Sashe 52
Ƙayar Ruwa 2&3 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Iska ya furzar me zafi daga bakinsa ya sauka akan gadon, wadrobe ya buɗe ya shiga kwaso tsaffin kayansa da zai bayar, wadrobe ɗin duk tayi kaca kaca sai tashin tsamin jiki da na turare da ya haɗe wuri ɗaya, ya girgiza kana saboda takaici da ya maƙure shi, ko da wasa Sa'ida bata taɓa haɗa kayan da ya cire da wankakku, kuma idan kaya sun isa a ɗauka a bayar da kanta zata ɗauko tace Hubbi wannan sun isa a bayar kafin su ƙarasa mutuwa, amma zai iya cewa bai taɓa ganin hannun Zahra'u a cikin wadrobe ɗinsa ba da sunan gyara masa kaya ko ɗakkowa tun bayan da ta gama na marmarin amarci.
Yana cikin haÉ—a kayan ne kuma ya tuna da kiran Lubabatu da zai yi, cikin hanzari ya ajiye kayan hannunsa ya É—auko wayarsa ya kirata, ya sanar mata cewa zai tura mata dubu huÉ—u tayi sauri ta siyo kifi tayi ferfesunsa ta kai asibiti.
Gama wayar tasu yay daidai da shigowan Zahra'u, yanda ta shigo fuska a haɗe shima kuma ya haɗe tasa fuskar zaka san ba a shiri da juna an samu saɓani. Ta zauna kan kujera tana kallonsa tace,"Wai yanzu da gaske ka ke ba zanje bikin nan ba?".
Tayi maganar tana girgiza ƙafafu haka kuma tana faman jijjiga kai alamun dai ranta a matuƙar bace yake, sannan ta shiryawa rigimar da duk ya taka.
Bai ko kalleta ba balle ta saka ran zai amsa, ya sunkuya ya ɗauki Iman da ta fara rarrafawa can zata tafi yo ta'adi, wasa ya shiga yi mata, ba zai taɓa iya musalta yanda yake matuƙar kaunar ƴarsa ba, yana son fiye da kowa da komai nasa, irin son da bai haɗa shi da komai ba, haka yana matuƙar godiya ga Allah da ya ba shi ita ya ke kuma kan ƙara basa wasu.
"Daddyn Iman magana fa na ke maka kayi banza kamar baka jini ba".
Ido ya É—aga ya kalleta, sai yay murmushin da shi É—aya yaji sautin kayansa kana yace,"Sai na rubuta a takarda na bi ko'ina a cikin gidan nan na manna tukunna za ki gane abin da na ke nufi kenan".
Sai kawai ta fashe da kuka kamar ƙaramar yarinya, kuka sosai irin na cin rai. "Me yasa za ka zaɓi hakan a matsayin hanyar ƙuntata mini, ko laifi na maka ai bai kamata ka huce akan hakan ba".
Barin Iman yay ya miƙe ya yana tuɓe jallabiyarsa, bai da lokacin biye mata shikam, ya fi gane ya mayar da ita mahaukaciya tayi ta zuba a duk san da irin hakan ta motsa.
faɗa suke yi sama da watanni, dama tuni yana ta fushi da ita yana jin haushinta akan nuna rashin sanin darajar iyayensa da muhimmancin su, kwata kwata bata nuna damuwarta da kulawarta akan rashin lafiyar mahaifiyarsa, ta mayar da shi wani ɗan iska sauna sai dai ta shirya tayi fitarta aiki, haka idan zuwa anguwa ne ya kama tana kan gaba wajen fita, amma ko da sau ɗaya bata taɓa dubansa ba tace zata je asibiti wajen Iyam, haka ko da tursasata yayi akan su tafi ranar sai sun yi tashin hankali tun daga kan tafiya zuwa dawowa.
Ga shi yana buƙatar kuɗi ƙememe taƙi ta ba shi wani abu a cikin kuɗaɗen da ya riga ya mallakawa su Iman tun kafin haihuwarsu, a cewarta yanzu ai ba nasa ba ne ko auro ba zata ba shi ba balle yay iko da su ganin yana ubansu.
Sannan ta zo ta Yaye Iman yarinyar na da wata goma wai ta gaji da bata nono ita ba zata bari nonota ya zube ba, ya rabu da ita a wannan ganin yarinyar bata kuka kuma tana shan madarar da aka basu a asibiti sosai da zai kama cikin yaro.
Kuma kwatsam bayan nan saboda bata da hankali tana batun zubar masa da cikin da Allah ya ƙara basa tana faɗin ita ba zata iya haihuwar kwanika ba, bata shirya mata ba, ya za'ai ƴarta ko wata goma sha biyar bata yi ba ace ta samu wani cikin, ba hauka take ba yanda ta tsara sai bayan shekara bakwai kafin ta sake samun wata haihuwar, bata yi aure don ta saki jiki tayi ta zuba ƴaƴa ba kamar wata kaza, don haka ko me zai yi sai ta zubar da cikin.
Wata huɗu kenan suna ta fama da shi, yace wallahi muddin ta zubar masa da ciki sai sun yi shari'a kuma sai ya saketa kuma ba zai bata Iman ba, to wannan furucin da yay shi ne ta ɗan sassauto amma ba wai don ta haƙura ba, tana nan akan bakanta na sai ta zubar da cikin.
Shi ne kuwa ya tattarata gaba ɗaya da duk huruminta ya aje a gefe, ko abincinta ya daina ci, magana ya daina yi mata, ko abubuwan da yake siyowa ya aje cikin gidan duk ya daina, shimfiɗa ma ban da kar ya cuci kansa sai ya ƙaurace mata gaba ɗaya don so yake ya horata ta horu.
