← Book details Ƙayar Ruwa 2&3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 39 OF 113

Sashe 39

Ƙayar Ruwa 2&3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Mazan kuma suna tare da mahaifiyarsu akan kujera ta na ƙara kora musu jawabai, jawaban da ke daɗa fusata su anci mutuncin uwarsu.
Idon Labahani ne ya fara kaiwa kan Nazifi da ke tsaye bakin ƙofa yana kallon su Maimu, da sauri ya zunguri mahaifiyar tasu da sauran ƴan uwansa, da yake suna bala'in shakkarsa duk sai suka natsu Garzali na kiran sunan Maimu da yi musu alama.

Yaya ta miƙe tana faman galla masa harara da cewa,"Ka dawo kenan, to ban tafi ba ina nan mara kunya mara mutunci, wato akan mace yau idonka ya rufe ka manta wacece ni a wajenka ko".

Ko kallonta bai yi ba ya nufi hanyar sama, da sauri su Zuwaira suka matsa masa suna faɗin,"Baba Ƙarami sannu da zuwa".

Babu wanda ya saurara cikinsu ya haye, ya daɗe yana faman kiran Zahra'u akan ta zo ta buɗe masa ƙofa taƙi, sai can tunanin sa spare key ya zo masa. Ƙasa ya sakko ya shiga ɗakinsa, durowan kusa da gado ya buɗa yana bincika maƙullan, sai dai iyaka dubansa babu, kuma nan take Sa'ida ta faɗo masa a rai, saurin kawar da tunaninta yay ya koma wadrobe yana ci gaba da bincikawa nan ma duk babu.

Tsaye yay ya kama ƙugu, Allah ɗaya ya san irin girman ɓacin ran da ke tare da shi, har yanzu kuma ya rasa ma wanne mataki zai ɗauka akan Yaya da Ƴaƴanta.
_"Na'am Hubbi, Ohhh na canja musu wuri suna É—akinka na sama cikin durowan kusa da madubi"._

Rumtse ido yay gam tare da sauke ajiyar zuciya, bai san ta yanda aka yi maganar Sa'ida ta faɗo masa ba a halin yanzu. ya fito ya koma ɗakinsa na sama, yana buɗe durowan ya kwaso maƙullan dukka gidan yana ƙara tunawa da ranar ƙarshe da Sa'ida taje ƙauye ya kirata yana tambayar maƙulli.
Ko da ya buɗe ɗakin ya tarar da Zahra'u akan gado ta kifa kai da gwiwo, tura ƙofar yay ya ƙarasa gareta da sassarfa ya ɗauki Iman da ke kusa da ita, duban jikin yarinyar yake kamar wanda aka ce masa taji jiwo. Sai da ya tabbatar babu wani ƙwarzanan rauni a jikinta tukunna hankalinsa ya sassauto har yana sauke doguwar ajiyar zuciya.

Shifa a rayuwarsa ta yanzu yarinyar nan ce, idan da ita akwai shi idan babu ita to tabbas babu shi.
Ya kai hannunsa saman kafaɗar Zahra'u cikin kwantar da murya yace,"Kiyi haƙuri don Allah". Ture hannunsa tayi tana fashewa da sabon kukan munafurci. Nan fa kuma sai ya ruɗe ya shiga lallashinta yana ta aikin bata haƙuri har da sakkowa ya duƙa gabanta, ita kuwa faɗi take tana sake maimaita masa sai ta tafi gida.

"Na faɗa maka Daddyn Iman ba zan ƙara kwana ba ka sallame ni kawai, ba zan iya da wannan cin mutunci da wulaƙancin na ƴan uwanka ba, kowa ya raina ni basa gani na da girma, Yayyunka su min Ƙannenka su min yanzu kuma tsabar cin fuska har ta kai ga Ƴaƴansu ma, kuma kowa ya tashi buɗar baki sai ya yaɓa min magana yace ba don kana sona ka auro ni ba, ni matar shige ce kuma matar shige bata daraja, tsakani da Allah kayi min adalci kenan idan ka san da haka me yasa baka faɗa min ba na cirewa kaina soyayarka tun da wuri".

