← Book details Ƙayar Ruwa 2&3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 86 OF 113

Sashe 86

Ƙayar Ruwa 2&3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

A hankali na ce,"Ai ba ni na fara zuwa nace ina sonka ba da zan ke bibiyanka".
"Kika ce me?".
"Ba komai".
"Har na tausaya miki yarinya".

Sai na kalle shi leɓena na daɗa talewa da murmushi nace,"Wacece yarinyar?".
Da yatsansa guda ya lakuce min hanci yana faÉ—in,"Ke me dimple É—aya da rabi".

"Sa ido dai babu kyau, har ina kasan É—aya dimple yafi É—aya".

Kawai sai ya saki wani murmushi irin nasa na shi kaɗai me tsada da ya kusa sumar da ni, murmushin da ya tsaya min a rai wanda tuni ƙwayar idona tayi capturing nasa, Rufewar ido da buɗewarsa shi kawai na ke gani.
Cikin sati uku muka yi wani shaƙuwa na ban mamaki da Salim, shaƙuwan da zaka rantse mun fi shekara guda, ga wani fahimtan juna da muka samu a tsakani, sosai ya fahimce ni haka nima sosai na fahimce shi, zuwa lokacin na gane ashe nayi masa bahaguwan fahimta ne a farko, amma mutum ne shi mai sauƙin kai, ya iya mu'amala bai da damuwa sam sam, sai na ce kusan halin su guda da gidan su Safiyya a ɓangaren kirki da mutunta ɗan Adam, ba ɗagawa ba nuna shi wani ne ko ɗan wani ne, ga kyauta da son yin taimako abin hannunsa sam bai rufe masa ido ba, ina ganin hakan ne duk sanda ya kaini aiki ko ya ɗakko ni, ko idan ya zo gidanmu ya gamu da wani nawa, ko a hanya haka idan yaci karo da masu neman taimako, duk da ni bai fiya sakar min kuɗi ko bani abu ba, kyautansa bai wuce idan ya zo naje raka shi ya miƙo min sauran turarensa, sai wataran da ya cire agogonsa yay alwala na ɗauka na gwada sai yace ya bar min.

Na saki jiki da shi sosai ya zama best friend ɗina, bamu fiya waya irin bini bini an yi kira ba, hakan bai dame shi ba sai aka yi dace nima kuma dama ba na son namiji me nacin kira, ko da yaushe a waya ko idan yazo cikin raha mu ke da farin ciki gami da annashuwa, har idan ina tare da shi na kan manta komai, bana jin asaran ɓata lokaci tare da shi domin kuma a duk wata hira tamu sai na ƙaru da shi ɓangaren ilimi ne ko ita kanta rayuwa.
Yanzu ko da abu zan aiwatar shi na ke kira na nemi shawaransa, har Safiyya ke min ciwon bakin soyayya tasa na kware mata baya, nace ba za ki gane ba ne Beb, tace ni kuwa na gane tunda na san waye Yayana.

Ya haɗa ni da Mahaifiyarsa mun yi waya da ita, ranar ji nayi kamar na nutse a ƙasa don kunya, matan free take na fahimci tana da kirki sosai, tayi ta jana da hira tun ban amsawa har na saki jiki naji ma kamar tare da Ummani na ke, tana tambayan yaushe zan zo in ganta, ban iya cewa komai ba sai ita ke cewa to zata zo da kanta taga ƴarta, Kakarsa ma wadda ta haifi Babansa har da aike ta yo min na wani atamfa ankara me shegen kyau.
Har matarsa da yaransa duk mun gaisa da su, matar ma ita ne ta takura masa kan sai ya haɗa mu a waya, ni kishi yasa na ke ta zillewa ranar kuwa muna tare sai gata ta kira, muka gaisa da ita cikin mutunci da girmama juna, da farko ina magana a daddaƙile daga baya da na fahimci ita with all her heart take waya da ni sai na sake kawai, tace min ga yarana ma kafin su zo su ganni, ina ji yaran na tambayanta Maama waye take ce musu New Mommy ɗin su ce wadda Papa zai kawo ta haifo musu Baby Boy, ni dai nayi ta mamaki na ce to Allah yasa dai yanda ake faɗan bata da matsala hakan take, don ni har ga Allah idan na tuna da ita na kan ɗan ji fargaba haka, to amma shi kansa yana yawan faɗa min kamar yanda Ummansu Safiyya ke faɗa min Kudrat bata da problem zan ji daɗin zama da ita sosai, idan kishina ya motsa min zan ta cewa ya tafi wurin matarsa ya ƙyale ni, sai ya nuna min shi ba ya son hakan, yana son matarsa kuma nima yana sona kowacce da matsayinta a zuciyarsa, zai kuma yi ƙoƙarin ganin ya fita hakkin kowaccenmu.

