← Book details Ƙayar Ruwa 2&3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 23 OF 113

Sashe 23

Ƙayar Ruwa 2&3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

#TeamFitattuBiyar
[2/2, 07:47] Hlm: *B2ƘR12FT5*
Wuri na samar mana can gefe da su Fati muka zauna kan wata kujera. Zamanmu Rumana ta takura akan muci gaba a game É—in, ni kuma gaba É—aya raina a dagule yake, sai ji nayi Anty Aisha da su Basira na faÉ—in,"Yo dama juya ai bata da wani daraja a wurin miji".

Na ɗago ido na kalli ɓangaren da suke, ban san wacece ɗayar ba amma dai naga har da ƴan uwan Zahra'u su uku da na sani. Suka ɗora da maganar da Anty Aisha ta dire.
"To ai kinga ita yanzu duk wata dukiya da aka mallaka tata ce. Me haihuwa da mara haihuwa darajar ai ba ɗaya ba ne, ita fa me haihuwa gaje gida take yi, ta mallake miji da komai nasa, soyayyarsa ta zama tata gaba ɗaya, kuma a dangin miji za ki ga ita ce ƴar lele, kinga dai ita Zahra'un ai ko mutuwa yay ƴaƴanta sun mallaki komai ɗinsa, kuma ko a yanzu dai kinga ƙiri ƙiri ai ya na nuna yafi damuwa da ita akan uwar gidan".

Ni kam jin su kawai nake yi zuciyata nata min ba daÉ—i, A wannan lokacin na samu kaina cikin tsananin son haihuwa. Sai dai a gefe É—aya cike na ke da tsoron duniya da mamakin halin É—an adam, wato shi yana maraicin rashin Æ´aÆ´a, yanzun kuma da Allah ya ba shi amma har an fara maganar mutuwarsa da gadonsa, ba ma Æ´an uwan matar ba kawai har da nasa Æ´an uwan, lallai duniya.
Sai dare Nazifi yazo muka tafi, haihuwan da kwana uku aka sallamo su, cikin wannan kwanakin kam na aikatu, abincin safe rana dare duk nice, jama'ar Iyam a ƴan barka duk ni ke ɗawainiya da su. Ban taɓa nuna ɓacin rai ko gajiyawa ba, ni ina yi ne ma ina roƙon Allah da nima ya dube ni ya bani ko da ɗaya ne.

Sai bayan dawowan na su na samu ɗan sararawa hakan ma ban wani hutawa kawai dai aikin ya ragu, tun da suka dawo kuwa ban ɗauki yaran nan ba duk sona da na ɗauke su, tsakanina da su kallo ne daga nesa, ko kusa da su na tunkara Kakarsu ta ɗaga min murya, sau ɗaya ne ma na shiga ɓangaren Zahra'un sai ce tayi yanzu suka gama shan nono suka kwanta, kuma ba'a ɗaukarsu idan sun sha nono saboda tumbuɗi suke yi.
Kullum da anyi musu wanka ake miƙa su wurin Kakarsu, ita kuma ko Uban ne ya dawo sai tace ya ɗauke su iya nan ɗakinta kar yaje can wani waje da su a cutar mata da jikoki, to yanzuma in ya dawo har sai nayi bacci bai shigo ɗakin ba, abinci ma can ɗakin Iyam ɗin yace na ke ajiye masa, tun da ba ya rabuwa da yaran sai kusan sha biyu ƙarfe ɗaya yake kaiwa uwar su.