Tayi maganar tare da fashewa da kuka sosai a wannan karan kuma na gaske ne, ta goge hawayen tana kallonsa,"To ka bani takardata kawai tunda ka samu dalilin da yasa ka aure ni É—in, idan ya so sai kaje ka dawo da Uwar gidanka ka bata Æ´ar taka ni na yafe, Allah ya haÉ—a ni da mafi alkhairin...".

Saurin kai hannunsa yay bakinta ya rufe,"Haba Zahra'u, wai ke har akwai wanda zai faɗa miki cewa bana sonki ki yarda. Ke da kan ki ya kamata ki ƙaryata hakan ai, kin sani babu wanda na ke so bayan iyayena sama da ke da Iman, na sha faɗa miki zanen ƙaddara shi yasa na fara auran wata kafin ke, kuma ban san wata soyayya ba sai da na aure ki, in ace ni ke da kundin littafin rayuwata da babu wata mace da zan yi tarayya da ita in ba ke ba, ke ɗin nan kin fiya min kowa da komai, kar ki ƙara min zancen wacca muka rabu tarihinta ya riga ya shuɗe a wajena, ni ke kawai na ke kallo a matata ta farko kuma ta ƙarshe, Don Allah don Annabi na roƙe ki ki bar batun za ki tafi, in dai abin da suka miki ne zan ɗauka mataki akai ki bar ni da su, babu wanda ya isa ya taɓa min ke na ƙyale shi".

Kukanta taci gaba, ya hargitse duk ya gigice ya burkice, yafi tsawon awa guda yana famana lallashi kafin tayi shiru tace masa ta haƙura amma ya takawa Yayarsa burki. Ya shiga mata rantse rantsen zai ɗau mataki amma ta bar kukan idan ba haka ba zai sami wata natsuwa ba, shi kukan nata ne ke ɗaga hankalinsa.
Fita yay a ɗakin da Iman saɓe a kafaɗarsa, yana fita tayi wata dariya tana tafa hannu, ranta ƙal ta cimma target ɗin farko sai na gaba kuma, ai ta sha alwashin babu boka babu Malam sai ta raba Nazifi da kowa ya zama nata ita kaɗai, shi da duk wani abu da ya mallaka.

Yana sakkowa ya dubi Yaran Yaya da ke zaune a falo, waÉ—anda ganin nasa yasa suka fara rawar jiki suna raba idanu, ya dube su yace,"Wato a gidana ku ka zo kuna juye rashin tarbiyar da aka ba ku ko? Matata sa'arku ce don ubanku?".

Zuwaira ce tayi dakiyar cewa,"Baba Ƙarami ai ita ce ta fara cin mutuncin mahaifiyarmu, mu kuma babu wanda zai taɓa mana uwa mu ƙyale shi".

Tasss ya ɗauke fuskarta da mari. "Nayi ball da ke a wurin nan, ita Uwar taku idan ta kama girmanta har a tsinka shi? To wallahi duk wadda ta ƙara zuwar min gida tayi ɗiban albarka irin haka sai taga yanda zamu kwashe da ita, banzaye marasa ɗa'a, Kun fita kun bar min gida ko sai na juye muku dukka ɓacin raina".

Ya kalli mazan yace,"Minti ɗaya ku ka ƙara a cikin gidana sai dai yau ku kwana a bayan kanta, kuma ina mai tabbatar muku ba ku da me tsaya muku wajen karɓo ku".

Ɗaya bayan ɗaya suka yi gaggawan ficewa, matan kuma suka ɗauki mayafansu Maimu tayi saurin saɓa ɗanta a baya suka fice da hanzari ba tare da ko sun tsaya sallama da uwarsu ba.
Suna fita ya shiga É—akin Iyam, yana shiga suka yi karo da Yaya da ke niyyar fitowa don ta jiyo shi da yaran.