Haka Salim yay amfani da salon soyayyarsa yay raga raga da zuciyata a lokaci ƙanƙane, ashe ma ni ban san komai ba a soyayya, soyayya tana inda aka iya a wurin mutumin arziƙi, har tsokanata ake a gida da wurin aiki saboda nema na ke na zauce kamar farin shiga, alerm ɗin wayata duk sai da na cire, in ƙarfe biyu da rabi tayi shi zai tashe ni in yi sallar dare, haka idan asuba tayi, da safe kafin na farka yay min text da daɗaɗan kalamai da suke sawa naji ni a gajimare, har idan ban ji daga gare shi ba na ke takura, in koma kamar mara lafiya, Salim ya mantar da ni duk sauran guntun damuwan da na ke yi na famin ciwo, banda wata matsala ni kam na yarda Allah ya kashe ya ba ni, domin samun namiji kamarsa a wannan marrar sai dacen ubangiji kawai, wai kafin ma na shiga cikin gidan nasa kenan, shi kansa yana faɗa min Baby ba ki ga komai ba a soyayyan da na ke miki da kulawa sai kin shigo gidana tukunna, duk da wani sa'ilin ina cewa Allah yasa kar ya sauya daga baya, aurena na baya yasa na gasgata zancen Namiji bai da tabbas.

Ya rage saura kwana uku biki, ana ta shirye shirye, ƴan ƙauyenmu duk sun zazzo wasu daga cikinsu, ni sai mamaki ma na ke ko a aurena na farko irin hidima da zumuɗin da ake a yanzu ba'ai a wancan lokacin ba, na farko kamar wani taron mutuwa haka aka yisa, ni ba'a farin ciki ɗari bisa ɗari ba haka suma iyayen nawa, amma a wannan kam farin ciki da zaƙuwar da na ke ciki sun kai kaso fiye da dubu, farin cikin Ummani har ba ya barinta rufe baki, ta kira wancan ta aikawa wancan, haka Abbaa na ma shi kansa kamar yanzu ne karon farko da zai aurar da ni.

Kuma wannan auren sai ya zo da albarka, domin kuwa wani buɗi ubangiji ya kawowa Abbaa, yanzu haka babban teburi ya kama a kasuwa, cikin gida kuwa sai da ya aje botikan fenti huɗu aka shafe mana shi kamar za'a aurar da budurwa, na lura dai kowa yafi farin ciki da wannan auren hatta yayuna, idan nayi magana sai Ummani tace bazawarar ai me daraja ce, ni dai sai in murmushi kawai, idan na ɗauko kuɗi na bayar ayi amfani da su sai Abbaa yace a'a hakkinsa ne yay min komai, nauyinsa ne ba nauyina ne ba, in adana kuɗina za su min amfani nan gaba, amma yanzu na bari su zasu yi min komai, hatta kuɗin ɗunkuna duk shi ya bani yay min kashedin kar na sake na karɓi ko sisin Salim,

Abbaa yace shi ba zai ƙarya ba amma zai iyaka ƙoƙarinsa wajen ganin ya fitar da ƴarsa kunya, haka ya yankewa Yayyuna kuɗi suka haɗa dubu ɗari biyu su huɗu, aka haɗa da kuɗin aurena dubu ɗari biyar, sai kuɗin kayan lefena da aka rage Ummani ta kaiwa Sale dubu ɗari uku tace don Allah yay min furnitures masu na miliyan ɗaya irin wanda ake yayi.
To da yake ma aiki ya mayar da shi Delta state satin baya aka yi masa ƙarin girma, Kudrat ma da ta kira ni a waya tana zolayana wai ni ƴar sa'a ce, dama sun gaji da zaman Edo ɗin, ba yanda ba su yi ba a tashi a gidan yaƙi sai ga shi dole tasa an tashi babu shiri, ita da yarana suna min godiya.
Salim ɗin na cewa ba sai anyi min kayan ɗaki ba, nayi karaf kuwa nace sam bai isa ba, na wani hasala kamar wanda ya zage ni, na dinka fifiƙa ina masa masifar ai ba'a gidan babu ya tarar da ni ba, Abbaa ma ba zai yarda da zance ba, mahaifina zai yi min kayan ɗakina idan ma ya san ya siya ya aje ya kwashe abinsa ya fitar da su idan kuwa ba haka sai dai idan ba zan zauna a gidan nasa ba, ni kuwa ai ban manta gorin da Nazifi yay min ba sanda zai ƙara aure na cewan iyayen matarsa har kayan ɗaki sun mata ba irin iyayena ba da suka bar miji da ɗawainiyan komai.

Saboda yanayin nisa zuwa can garin sai Sale yace zai ɗiba mutanensa suje Delta ɗin a haɗa kayan acan maimakon ace daga nan za'a a tafi, kuɗin mota ma kansa wani babban lamarin ne, hakan kuwa aka yi aka tafi da Yaya Al'amin da Abbayo, Salim ɗin yace akwai wurin zama a gidan nasa ba sai sun nemi hayan wajen kwana ba, Abbaa yace to gwara ayi tafiya ɗaya kawai tunda bikin ƴan kwanaki ya rage a tafi ayi jere gaba ɗaya, sanda ake fito da bahhunan kwanuka sai da nayi matuƙar mamaki, Ummani ba ƙaramin ƙoƙari tayi ba har sai da na tambayeta ina ta samu kuɗi haka tace rufin asirin Allah ɗan abinda take tarawa ne, sai kuma gudumawar da ƙannenta da yayyunta suka aiko mata, kayan kitchen masu kyau da tsada ni har ce nayi ma ina zan kai su.
Chapter 86 · 0% Book details