Ummani da Maman Yasmin da Anty Khairi suka zo barka, a wajenta kuwa an musu tarbar mutunci don wata Yayar Mamarta da Inna suka yi ta godiya da kayan barka, riguna ne set biyu sai turmin atamfa guda biyu amma kace akwatun kaya guda aka kai musu.
Da muka je wajen Iyam kuwa haka ta nuna tamkar bata san Ummani ba, kamar ba Iyam ɗin da shekara goma baya ba ta laƙabawa Ummani Ƙawata ƙawata, ta ɓata fuska tana faman amsa musu gaisuwarsu a wani daddaƙile kamar waɗanda suka zo neman taimako wurinta, sosai zuciyata ta sosu, na tabbata da ace jariran ma suna wurinta ba lallai ne ta basu ba, har wani cewa take da Fati tayi sauri ta kunna hayaƙi saboda masu zuwa ba'a san da irin manufar da suka zo ba, Maman Yasmin tsabar ɓacin rai sai da ta so ta gaggaya mata magana Ummani ta hanata.

Ranar suna kuwa wani shagalin taro aka haɗa zan iya rantsewa tsayin rayuwata ban taɓa ji anyi shi ba da dai sunan wai taron haihuwa, duk kuwa irin kuɗin masu kuɗi, duk irin tarukan sunan da nake jin labarin ana yi. Waterfall event center aka kama da naji ana batun miliyoyin kuɗi aka saka a iya kama wajen kawai ban da kuɗin abinci da sauransu, ni ban ma san da cewa ba'a gida za su yi taron ba sai da azahar na shiryo na fito naga suna tafiya, sai kuma ga Rumana tana ce min na bata sabon kaya wai za su tafi wurin suna.
Kuma sai da na shiga IG ne ma na ke ganin vedio har ya fara trending, abun ya ƙayatar da ni matuƙa da ke zuciyata babu baƙin ciki, ga shigar da aka yiwa yaran ma sha Allah kamar ka sace ka gudu, ni dai sai naji na ƙara jin sonsu a raina, jama'a a hall ɗin kuwa tamkar kaji an cika maƙil, shi da matar shigar kaya kala ɗaya suka yi, kowanne fuskarsa da annuri yana riƙe da ɗaya itama tana riƙe da ɗaya, shi ya saka shadda dakakkiya ita kuma ta sanya wani arnan less da shi ɗaya ya isa ɗaukan ido a wajen, ina kallon bidiyon ina murmushi ina hawaye.

Ina sama sai na sakko ƙasa saboda gidan ni kaɗai ce, sai da na sakko ne ma naga ashe su Marawiyya sun dawo, na samesu suna faɗin irin watsi da nerar da uban ya dinƙa yiwa yaran da uwarsu, kyauta kuwa da aka dinga bawa yaran ba'a magana, shi kansa sai da ya bada atamfofin chiganvy aka rarraba. Har yaywa mahaifiyar yaran kyautar mota dalleliya. Haka kawai naji ba zan iya ci gaba da zama ina jin labarin na su ba, na wuce ɗakina na ƙasa ina jin kamar ina so nayi kuka, ina shiga na kashe wayata kawai na kwanta ina ta tasbihi cikin raina saboda kawar da abin da shaiɗan ke neman dasa min.

Basu fara dawowa ba sai bayan isha'i, lokaci É—aya gidan ya kacame da hayaniya.
suna kan hanyar dawowa ya kira ni yace na shirya zamu je akaiwa Malam yaran, nace masa to. Bai ma shigo gidan ba ya turo aka kira ni, na isa motar na sameta hakimce a gaba, sai naga ai cin fuska ne ace ni na zauna a baya, don haka na tsaya daga bakin motar har ya dawo daga sallamar wasu ƴan ƙauyensu, Iyam ta aiko masa a basu kuɗin mota.

Ya dube ni yana hararata yace,"Ba ki je wurin suna ba motar ma ba za ki shiga ba?".

Nayi guntun murmushi na ce,"Ina da muhimmancin da za'a ce naje suna ne? Ko ina da arziƙin da za'a faɗa min abin da aka shirya? Rashin zuwan nawa ai bai hana kun yi yanda kuke so ba. Ita kuma kayi mata magana ta dawo baya".