Kuma sai Allah ya kawo masa hanyar da zai rama ɗin, za'ai bikin Ƙanwarta da suke uwa ɗaya uba ɗaya daga ita sai ita, Mahaifiyarta ma zata je saudiya duk ya hana yace ba zata je ba, ya kuma rantse da hakan, shi ne ta kira mahaifinta ta kai masa ƙara, shi kuma ya kira Nazifin ya dinƙa zazzaga masa bala'i yana cewa kar fa ya zaƙe da yawa, ya daina ganin don ya isa ne ko ya kai ya ɗauki ƴarsa ya ba shi, alfarma yay masa saboda haka in yace zai zaɓi cuzgunawa ƴarsa to tabbas zai ji sammaci.
Tun da mahaifinta ke shiga huruminsu yay bake bake akai bai taɓa buɗe baki ya maida masa martani ba, idan aka cire mahaifiyarta kowa a familyn na su taka shi yake son ransa musamman ma mahaifin nata, shi har yana faɗa masa banda ƙaddara ma dai ai bai cancanci ya ɗauki ƴarsa ya bawa mara ilimin boko ita ba, wanda ko rubutun kirki bai gama iya ba, ranar kuwa ya kada baki ya maida masa martanin cewa ilimin addini shi ke gaba da na bokon da suke alfahari da tutiya akai, kuma Alhamdulillahi ya samu ko yanzu ƙiyama ta tashi, ko yanzu zai kwanta ƙabari lafiya tun da bai fifita duniya akan lahirarsa ba.
Da wannan su kai ta fafatawa da mahaifin Zahra'un wanda ta kai har yace to shikenan zai É—auke Æ´arsa, shi kuma yace to in har ta fita daga gidansa a bakin aurenta, haka kuma yaywa Æ´arsa kashedi tare da jan kunne kar tayi kuskuren zubar masa da ciki idan ba haka ba za su yi shari'a da ita, shari'a irin ta gani kashe ni.
Zahra'u ta sassauta murya tana dubansa tace,"Daddyn Iman kawa girman Allah da manzonsa kayi haƙuri idan laifi na maka, amma don Allah kar kace zaka hana ni zuwa bikin gidanmu ka taimaka min".
Ya isa gaban madubi yana ɗaukan clipper yace,"Ashe shugabar sanin right ta iya bada haƙuri".
Ta rufe ido ta buɗe. "Ni dai ko me zaka kace ka faɗa amma kayi haƙuri ka bar ni naje, ni wallahi na yarda idan naje na dawo ka ware watanni ka hana ni zuwa ko'ina bayan aikina".
Yay wani murmushi kafin yace,"Aikin ma ai kina gab da daina zuwansa, ai yanda kika zaɓi ki baƙanta min haka nima na dinƙi ƙuntata miki kenan, da ni kike zancen wallahi muddin ni ke aurenki sai kin shekara guda ba ki je gidanku ba, za ki sha mamakina".
Aikuwa sai ta miƙe ta baɗawa idonta ƙasa ta kama tafa hannu cikin masifa tana faɗin,"Ƙaryarka tasha ƙarya Nazifi, baka isa ka hana ni zuwa gidanmu ba, baka isa ka raba ni da aikina ba, ka yi kaɗan, idan kuwa kace hakan za'ai nima zaka sha mamakina wallahi wannan cikin na jikina sai na zubar da shi, ba kuma shi kaɗai ba kowanne ciki naka da zan samu sai na zubar da shi kaji ma na faɗa maka".
"To ki ta zubarwa mana, wa kika yiwa in ba kan ki ba, ke ce za ki ƙare a wahala kina shan magani yana lalata miki mahaifa ƙarshe ki zo ki daina ɗaukar cikin, ni kuma daga nan na danƙaro wata matar".
Wani kukan kura tayi tayo kansa zata cakumi kwalarsa tana faman hargagin cewa,"Na rantse da Allah baka isa ka ƙaro aure ba, ni ɗaya zan ci gaba da zama da kai, kuma kayi gangancin hakan ka gani ko wacece sai na kasheta sai naga bayanku kai da ita, kuma ban ga uban da zai hana ni zubar da cikin nan ba ko me za'a yi".
Tana gama maganar ta fita kamar zararra, in few minutes sai gata ta dawo da goran wani magani na hausa da kuma ƙwaya a hannunta, zuba mata ido yay yana kallonta ya kasa hanata har ta ɗiɗɗiki maganin.
Jarkan faro guda sai da ta shanye kana ta sauke sai sauke numfarfashi take yi,"Na sha kuma zai zube, na kashe É—an naka kayi duk abin da zaka yi....".
Cikin tsananin ɓacin rai da ƙunar zuciya yay kanta yana ɗaukar sachet ɗin maganin ya duba, take ya daga waya ya roƙi wani likita da cewa ya hau whatsapp yay masa wani taimako, ya ɗauki hoton maganin ya turawa likitan kai tsaye yace masa ai maganin zubar da ciki ne.
Lokaci guda gashin jikinsa ya mimmiƙe, gumi ya keto masa, abun da ya ƙwallafa rai a kai ta zubar masa? Ɗansa na halal ɗan sunnah ba ɗan shege ba?
Zuciya ta É—ebe shi ta kai shi ga nufar wadrobe ya buÉ—e tare da zaro belt É—in wandonsa.
Zahra'u da ke faman zazzaga masifa tana yayi abin da yake tunanin zai yi ba tayi aune ba ya shiga lafta mata belt É—in ta ko'ina tamkar an aiko shi.