinki idan kina so shikenan, idan ba kya so shikenan".
Tun fara maganar tasa kallonsa kawai na ke yi na kasa rufe bakina haka na kasa ƙifta idanu, ba zan iya tantance yanayin da na ke jina ba amma tarin tunanine fal a cikin kaina. Ta ina zan soma?....
[2/2, 07:47] Hlm: *B2ƘR21FT5*
Cikin kwanaki jikin Iyam ya tsananta ta zama babu yanda take, kullum suna kan hanyar asibiti, ta koma gidan jiya bata iya komai sai dai ayi mata, daga kwanciya sai kishingiɗe, dama ga jikin tsufa idan ka ganta sai ta mugun baka tausayi, ƴaƴanta ma da suka shiga damuwa duk sun rame musamman Nazifi don ko a baya ma da bai da kuɗi shi ne komai akan ciwon nata, wannan dalilin yasa dole Malam ya haƙura ta koma gidansa. A hakan ma saboda irin magiyar da Nazifi ya dinga masa da ba shi haƙuri, har da haɗa shi da wani amininsa da Malam ke jin nauyinsa, du dai sai da akayi ta fama da shi don sai da ƴan uwa suka shiga maganar, yace shi idan suka takura shi ma sai ya sallameta, lokacin da ta tafi ta tare a gidan ɗan nata ai nuna masa tayi bai isa da ita ba, ta mayar da shi kamar babu aurenta akansa, har faɗa masa take ita ya ƙyaleta, don haka in har zata dawo cikin gidan to shi zai tattara sauran iyalansa su sauya matsuguni tunda dama ba shi ya gina gidan ba, da hakan dai aka ta basa haƙuri ana faman lallashi sai da ƙyar ya sakko ya yarda aka mayar da ita can.
Barinta gidan Nazifin kuma ba ƙaramin daɗi ya yiwa Zahra'u ba, dama sam bata son zamanta a gidan tun ma Sa'ida na gidan, lokacin kawai kirsa ce irin tata don ta samu fada a wajen Nazifi shiyasa bata fito da ɓoyayyan halinta ba akan uwarsa da ƴan uwansa. Yanzu gidan ya zama daga ita sai ƴan uwanta, ƴan uwan Nazifi duk basa tunkarar gidan, waɗanda ba su san meke faruwa ba ma idan suka je basa marmarin ƙara komawa domin ba a yi musu tarba ta mutunci, duk wanda yaje sai ta wulaƙanta shi, yanzu haka kaf dangi baki ya ɗauka Nazifi bai yi sa'ar matar aure ba, babu wanda bai zaginta a cikin danginsa, ko hidima ce ta tashi bata zuwa, in ba yay mata da gaske ba a hakan ma idan taje to a tsaitsaye kallon raini da wulaƙanci zata je ta dawo, wai ƙyanƙyaminsu take bata son shiga cikin ƴan ƙauye.
Gaba ɗaya yanzu Nazifi jinsa yake wani empty, ba shi da natsuwa kwata kwata, ko wurin aiki ya fita hankalinsa na kan mahaifiyarsa, idan ya dawo wurin aiki ma can gidan yake tafiya ba ya dawowa gida sai wajen sha ɗaya, dalilin hakan kusan kullum sai sun yi rigima da Zahra'u waccca ke ƙorafin yana tauye mata hakkinta, ai itama tana da hakkin lokacinsa ba wai ya tattara duka lokacinsa wa mahaifiyarsa kaɗai ba, ga ƴarsa nan har ta fara yi masa ƙiwa.
Wani sa'ilin har fargabar dawowa gida yake yi, ba don komai ba sai saboda masifarta da fitinarta, nema take ta hana shi kwanciyar hankali sam. Kuma ba ya bi ta kan fitinartata domin abin da ya ishe shi shine ya ishe shi, shi kaÉ—ai yasan a halin da yake ciki, idan yana biye mata zata kai su ga haifar É—a mara ido, a hakan ma don ya tsaya a tsaye ne ya zama namiji a gidansa, yana tsawatar mata kuma tana É—an shakkarsa idan ya rikiÉ—e mata, da rainasa É—in da zata yi tamkar yaronta haka zata mayar da shi.
Yanzu ba damar ya zauna waje ɗaya sai ya fara tunanin shi fa da Zahra'u akwai ƙauna me ƙarfi da fahimtar juna tsakaninsu, sai dai bai san me ya lalata alaƙar soyayyarsu ta mata da miji ba, ko kafin aurensu irin yanda take kautatawa ƴan uwansa Allah ne kawai zai biyata, amma yanzu ya rasa me ya canjata lokaci ɗaya, daga ina haka canjin hali da ɗabi'a? Nuna masa take tamkar ita ke aurensa, hakama can gidan su gani suke yi tamkar ai alfarma suka masa suka ba shi ƴarsu, tun da ko ranar da ta kaiwa mahaifinta ƙararsa sai da ubanta yaci masa mutuncin da kare ba zai shinshina ba, har wai yana faɗin ai ƴarsa tana da freedom don haka ya barta tayi duk abin da taga dama a cikin gidan aurenta, kuma dama lokacin da zai aureta ba su yi yarjejeniyar zata yi zaman bautawa mahaifiyarsa ba, saboda haka kar ya ɗorawa ƴarsa wahalar da ba zata iya ba.