← Book details Ƙayar Ruwa 2&3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 69 OF 113

Sashe 69

Ƙayar Ruwa 2&3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"To yanzu dai na ce musu su turo yaron ya same ni zuwa jibi idan Allah ya kaimu saboda bana so a saka wasa a lamarin, sai dai ita É—in bamu sani ba ko ta amince".

"Kai rabu da ita yanzu ai ba shashasha bace da hankalinta ta san inda ke mata ciwo, a bayan ma ƙuruciya ce ta hanata gane wanda ya kamata ta aura".

****"Maman Nana ni zan wuce". Na faɗa a sa'ilin da na ke ɗaukan jakata ƴar ƙarama na riƙe a hannu. Maman Nana tace min,"To Sister Sa'ida sai Allah ya kaimu, ki gaida gida ki gaida su Ummani".

Na amsa mata yayin da Khadija ke tsokanata da cewa,"Wai ke don Allah ko ki É—an gwada soliderity watarana ki ce za ki kwana".

Ina murmushi na ce,"To madam indai za ki bar min albashinki na watanni biyu ni kuma zan dinga haÉ—awa da aikin ki".

"Ehh lallai da ya ke ni bani son kuÉ—in".

Ina dariya kamar yanda kowa yay na ce,"A'a to ke fa kin je saudiya, ni kuma so na ke nayi nayi na kwashe iyayena na kaisu su sauke farali, kinga idan na samu Æ´ar 380 duk wata ai tuni zasu wuce umra".

Maman Nana tace,"To Allah dai ya cika buri, ki yi maza kinga Ummani ta bani amanarki yau kin yi dare".

Nace,"Wallahi fa kinga Yaya Imam É—in ne ma har yanzu bai kira ni ba, É—azu ya kira nace masa Dr yace in tsaya saboda waccan matar da akai wa operation to ina ga ko tunani yake bamu gama ba".

"To ki kira shi mana".
Na ɗan karayar da wuya ina cewa,"Wallahi Maman Nana bana son takura mi shi, komai yake yi yanzu hankalinsa na kaina, Abbaa ne ma yaƙi ya bari na ke komawata ni ɗaya ni banga wani abu a ciki ba".

Suka haÉ—a baki wurin cewa,"Gata ne suka miki wallahi, mace yar tsaro ce sai da kulawa, ki gode Allah da ya ba ki iyayen da idon su yake akan ki".

"To bari naje, ni na manta ma daga yau nayi off ni da shigowa sai laraba".

Khadija da tsokana tace,"Dama kullum ana ba ki na goron albishir ai dole kike son zuwa aiki kullum".

Sauran pure water É—in da ke hannuna na jefa mata.
Da haka na fito daga Nursing station ɗin, Metrom na zaune muka yi sallama da ita, har na fito compound ɗin asibitin sai gata ta biyo ni tana ƙwala min kira da cewa,"Kinga ajiyar ki kin mance nima zan manta kuma".

"Sauri na ke ta yi kinga ƙarfe tara ta kawo kai, na gode".

Wasu hulunan sanyi ne da safuna Sister Hauwa ke siyarwa daga turkey ake kawo mata, shi ne na siya mana ni da Ummani da Safiyya, da yake safunan ma har da na maza sai na siya har Abbaa da Kaka.
Ina tafe zuciyata nata tunanin in kira Yaya Imam ko na ƙyale shi, har dai na fito bakin gate, tunda bai kira ni ba na tabbata wani babban uzurin ne ya riƙe shi, iyaka koƙari suna yi akaina, Abbaa zai rako ni kullum sai mun ci rabin hanya yake komawa, in dai kuma nayi evening to ya sakawa Yayyuna duty yau idan wannan ya ɗauko ni gobe wannan ne zai ɗauko ni.