Kamar bai ganta ba don ko arziƙin gaisuwa bata samu ba a wajensa, ya zauna kan kujera murya ƙasa ƙasa dai kana ji kasan a ƴan ƙunci ake yace da ita,"Sannu da gida".

Itama da irin nasa yanayin ta amsa masa,"Yauwa, ka dawo kenan".

"Na dawo".
"To sannu, Allah yay albarka".

"Amin, Allah ƙara girma da lafiya". Sai kuma ya kalleta yace,"Amma Iyam kina da masaniyar fitinar da Yaya ta zo ta tayar min a cikin gida? Fisabilillahi abin da tayi ya dace a matsayinta na babba wacce take uwa a gare mu? Tsakani da Allah ina ita na yin faɗa da matata? Ko da sa'arta ce ai babu daraja sam tayi rigima da ita matsayinta na Yayar miji balle ma ba sa'arta ba ce, kin kusa yin ƴa da ita amma ki zauna ki kama dambe har kina faɗa mata maganganu irin na ƙananun yara marasa lissafi, to gaskiya ni banji daɗi ba, don wallahi tallahi ban da ita ɗin ce kafin zuwana na turo hukuma sun tafi da ita, to taci darajar wata darajar ne kawai, ko ba komai ciki ɗaya yafi gaban wasa. Amma duk da haka zan ɗauki mataki, domin ba zan zuba ido tana haddasa min fitina a cikin gida ba, kawai tun da bata son matata to kar ta ƙara zuwar min gida gaskiya, ta tsaya can iya gidanta idan gaisawa ne na ke zuwa muna yi, kuma ai ga waya idan ma wani abun take buƙata tayi min text don ko yawan kirana ma da take yi ya kamata ta barni haka, kuma ta fita a harkar iyalina ko kallo banza kar ta ƙara yi mata".

Ya maida kallonsa ga Yayar da ke kallonsa da sakakken baki cikin mamaki.
"Kuma Yaya yaranku kawai ki ɗauke su ki tafi da su, dama rashin haihuwa yasa na karɓe su kuma yanzu Allah ya azurtani da nawa, na samu matar da zata ke haifa min ƴaƴa don haka na gode da taimakonku da nuna kulawarku. Ba zan ce ban ji daɗi ba haka ba zan ce ba kuyi min adalci ba, kawai dai kije da su suci gaba da rayuwa a gabanku nima kuma sai na ji da nawa da Allah ya bani, In yaso kuɗin da kika karɓa a wurinta sai a bawa yaran".

"KuÉ—i kuma?, wanne kuÉ—i kenan?". Suka tambaya a tare ita da Iyam.

Ya kalli Iyam yace,"Da safe da zan fita na bawa Zahra'u dubu ɗari huɗu akan zata yiwa yaran nan siyayyar sabbin kaya da duk abubuwan buƙatunsu, don har uniform ma tace ya kamata a canja musu, to da ta zo wai sai ta ƙwace kuɗin har tana faɗin ai satar min kuɗin tayi. To tunda bata ganin irin ƙoƙarin da take yi akan ƴaƴansu da ni kaina ɗin da bana banbanta cewa bani na haife su ba, to su ɗauki yaransu kawai dama bani nace a bani ba, ra'ayin kansu ne. Kuma na rantse da Allah Iyam ban da darajar ke da Malam da kuke raye wallahi akan danganta min mata da ɓarauniya da tayi sai nayi ƙararta gaban alƙali, don sai ta faɗi lokacin da ta kamata tana ɗaukar min kuɗi, bana son ƙazafi na tsani mutum me yiwa wani ƙazafi, amma a hakan ma taje ita da Allah don ta ɓatawa iyalina suna, kuma idan ta sake tabbas zan datse alaƙar da ke tsakanimu".
Chapter 39 · 0% Book details