Sashe 66
Ƙayar Ruwa 2&3 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Ta ajiya masa ta ɗauko ruwa ta aje masa, shi kuma yana ta saka mata albarka don shi kansa kaf matan ƴaƴansa yafi son Ummani, a ko da yaushe yabonta yake yi domin ita ɗin macece ta ƙwarai, yanda take masa tamkar shi ya haifeta.
Yashaik ya shigo gidan, a nan tabarmar da Kaka yake ya zauna suna gaisawa, kafin daga bisani ya miƙe ya shiga ciki wurin mahaifiyarsa.
Samunta yay ta fito da kayan sif É—inta dukka tana linkewa, daga gefe ya zauna yan agaishe da ita ta amsa tana tambayarsa ya iyali.
"Me makon ki aika a kira miki Maman Yasmin, yanzu ina ke ina aikin ninkin kaya masu yawa haka".
"Ku dai kun fi so kuyi ta gani na kwance sharaf wuri É—aya bana aikin komai, haka kawai kuma yarinya na can gidanta tana aikinta sai na aika a tasota, a'a kayan nawa suke gaba É—aya yanzu zan gama ai. Yau babu in da kaje kenan?".
Ya sauke numfashi yace,"Ban leƙa ko ina ba, gani nayi gwara in ke hutawa lahadin jiki na buƙatar hutu".
"Haka ne, Allah daÉ—a rufa asiri. Jiya naji ka ce zaku yi magana da Abbaan ku sai ban ga ka dawo ba shiru, ba dai wata matsalar ba ce ko?".
Ya kai hannu yana shiga tayata linkin kayan yace,"Da na ƙyale ne kawai saboda na san ko naje masa da zancen ba karɓa zai yi ba, wataƙila ma raina ya iya ɓaci, sai dai ko ke za ki faɗa masa".
Ummani ta mayar da hankalinta kansa sosai tace,"Menene fa?".
Yace,"Ba fa matsala ba ce". Ya faÉ—a yanda yaga mahaifiyar tasa ta kafe shi da idanu.
"Dama akan Sa'ida ne ban san me Abbaa ke hange ba da yaƙi bawa zaurawan nata dama, haka kuma gaba ɗaya bai son zancen auren nata ba, amma ni gani na ke bai kamata a biye mata ba, duk da cewar dole auren ya sire mata, amma ai ba zamu ɗauka cewa lallai abin da ya faru a farko shi zai kuma faruwa ba ko kuma yayta maimaituwa, kawai ta ɗauka hakan matsayin jarabawarta ba wai saboda dalilin hakan kuma tace ita ba zata ƙara yin wani auren ba. ita macece ko ai na take ko me take yi duk matsayin da take da shi da aurenta tafi daraja a idon duniya, kuma ku kan ku idan da aurenta hankalinki zai fi kwanciya, kuma sannan shekaru tafiya suke ta yi gaba ba dawo baya zasu yi ba, nan da wata shekarar magana ake ta zata shekara talatin idan da rai da kuma lafiya, to ta gama karatun ta samu aikin yi me za'a ƙara jira Ummani? Baka biyewa maganar mutane balle ta dameka amma ana gudun baki, wani bakin kaifi ne sune masu kambun baka, ni gaskiya na fi ga sha'awar tayi aurenta, ba duka aka taru aka zama ɗaya ba ta dage da adu'a kawai Allah kar ya maimaita mata irin mijin baya".
Ummani ta numfasa tace,"Ni kaina da ka ganni wlh yanzu hankalina yafi ga tayi auren, Sa'id idan ta fita aikin wannan wallahi sam sam bana samun natsuwa har taje ta dawo hankalina ba'a kwance yake ba, amma lokaci ne duk dai Abbaan naku na daƙile damar hakan, Allah dai ya kawo mata na gari ya musanya mata da mafificin alkhairi".
"To amin ya Allah. Kuma dama Nura ne yay min magana É—azu da safe yace abokinsa Ya ganta yace idan ba'a tsayar da maganar wani akanta ba ya gani yana so".
