Sashe 79
Ƙayar Ruwa 2&3 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Ai ban ida rufe baki ba ya sauke min mintsine a weast ɗina. "Ya sunana?". Dariya na ƙyalƙyale da ita dalilin cakulkulin da ya sakar min, na manne jikin bango ina cewa,"Salim sunanka". Ganin yana neman yi min rumfa na rumtse ido da kyau ina marairaice murya da cewa,"Kayi haƙuri ba sunanka haka ba, sunanka Lieutenant Onochie, kuma fa kaga kar wani ya zo wucewa".
"Ina ruwana ke za ki ji kunya ai, ni dama a ƙage na ke a bani abata na tafi, dama hotel ɗin da muka sauka idan za ki kwana kina ihu babu me kawo miki agaji".
[2/2, 07:47] Hlm: *B3ƘR06FT5*
Agogo ya kaɗa ƙarfe biyu, na miƙe ina tattara takardu na saka cikin file ɗin da ke aje kan ɗan ƙaramin table ɗin cikin nursing station ɗin namu. Na saka wayata cikin aljihun rigata na uniform tare da cire after dress ɗin da ke jikina na saƙale ta jikin hanger, in ka dubeni gwanin ban sha'awa, kayan na mini kyau tun balle da kullum na ke wani ƙara yin fresh da ni, wanda bai sanni ba ma sai yace ƴar Daddy ce, hankali da natsuwa sun wadatu babu wata makusa a tare da ni, a ganni a kushe sai maƙiyi, don ko daga aiki na dawo da uniform ban ɗora hijabi ko after dress akai ba, ƴan anguwa an dinƙi bina da kallo kenan me cike da burgewa, masu gulma suyi masu adu'a su yi, to surutun ma bai damuna tunda dai ina da iyaye a raye nima kuma ban yar da adu'a ba.
Na isa gaban firij na buɗe na ɗakko allurai a ciki. Ina jin Sister Maryam na faɗin,"Wai ni na rasa irin Sister Sa'ida, ki ta gume baki ba za kike magana ba, daga murmushi sai uhmm da ummm haba kamar kina jin haushin zama cikin mu, in haka ne to ayi maki office ɗinki mana don naga kina da ƙafa a asibitin".
Na waigo ina murmushi da cewa,"Allah ba don ko wulaƙanci ba ki daina faɗin haka Sister Maryam, ni kawai magana ce bata dame ni ba, kinga ko zaman nan da muke ku yi ta hira ana hayaniya wallahi hawar min kai take yi, kowa kin san da yanda nature ɗinsa yake, ni na kasa sabawa surutu har yanzu ko a gidanmu haka na ke".
Ta taɓe baki tana cewa,"Tab ai kuwa dai to ba hali ba ne wannan ɗabi'ar girman kai ce, ka yi magana kace zaka faɗi gaskiya ne aji haushinka".
Ban ƙara tankawa maganarta ba, gudun kar mu zo muyi rigima, rigima ba halina ba ce, haka Ummani ma tana cewa da ni kar na taɓa biyewa kowa muyi rigima. To ni ban san dalilin da yasa take jin haushina ba, har ga Allah ta takura min, babu siɗi ba saɗaɗa ta ke ƴar tsama da ni, amma ina ga don ina kama kaina ne ban shiga sabgar kowa, ba zaka ji ana gulmace gulmace ko munafurcin wani da ni ba, hira ma idan ana yi jefi jefi zaka ji na saka baki, ko kuma don fifita yabona da Dr yake yawan yi akansu ne oho, da su kansu mutane idan suka zo asibitin, haka ko a cikin ma'aikata asibitin kowa ya tashi kaji yace Sa'ida Sa'ida, ta dai ga Allah yay min ɗaukaka hakan sai ya tsaya mata a rai, don ita ko da yaushe cikin sukana take yi, tayi ta faman habaici akan ina da girman kai tana gaggaya min magana mara daɗi, ko kyauta aka bani a asibitin bata iya ɓoye baƙin cikinta ƙarara take fitowa ta nuna, ni kuwa bana taɓa nuna mata na san ma tana yi, idan tayi wani abun ne Khadija da Maman Nana ke shigar min su caccaketa, sai sun gama da ita su dawo kaina suyi ta zazzaga min masifa akan rashin baki, ya kamata in koyi maida martani idan anyi min, haka kuma in daina barin ko ta kwana, ni dai to kawai na ke ce musu, me zan ce wanda ya wuci hakan? Na riƙe adu'a na riƙi azkar don haka na sha gaban kowanne mutum babu faɗa balle tashin hankali.