Ina tsaye bakin gate na buɗe jaka ina laluben wayata sai naji gate man na ce min na matsa za'a wuce. Nayi gefe ce na ke ma ko Dr ne zai tafi sai naga ba motarsa ba ce. Na ɗaga waya na kira Yaya Imam yace,"Kin ganni na taho mashin ɗin nawa ya samu matsala yanzu haka ina wurin masu gyara, kiyi haƙuri gani nan zuwa kin ji".

Nace,"'To Yaya kana ta wajen ina? Na gaji ne wallahi yunwa ma na ke ji".

Yace,"Zan taho yanzu yi haƙuri".

Na kashe wayar ina sanyawa a jaka, na fara tafiyata ni É—aya cikin tsoron da ya fara kama ni, kafin na gama fita a layin ne Allah ya taimake ni na samu me adaidaita sahu na kuwa yi saurin tsayar da shi, na faÉ—a masa inda zai kai ni yace na bayar da É—ari takwas.
Na shiga ina faɗin Allah ya sauke mu lafiya, ban manta da adu'ar zama cikin mota ba, a koƙarinsa na tayar da babur ɗin motar da ke gefenmu tayi masa horn, na ɗan leƙa na kalla sai naga motar da ta fito daga asibiti ce ɗazu.

Mutumin da ke cikin motar ya fito ya ƙaraso yana cewa me adaidaitar,"Ina kayi?".

Yace masa,"Cikin gari nayi can wajen gidan sarki".

Yace,"Ok to nima can É—in nayi motana ne kaga ya samu matsala, samun bakaniken da zai zo ma yanzu aiki ne".

Na ɗan saci ido na kalle shi jin yanda yake hausar gwari, kananun kaya ne jikinsa blue riga me dogon hannu da baƙin wando, yasa bakin gilashi da face mask da sam ba zaka gane fuskarsa ba, zubinsa ma ba na hausawa ba ne duk da fuskarsa a ɓoye take.
Zan fito ya fara shiga sai naji yace,"Noo shige daga ciki".

Na matsa ciki ya shigo, ƙamshin turarensa ya daki hancina sai naji zuciyata ta motsa, kuma ban aune ba na tsinci gabana da faɗuwa sosai, yatsun hannuna har ji nayi suna rawa, sai da muka yi nisa sosai a tafiya kana na kira Yaya Imam nace masa ba sai yaje ba nama taho, ya gama min faɗansa ya kashe wayar.
Ni dai na yita mamakin mutumin ganin bai sauka ba duk da cewa bai faÉ—i inda za'a kai shi ba, muna tafen ma me adaidaitar ke daÉ—a tambayarsa yace masa no worry muje kawai idan anzo inda zan sauka zan faÉ—a maka.

Me adadaitar yake ce masa,"Yallaɓai ko dai baƙo ne kai a garin".

Na jiyo sautin karamin murmushin da yay kawai ba tare da yace komai ba.
Muka iso unguwarmu ina ta ma me adaidaitar kwatance har muka zo ƙofar gida, idona ya hasko min Abbaa tsaye a ƙofar gida hannayensa sarƙe a baya, ban san lokacin da na furta,"Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un, shikenan na kaɗe".

Mutumin ya juyo yana kallona me adaidaitar ma ya juyo, duk da banga ƙwayar idon da ke cikin gilashi ba na san dai ayar tambaya ce a cikinta dangane da furucin da nayi. Me adaidatar yace,"Hajiya akwai matsala ne?".

Ai kuwa kafin na buÉ—e baki Abbaa ya doka min tsawa da cewa,"Ba za ki fito ba ne".