Ummani tayi murmushi me faÉ—i tace,"Allah sarki, ai na yake to?".
"A can garejin ma su yake shima, kin sansa ma sai dai ba za ki gane shi ba, amma da sallah ƙarama tare suka zo da Nuran ai".
Tace,"To madallah, ai ina ga sai kace masa ya tunkari Abbaan na ku da maganar ko, ya gwada tasa sa'ar ko a kansa dacen yake".
"Ehh to dama ni abin da ma yasa ban masa maganar so na ke na fara bugar cikinta naji ko tana da ra'ayin auren me Æ´aÆ´a".
Ummani tayi gajeriyar dariya tace,"To ita wanne zaɓin saurayi ne da ita yanzu, sai dai kuma wani lamarin na Allah, fatan dai Allah bata wanda yafi wancan".
Da haka suka ci gaba da hirarsu akan maganar Al'amin ma da za'a kai kuɗin aure cikin satin nan, har sai da suka ninke kayan dukka. Shi ya share mata ɗaki ya goge ko ina, yay mata sharar tsakar gida da kitchen suma duk sai da yay mopping, dama sun saba hakan shi da Imam duk sanda suka sameta tana aiki, don shi da yake kusa da suma da sassafe yake zuwa yay sharar soro da ƙofar gida.
Bayan tafiyarsa yana zuwa gida kuwa ya aiko mata Yasmin wadda ta shigo tana ta ƙunci wai Kawu yace ta zo tayi wanke wanke.
Da yamma yaro ya shigo tsakar gida yana ta doka sallama babu wanda ya amsa, Ummani na daga cikin ɗaki a kwance kamar a mafarki taji sallaman wajen ƙofan ɗakinta, tayi saurin tashi tana cewa,"waye ne?".
Yaron yace,"Ai ko ni aka yi, wai ana sallama da me gidan".
Labule ta ɗaga ta leƙo tana cewa da shi,"To masu gidan ai da yawa, kaje kace wa ake nema?".
Ba jimawa ya dawo yana cewa,"Wai Malam Salman".
Ummani tace,"Tooo wallahi ba ya nan, amma kace musu yana kan hanyarsa ta dawowa ko zasu jira shi, suna da yawa ne?".
Yaron yace,"Ehh mota biyu ce har da sojoji".
Gaban Ummani ya yanke ya faɗi ya bada rasss, tayi saurin dafe ƙirji tana faɗin,"Sojoji kuma ɗan nan? An ya ba makuwa ka yi ba kuwa, ko can ɗaya gidan aka aika ka kusa da me kayan miya".
Yace,"A'a ni dai nan suka ce min".
"To shikenan je ka kace musu bai dawo daga kasuwa ba sai dare".
Yaron ya juya ya fita ita kuma ta dawo cikin É—aki, ta kasa zaune tayi tsaye tana tunanin lafiya? Me zai kawo sojoji neman Abbaan su? Sai tayi maza ta É—auki wayarta ta yiwa Sa'ida flashing, Sa'ida ta biyo bayan kiran, ta É—aga tana ce mata,"Ke sako min kati zan kira Abban ku".
Yanayin fitar muryan nata yasa Sa'ida cewa"Lafiya Ummani?".
"Lafiya lau sauri sako min zan ba shi sallahu ne a kasuwa kar ya riga ya taho".
Within one minutes sai ga shigowan katin ɗari biyar a wayar, ta lalubo sunan Abbaan Sa'id ta kira. Abbaa a lokacin na bakin titi ya ɗaga kiran wanda hayaniyar ƙarar ababen hawa bai barin sa yaji me take cewa itama ɗin kuma bata jinsa sosai, haka tayi ta faman kira ƙarshe sai haƙura tayi, ta fito tsakar gida ta zauna tayi jugum, har sai da ta leƙa ƙofar gidan taga tabbacin maganar yaron, soja ɗaya na tsaye bakin mota da bindiga a hannu, wannan fa yasa ta daɗa tsurewa ta kama safa da marwa a tsakar gida tana ta faɗin Allah sa lafiya.
