Sashe 17
Ƙayar Ruwa 2&3 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Suka wuce ina bin su da kallo, irin set ɗin robar kayan wankan jarirai ne sai ƙatuwar baƙar leda da na san ba zai wuce kayan yaro ba. Abin na ta dai ba na Allah ba ne don ta ƙara samun shiga wajen Iyam ne da shi kansa Nazifin. Dama ai ita da Iyam ɗin kansu a haɗe yake sun ware Amarya a gefe baiwar Allah da babu ruwanta, ita kam zuciyarta fess babu datti.
Sama suka nufa, kuma nayi musu shiru ban shaida musu cewar tana ƙasa ba, tun da ba wurina suka zo ba ina na ke da hurumin faɗa musu kuwa, gwara nayi shiru kafin a ƙara faɗa min magana, ile sai ga su sun sakko suna raba idanu.
"Sa'ida ai babu kowa a wurin nata".
"Ta nan ƙasa ai". Ta bini da kallo wanda ke shaida taji haushi, ta kama faɗin,"To da ba sai ki shaida mana ba amma kika barmu muka hau. Ko don na ce ba wurinki na zo ba, to me zan zo nayi a wurinki ke da ba ƴaƴa ba balle na ce na zo ganin ƴaƴan Nazifi".
Ta gama maganganunta suka wuce, nan ma dai haka ta gama bin ɗakunan ƙasan ta dawo tana ce min. "Ina ne wajen nata ne, wannan ƙasan naku masu surƙuƙun waje duk a kasa gane masa".
Kamar na ce,"ki kira wayarta ki tambayeta". Sai naga hakan kuma ai zama da rashin girmamawa, ko ba komai matsayin uwa take, ni kuma ban da halin rashin kunya wa manyana. Na kalli Rumana zan ce ta tashi ta raka su sai naga ta ɓata fuska tana kaɗa min kai a hankali alamar bata son zuwa, kawai sai nayi musu nuni da hanyar dama ta jikin lungun tsakanin ɗakina da nasa ne.
Saudatu tace,"Wallahi Yaya Sa'ida idan da nice ba zan faÉ—a mata ba. Mtswww mutanen nan ba su da kirki ko kaÉ—an".
Nayi guntun murmushi bance komai ba. Ni dai hankalina duk bai ga kallon da muke yi, domin kuwa lokaci ɗaya naji gabana na ta faɗuwa kamar ƙirjina zai faɗo, na shiga adu'a amma inaa.
Tuni kuma sai na fara tunanin can gida, kwana uku kenan bamu yi waya da Ummani ba saboda wayarta ta lalace, wanda rashin jin nata ya haifar min da rashin kwanciyar hankali duk abin da nake ina daurewa ne kawai. Jiya ma sai Yashaik na kira yace idan ya shiga gidan zai haɗamu, Yaya Al'amin kuma haushi naji don ko a shekaranjiyan sau huɗu ina kira ina cewa ya haɗa ni da ita sai yace in kashe zai je ya kai mata amma sai inji shiru, ni kuma nayi zuciya na ce ba zan ƙara kiransa ba.
Kasa haƙuri nayi na kira Maman Yasmin, muka gama gaisawa muka yi ƴar hira sannan nace ko zata taimaka ta bayar akaiwa Ummani wayar. Tace min to bara ta duba ko zata sami yara don yanzu duk sun tafi Islamiya.
Shiru shiru bata kira ni ba har na ƙara kira tace bara kawai taje ta kai da kanta, na ce a'a ta bari ko su Yasmin suka dawo ta basu, ni dai kawai don Allah ta haɗamu. Bayan gama wayar tamu na kwanta, a raina ina jin ina ma ina da kuɗi in siyawa mahaifiyata sabuwar waya, da haka bacci ya ɗauke ni.
Ban jima da soma baccin ba na farka a tsorace ina salati, wani mummunan mafarki nayi wai ƙofar gidanmu cike da mutane an kafa rumfar tanfol, kuma na shiga gidan sai na tadda su Yashaik sunata kuka, na tsallake mutane na faɗa ɗakin Ummani da gudu, ina shiga na ganta itama tana kukan, na faɗa jikinta ina tambayarta me ya faru sai ta kasa ce min komai.
Daga tsakar gida sai naji ana Allah yasa ya huta yasa Annabi ya san da zuwansa, ban san lokacin da na fita ba ina tsallaka mutanen tsakargidan nayi É—akin Kaka, shima a can na sameshi shi da Æ´an uwansa da su Baba Tijjani, na bi kowa da ido Abbaana ne kawai babu, ban gansa ba haka kuma fuskokin duk É—insu da jimami.
Sai naji kafafuna sunyi sanyi na fito a gigice nayi ɗakin Abbaa, ina zuwa naga an saka kwaɗo abin da ba'a taɓa ba, wai sai naji muryar Hajjo na ce min kiyi haƙuri Sa'ida ita mutuwa dole ce, Abbaanki ya amsa kiran mahallicinsa. Ai ban san lokacin da na ƙwalla razananniyar ƙara ba na zube a wajen ina ihu ina kiran sunan Abbaa, aka taru akaina Ya Imam shi kuma na min ihun na rufewa mutane baki.
Ina hankalina zai kwanta da wannan mugun mafarkin, ai tuni na miƙe ina cewa da Saudatu,"Tashi ke ki shirya".
Itama yanda taga na fita a hayyacina ta kama tambayana, ban tsaya sauraronta ba na haye sama suka biyo ni suna ta me ya faru. Ko da na shiga É—aki sai na rasa abun É—auka, duk na ruÉ—e na riki ce. Ta zo ta kamani ta zaunar, Tuni kuma hawaye ya fara sauka a fuskata kamar an kunna famfano, ina ta juya kai na kasa cewa komai duk da cewar magana na ke so nayi, mafarkin ne yake ta haska min a ido.