Ganin zai ɗaga min murya yaci mutuncina gabanta gaban mutanen unguwa na ɗaga masa hannu kawai na buɗe bayan na shiga. Da muka je gidansu ashe can mutanen ƴan uwan Iyam gayya guda ta gayyato, Ah to kuwa Nazifi ya shekara goma da aure bai haihu ba ai dole ayi shagali ban ga laifin su ba. Ni na ɗauki Noor me sunan Iyam da ubanta ya miƙo min ita da muka shigo, Iman ɗin kuma tana hannunta, abin sha'awa idan ka kallemu sai naji inama ace kanmu haɗe yake kamar ya da ƙanwa. Wurin Gwaggoje muka fara shiga muka gaida ita, sannan muka je ɗakin Amarya kai matar nan da mutunci yana yawa zancen kirkinta yay yawa. Ummaa kuwa dama a falo muka sameta ita ce ma taje ta isawar da Malam cewa mun zo, da ke ita ke da girki, ni tun da na gaida itama bata ƙara bi ta kaina ba sai karɓar Noor ɗin tayi tana cewa ga yanda ake ɗaukar yaro hakan da nayi ai sai wuyan yarinyar yay ciwo, kuji haɗin masifa don Allah.

Ana haka kuwa Yayan Shago ya iso wurin, cikin barkwancin nan nasa da zolaya yake cewa Hassana da Hussaina matan Alhaji Ƙarami uwayen Hassana da Hussaina. Ni dai murmushi na ke muka gaisa da shi, ita kuwa ta haɗe rai da ƙyar ma suka gaisa. Bata san shi ɗan ba ruwansa ba ne yana tsokanarta ya ce,"Amma dai Amarya kin bawa Yayar taki ɗaya ko?".

Kanta a gefe tana ƙara haɗe gira sama da ƙasa tace,"Wace Yayar tawa? Kuma akan me zan ba da abin da ba'a tayani naƙuda ba, ita ma macece ai ta haifi nata mana".

Da yake shi ba baƙon zafi ba ne yay ƴar dariya yana ce mata,"Maida wuƙar Amarya, Allah ya raya mana sai an kawo min kwanon nama na".

Yana barin waje na ce da ita,"Kiyi haƙuri fa shi haka yake da wasa".

Bata tanka min ba sai faman kallon ƴarta da ke hannuna take. Sosai Malam yayi murnar ganin yaran, ya tofe su da adu'oi kafin ya miƙo mana su, bayan mun gama gaisawa ne sai muka ji ya fara faɗa, ya tasa Nazifi a gaba kamar zai cinye shi ɗanye, wallahi ni ban taɓa tsammanin ba zai yi masa mugun duka ba, dama shi mutum ne me zafi, Ƴaƴan duk tsoronsa suke yi, bana mantawa da ko hira ake aka ji sallamarsa sai kowa yay ɗif, gyaran muryar Malam kawai zaa ji a natsu, shi kansa Nazifin tun kan aurenmu yasha faɗa min da ka aikata laifi Malam ya sani gwara baka ma fara aikatawa ba, ga fadansa ba ya wucewa.

Kuma yana da sakin jiki da Æ´aÆ´ansa kawai dai yana da faÉ—a. Ni Iyam ce dai da ta fanÉ—are masa yanzu, amma ko ita da ai mugun tsoronsa take ji, kuma duk rashin lafiyar nan da yay ne yay sanyi dan ni dai nayi mamaki ace Malam ya iya barinta zama a gidanmu.
Haka yay ta faÉ—a jikina har rawa yake, yana cewa ashe zaluncin da ya ke bugawa a cikin gidansa babba ne, to an same shi an zayyana masa from A-Z.

Yana nuna shi yace,"To Nazifi idan shiryawa tashi ranar ƙiyama da shanyewar ɓarin jiki kayi to kaci gaba da duk abubuwan da kake yiwa matarka. Ita kuma uwar taka da taje can ta tare ta zama fitina a tare da ku, zata zo har inda na ke ta same ni, wallahi Nazifi ka sani sai na mugun saɓawa mahaifiyarka, ka dai san sarai waye ni".
Chapter 23 · 0% Book details