Bayan kusan rabin awa sai ga Abbaa ya shigo gidan a gaggauce yana ƙwala kiran,"Sa'a! Sa'a! miƙo min babbar tabarma maza maza".
Irin yanda yake ƙwala kiran bana lafiya ba, Ummani ta fito daga ɗaki fuskar hijabi a juye jiki duk sai ɓari yake yi, ganin yanda Abbaan yake shima da ruɗani ta tsaya tambayan,"Abbaa lafiya? Kaga baƙin ƙofar gidan ne kaima?".
Bai amsa mata ba yaci gaba da ɗauraye ƙafarsa da duk tayi ƙura tare da wanke fuskarsa ma. "Ni dai sauri miƙo min tabarmar tukunna, ni kaina ba na ce miki lafiya ko ba lafiya ba Sa'a, amma hankalina duk ya tashi".
"Abbaa to kaje wurin su kuwa? Ko na aika a kira Yashaik yau yana gida bai fita ba".
"A'a ƙyale su Sa'a, bara na fara jin me ke tafe da su sun ce sun jima waje, maza miƙo min tabarmar dai, kin san irin mutanen ba'a barin su da jira".
Ganin ta tsaya kawai ya wuceta yay ɗakinsa ya buɗe ya yayibo tabarma ya fito yay waje da hanzari, duk ya rikice tafiyar tamkar zai kifa ƙasa. A soro ya baza ƙatuwar tabarmar, takalamansa ma a baibai ya saka ya leƙa yana ce musu,"Bismillah ku shigo daga ciki".
Zatonsa iyaka waɗannan sojoji biyun na waje ne sai yaga an buɗe mota manyan mutane dattawan arziƙi suna fitowa, da kallo ɗaya ba sai ka ƙara na biyu zaka shaida duniya ta san su ta san da zaman su, matsayi kuma an same shi sai wanda ake kan rabawa, kuma masu faɗa ne aji a ƙasar da suke ciki.
Sojojin na basu kariya har suka shigo soron wanda duk Abbaa ya daɗa hargitsewa yana duban tabarmar da duk ta ɗan sha jiki, da shi kansa soron gidan wanda yake ganin sun girmi su ko rakuɓe a cikinsa balle zama.
Sai dai ga mamakinsa babu wani yanayi na ƙyama ko jin kai a tare da su, duk sai yake jin wani iri, bai taɓa yin baƙo yana jin ya ƙasƙantar da shi duba da irin muhallinsa ba sai waɗannan mutanen.
"To ko kujera za a samo muku?".
ÆŠaya daga cikin su yace,"A'a babu komai Malam, ai nan É—in ma Alhamdulillahi ya isa, ga shi duk mun zauna, muna godiya da karramawa".
Sai da duk suka gama zama sannan ya zauna yana mai fuskantarsu, ya ranƙwafa kamar bafaden sarki, da firgicin da ke tare da shi ya shiga miƙa musu hannu wanda a farko sai da yaji shakkar hakan, sai kuma yaga saɓanin fa yanda yake tunaninsu ne domin da kansu suka miƙo masa nasu suna gaisawa da girmama junansu da kuma mutuntawa.
Cikin wani yanayi Abbaa da bai taɓa shigansa ba yake kallon tsohon mutumin da ke cewa da shi,"Da ka natsu naga duk ka dabarbarce da ganin namu".
Abbaa yace,"To ai ranka ya daÉ—e ganin mutane irinku dole mutum ya shiga irin wannan yanayin na ruÉ—ani, ni dai fatana Allah yasa lafiya, Allah yasa lafiya don cikin gida ma kanta iyalina a tsaye take".
Alhaji Sama'ila ya murmusa yana duban Abbaa da kyau yace,"Kar ka samu damuwa lafiya lau, Alkhairi ne ya kawo mu gare ka, saboda haka ka bar tunanin ko ba lafiya ba ne".
Sai sannan Abbaan ya samu ya ɗan sauke ajiyar zuciya ta salama yace,"To masha Allahu, bara a miƙo muku ruwa".