Yawu naji tana tofa min wanda na fahimci adu'a ne take yi, ita kuma Rumana ta ƙanƙame jikina ganin ina kukan itama sai ta sa kuka.
Sama sama naji Saudatu na faɗin,"Kema da saka abu kike a rai, na san rashin jin Ummanin ya sa kika yi mummunar mafarki, dama shaiɗan me jiran kaɗan ɗin saƙa maka mummunan abu. bara a ƙara gwada lambar Ya Hindatun ko zata shiga".
Murya na rawa na ce,"Ba ita za ki kira min ba, kira me gidan nan ki faÉ—a masa zan tafi gida".
Ganin bata da niyyar kiran na ƙwaci wayar, ruwan da ya taru a idona yaƙi barina ganin screen ɗin wayar, sai itan dai na miƙawa nace ta taimaka ta kira shi. Ta kira har sau uku bai ɗaga ba, nima na karɓa na dinga kira amma bai ɗaga ba, duk da ba yau ne karon farko na rashin ɗaga min waya da yake amma na yau ɗin sai na fi jin na damu da shi, hankalina ya ƙara tashi, to kar dai mafarkin nan ya zama gaskiya Abbaa ya mutu, Ina zan sa kaina idan na rasa Abbaana a wannan gaɓar? Yaushe rabon da na gansa? kuma ya mutu yana fushi da ni? Bana so ya mutu duk da mutuwa dole ce, haka ba na so ya mutu sai ya san gaskiyar lamarin da ya faru akan case ɗina da Nazifi da yaransa.
Tunani nake akan na tafi kawai in yaso ko na ƙarasa gidan na faɗa masa, sai dai har kullum ina tsoron fita babu izinin miji duk da lalura ce ta kama a yanzun, to amma ai bani da tabbas. Zuciyata ta yanke shawarar na tashi na shirya kawai, kuma sai bayan mun shirya har mun sakko falo na tuna da kuɗin mota, naira ɗari ce da ni hagu da dama, na kalli Saudatu nace,"Nawa ne kuɗin hannunki?".
"ÆŠari ce".
Shiru nayi ina tunanin yanzu wa zai ɗaukemu ya kai har makwarari a ɗari biyu? ga shi kwanakin nan na fahimci can gida ma a matse suke don haka ba na ce in munje can ma karɓa ba.
Kiran wayar Nazifi na ci gaba da yi, nayi sa'a ya É—aga a wannan karon, ko sallamarsa ban amsa ba nace,"Don Allah zan je gida".
A daƙile yace min,"wanne rainin hankali ne hakan baki san da tambayar ba sai bayan na fita, kuma tun tashinki sai yanzu za ki kira ki tambaya, to babu in da zaki je".
Roƙonsa na shiga yi, yanda yaji ina masa magiya ya daka min tsawa da cewa,"Ke ya isa, ina tsaka da aiki kin addabe ni da kira kamar me bina bashi, na kira kuma kina min kuka da faman magiya, ke wacce kalar macece ne mara natsuwa da rashin sanin yacca ake magana da miji. Me ake a gidan naku dama?".
"Kayi haƙuri, zan je naga Abbaa ne".
Hmmm zuciyata ta matse jin yana tambayata,"Waye Abbaa?". Ya faÉ—a kafin na bashi amsa kuma sai ji nayi yana faÉ—in,"Hasbunallahu ai na manta ma gaba É—aya". Kamar an kulle masa baki sai yay shiru.
Na daɗa ruɗewa ina tambayarsa,"Me ka manta? Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un don Allah ka faɗa min wani abu na faruwa ne da aka ɓoye min?".
Ƙaramin tsaki yaja kafin yace"Ki shirya kije ɗin".
Na ce,"To don Allah ko zaka turo min da kuÉ—in mota, É—ari biyu ce da ni ba zata kaimu ba".
Sai ya ƙara cewa,"To wai dole ne zuwa gidan, ko kin manta har yanzu wa'adin da Baban naki ya ɗauka miki na rashin zuwa gidansa bai ƙare ba ne. Ko kiranki suka yi?".
A sanyaye na ce,"A'a hankalina ne yaƙi kwanciya don Allah kayi haƙuri ka taimaka min da kuɗin motar".
"Ki aika Saudatu ta karɓo miki dubu ɗaya wajen Amarya".
Na rumtse ido nace,"Amma...".
Ya katse ni da cewa,"Kinga idan ba za ki aika ba ki haƙura ko ki tafi a ƙasa. Ni dai kar ki ƙara kirana kina katse min abu me muhimmanci".
Daga haka ya katse wayarsa, ina jinsa kafin ya katse yana faÉ—in,"Hamisu kaga na manta ina cewa zaka raka ni gidan su Sa'ida, wanne asibiti ma Al'amin yace mana?".
Sai naji hawaye ya ƙara zubo min, zuciya da jiki na rawa na miƙe. Tabbas akwai abin da ake ɓoye min, kuma mafarkin nan yana haska min ne, haka nayi watsi da takaicin karɓo kuɗi wurin Zahra'u. Ban da yanda zan yi haka dole na tura Rumana ta karɓo, sai da ta jima aka gama jan lokaci sannan aka bata dubu biyu wai ya kirata yace ta ƙara mana dubu ɗaya. Rumana tana kuka akan zata bi mu na ce tayi haƙuri saboda makarantarta ba zai yiwu mu tafi tare ba.