Ina ƙara kallon agogon hannuna nace,"Maman Nana bari na je duba waccan patient ɗin".
"Wadda tayi miscarrage É—in nan?".
Nace,"Ehh ita".
"Oak tom sai kin dawo".
Na fita a ɗakin cikin hanzari don ko kusa bana son yin latti wajen kula da majinyacin da ke ƙarƙashin kulawata. Na tura ƙofar ɗakin na shiga da sallamata, muka gaisa da patient relatives, suna girmama ni kamar yanda nima na ke girmama su, ga yabona da suke yi wanda har Dr sai da suka faɗawa irin ƙoƙarin da na ke yi akansu, har da cewa na iya mu'amala da mutane, mijin matar kuwa kusan ko da yaushe sai yay min ihsani saboda jin daɗin yanda na ke kula da iyalinsa cikin sauƙin kai.
Wadda ke zaune gefen gadon kusa da mara lafiyar tayi saurin tashi daga wajen, Na aje file ɗin hannuna bisa loka na isa gaban mara lafiyar wanda yay daidai da ƙarewar drip ɗin da ke shiga jikinta.
Ta buɗe idanuwa a lokacin tana kallona, na mata murmushi na ce,"Sannu, ya sauƙin jikin?".
A hankali tace,"Da sauƙi, sannu da ɗawainiyarki na gode".
Na amsa da faÉ—in,"Aikina ne ai, Allah ya ba ki lafiya".
Cikin sanin makamar aikina da ƙwarewa na cire drip da ke jikinta tare da mata alluran da za'a yi a lokacin, bayan duk na gama kana na ke tambayarta ya take jin yanayin jikin nata duk ta min bayani.
Na dubi ɗaya daga cikin ƴan uwan nata wacca ke tsaye daga bakin gadon, ni dariya ma ta so bani don kamar a tsorace take, ganin cewa dukka ƴan boko ne cikin ƙwarewar harshen turanci idona cikin ƙwayar idonta na ce,"Kun bata drugs ɗin ta?".
Kamar bata gane me na ke nufi ba ne sai ta tsaya lakato kamar wadda ta samu kallo kallo, ta ɗan ban haushi na canja fuska ina mayar da dubana zuwa ga ɗayar wacca ta taso tana cewa,"Wallahi na sha'afa kin ce ƙarfe biyu za'a bata, kuma yau ɗin kawai aka yi kuskuren hakan".
Faɗa na kama musu akan sakacin da suka yi na rashin bada maganin akan lokaci, kafin daga bisani na nusar da su muhimmancin bayarwar akan kari. Muna haka Sister Badiyya ta shigo, ai fa sai ta amshe ganin ina magana a sanyaye wai da sunan faɗa na ke yi, tunda ta fara musu faɗan suka shiga bata haƙuri saɓanin ni da shiru kawai suka yi sai wata dattijuwa ce ma tace za'a kiyaye gaba.
"Yanzu sai wani abu ya faru da ita ba fata ake ba ku janyo mana ace rashin iya aikinmu ne".
Dattijuwar ta taso daga inda take tana cewa,"Ayi haƙuri Nurses ba za'a kuma maimaita kuskuren ba".