Na haɗiye dunƙulallan yawu, mutumin ya fita nima na fito sai rawar jiki na ke yi, na ciro kuɗi na bawa me adaidaitar na wuce zan iya cewa ina jin yanda ƙwayar ido ta manne a jikina.
Muryar Abbaa tuni ta cika kofar gidan da faɗansa akan tahowar da nayi ni kaɗai, ga layin yay tsit ƙarfe tara da arba'in a lokacin, faɗi yake da uban dare na kamo hanya na taho ina matsayin mace, da ba zan iya jiran Imam ɗin ba me yasa ban kira Yashaik ko Al'amin sun je sun taho da ni ba. Hannu ya kawo zai buge ni nayi saurin shigewa cikin gidan, Ummani ma na tsakar gida na shiga tace,"Ya za ki mana haka, ba dole ayi miki faɗa ba ga wayarki anata faman kira ba ki ɗaga ba".

Idona a waje nace,"Wallahi banji kiran ba na sakata a silent".

Abbaa ya shigo yana ci gaba da faɗin,"Idan kika kuma tahowa ke ɗaya sai ranki yayi mugun ɓaci, kuma faɗa min gidan uban wa kika tafi?".

Jikina ya kama ɓari na shiga wallacewa ina faɗin,"Allah Abbaa babu inda na je".

"Ƙarya kike yi in ba haka ba me ya hana ki ɗaga waya? Kin san Allah zan soke fita aikin nan? Ba dai kin yi karatun ba kin samu na tsira da mutunci, to aikin ba dole ba ne zan hana ki".

Tuni na durƙusa ƙasa hawayen idona na neman sakkowa nace,"Wallahi Abbaa babu inda na je, kayi haƙuri don girman Allah".

Uwa me tausayin ƴaƴanta tuni ta shiga bawa Abbaa haƙuri da tausarsa akan yay ƙasa da murya dare yayi, cikin gida ana jinsa haka maƙota ma duk suna ji. Ya watsa min wani mugun kallo da cewa,"Ba zan ɗauki sakarci irin haka ba, kike jira duk dare za'a zo a ɗauke ki, amma wallahi kika ƙara kuskuren tahowa ke ɗaya daga ranar kin gama aiki".

Yana faɗa ya shige ciki, nima na miƙe na wuce ɗakina, Ummani na leƙowa tace,"Abincinki yana ɗakina".

Ko takalmi ban iya cirewa ba na zauna ina goge hawayena tare da danasanin tahowar da nayi. Ko kayan ban cire ba na tashi na fita zuwa ɗakin Abbaa, sai da na tabbatar ya haƙura ya daina fushin kana nayi masa sallamar sai da safe na wuce ɗakin Ummani na ci abinci.
Wajen sha ɗaya har na rufe ido naji wayata na ringing, da sauri na tashi na rarumota gudun kar Abbaa ya jiyo ƙararta, nifa mahaifina is very strict, bai ƙi ya zo ya ƙwace wayar ba, ban ɗaga ba sai da naga kiran yay yawa har sau uku sannan na ɗaga ana huɗun.

Nayi sallama aka amsa, shiru for some seconds sai aka ce,"Nurse Sa'ida ce?".

Na ce,"Ehh ita ce". Na faÉ—a ina jin muryan kaman na santa duk da cewan muryan namiji ne.

Sai aka ƙara cewa,"Sorry don Allah na kira ki da daddare, ɗazu na zo asibiti ne Dr Samuel yake bani number na ki yace duk sanda na zo na dinga nemanki, domin ke ɗin ƙwararriya ce wacca ta san makamar aikinta".

Babu shakka na san muryar sai dai ba zan ce ga inda na santa ba ko kuma ta wacece ba, a hankali yaci gaba da magana yana ce min yana fama da ciwon baya ne da ƙafa ko zan taimaka na recommending masa maganin da zai sha yanzu kafin zuwa da safe yaje asibiti. Na zage na buɗe murya ina ta kora masa bayani da tambayan ya yake ji, kusan minti goma haka sai naji ya katse ni da tambayan,"Babu dai wani damuwa ko?".

Na ce masa,"A'a babu, duk sanda kake neman taimako irin haka zaka iya kira na".

Sai ya sake cewa,"Thank you so much, but still ba ki cikin wani matsala dai ko?".
Chapter 69 · 0% Book details