Sai da na lallaɓata kana tayi shiru, domin idan aka kaiwa Dr gulma zai iya zamar mana matsala ace mun zo kan patient muna ɗaga murya kamar bamu san ya nurse ya kamata yayi ba idan irin hakan ta taso, balle su da suke ganin kuɗi suka biya maƙudai ba kamar asibitin gwamnati ba. Barinta nayi tana musu bayanin jinin da Dr yace za'a saka mata. Ni kuma office ɗin Dr na shiga na basa file ɗin mara lafiyar tare da masa bayanin yanda tace min tana ji a jikinta, yay rubuce rubucen da zai yi da sake rubuta magunguna a ciki yace ga drugs ɗin da za su ƙara siya, sannan ya faɗawa Badiyya ta sanar musu da batun ƙarin jini leda ɗaya da za'a yi mata.
Ina fitowa daga office ɗin sai ga Badiyya ta ƙaraso, ta dafa kafaɗana muka nufi recieption tana ce min.
"Ke naji wata cikin ƴan uwan marasa lafiyar can na ƙusƙus akanki, saura kaɗan na daki bakinta to sai naji maganar da take yi kamar ta sanki, kar naje ko ƴar uwarku ce in abin kunya".
Murmushi nayi da sautinsa ya fita sosai, ba sai na tsaya tambayarta wacce a cikinsu ba balle ta tsaya min dogon bayani, tuni na rigada na san wadda take nufi, ni kaina nayi mamakin yacca nayi fuska na É—auke kai, wanda na san kuma hakan dole yaywa wanda ya san ka sanshi ciwo, nuna tamkar ban ganta ba da nuna tamkar ban santa ba dole zai sanya ta magantu, ba kuma nuna ko in kulawar ganinta ba ne zai daketa illa yanda ta ganni, dole tayi mamaki kuma dole ta girgiza.
Muka gama abinda zamu yi a phermacy don mun É—an jima tsaye da su Manager muna magana, a hakan ma banda na zame Badiyya da surutu ba tahowa zata yi mu tafi ba. Can É—akin mara lafiyar muka koma, ina kallonsu É—aya bayan É—aya na ce,"To cikin ku wa zanyi wa bayani?".
Suka yi min nuni da Dattijuwar ɗazu, nace,"Mama ga wannan total amount ɗin drugs ɗin da Dr ya sake rubutawa ne, ayi payment yanzu sai kuje can pharmacy already an haɗa magungunan karɓowa kawai zaku yi, amma don Allah Mama kar ayi wasa ƙarfe shida na yamma za'a dinga bata".
Ta amsa da to. Ni kuma na ƙarasa gaban gadon domin ƙara yi mata allurar da Dr ya sake bayarwa, ina cikin mata ne wadda tun ɗazu ƙwayar idonta tamkar zata faɗo ƙasa don kallona tace,"Ni kuwa kamar na san fuskar nan".
Nayi kamar ban jita ba har na gama aikina, har sai da zan fita ne ta sake maimaitawa tana tasowa da sauri ta dafa shoulder ɗina. Na waigo na mata kallon sama da ƙasa sai duk ta dabarbace, irin kallon da na watsa mata yasa ta ɗauke hannun nata da cewa,"Am so Sorry".
Na ce,"Lafiya?".
Ta ce,"Ce nayi kamar na sanki, ko ba Sa'ida ba ce?".
Na kalleta kamar ba zanyi magana ba sai kuma nace,"Ehh sunana Nurse Sa'ida".
Ta kaÉ—a kai,"Haba nifa in ce, Sa'ida tsohuwar matar Nazifi ko?".
Na ɗaga gira da ke nuni na tooo ina kallonta tare da girgiza kai nace,"Anya kuwa? Ƙila na miki kama ne da wadda kike magana".
Baki ta saki da al'ajabin da ya bayyana muraran a fuskarta ta sake cewa,"Tsohuwar matar Nazifi fa me kalwa na ke magana, ke ba ki gane ni ba ne?".