← Book details Ƙayar Ruwa 2&3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 81 OF 113

Sashe 81

Ƙayar Ruwa 2&3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Kwanciya nayi akan kujerar sanyi Ac na dukana ta ko'ina, sai kuma na tashi, da yake akwai wani switch na ƙararrawa shi ake dannawa ya isar da zuwan baƙo, naje nayi ta dannawa don ba zai wuce tana can tana aikin baccin da bata gajiya da shi ba, ƴan aikin nata ma inaga basa nan.
Sanin cewar mijinta bai gari na zaƙe kamar gidana, ban da shamaki da ko'ina a gidan Safiyya, kai tsaye na wuce kitchen ɗinta sai miƙa na ke, na duba babu abinci sai na buɗe firij na ɗauko maltina, sai da na kusa shanyewa na sauke robar, sannan ne na ɗanji dama dama na fito ina faɗin Allah ka rabamu da ƙishiryawa da yunwa.

Da yake gaskiya abinci ba ya yankewa a gidan, in babu a kitchen to akwai a dining, saboda haka na nufi rumfar da dining table yake. Ina zuwa naja kujera zan zauna, a wani mugun tsorace naja da baya ganin mutum zaune kamar aljani, ina aikin zare idanu na ke kallon ko'ina musamman ma shi ɗin da na ke ganin kamar gizau, ƙaramar riga ce ta kaki a jikinsa kansa babu hula.
Ko motsi bai yi ba abincinsa kawai yake ci hankali kwance kamar ma bai ji alamun mutum ba, duk sai na rikice naji kamar na saka ihu.

Haka na daskare a tsaye kamar wata soja, na kasa gaba na kasa baya, idona a rumtse ina jin kamar nayi kuka, takaicina ɗaya yanda na ke, kai babu ɗankwali na saki gashi, ga rigar jikina ta kamani daga sama, dogon wuya duk a waje. Bugun zuciyata ya ƙaru, mintinan da ba su fi biyu ba suka wuce, na buɗe ido a tsammanina ya tashi ya bar wajen sai naga har yanzu yana nan, ya gama cin abinci ya ture plate ɗin gefe, ya kwantar da bayansa jikin kujerar yana shafa waya, na saci kallonsa naga taunar cingom ɗinsa kawai yake alamun bai da wata matsala, babu ko tunanin ya kamata ya tashi ya bar wajen.

Nayi guntun tsaki a ƙasan raina ina cewa ƙabila ma dai sam ba su da kunya, ni na kasa barin wajen saboda yacca na ke amma shi bai da hankalin ya tashi ya bar min wajen tunda ya san ni ba muharramarsa ba ce, na ƙara jan tsaki wanda na san yaji don sai da naji saukar ido akaina.
Na ɗaga ƙafa a hankali cikin jin kunyar kaina sai naji muryan Safiyya na cewa,"Me ya kawo aljana gidana? Me aka zo yi min? Saukar ƙur'ani ake min duk sati don haka aniya bil aniya tub tub, azo ayi waje bana neman ku".

Kamar in je in hamɓareta saboda takaici, na ɗaga ido ina kallon inda take tsaye na ce,"Dilla Malama ni miƙo min hulana da rigana".

Maimakon ta ɗauko tukunna ta taho wai sai da ta zo ta gama ƙare min kallo tana cewa ta ina na ke jiyo maganar jinnu, muka haɗa ido ta wani yatsine fuska irin nata na wulaƙanci kana ta dube shi tana masa magana cikin yare. Bai bata amsa ba ko da ido ya amsa mata oho ni ba kallon inda yake na ke ba, sai ta juya ta koma, sai da ta shafe kyawawan mintuna kana ta jefo min hular tana faɗin,"Kuma ban girka da mutum ba".

Na sunkuya na ɗauka hulan na saka, kamar zan bar wajen sai naji har ga Allah ba zan iya ba, ko bai kallona ji zan yi kamar ni ɗin yake kallo, yanzu sai in tafi na juya masa baya mazaunai na rawa? Inaa ba zan iya ba, kawai sai na dake naja kujerar nayi zamana, na kai hannu na janyo flask na zuba abincin, da ƙyar na ke iya kai spoon ɗin baki ina tauna kamar ba zan ba saboda duk na tsargu, gani na ke kawai kallona yake yi.

Dalilin haka sai na haɗe girar sama da ƙasa ina harare harare da murguɗa baki, karaf idona ya kai kan hannunsa ya fito da shi daga cikin aljihu ya aje bindiga a gabansa, gabana ya yanke ya faɗi, tuni na jefar da spoon ɗin ƙirjina sai bugawa yake yi, lokaci ɗaya zufa ta wanke min fuska, na kasa ɗauke ƙwayar idona akan bindigar, ba komai na ke haskowa ba sai lokacin da ƴan sanda suka ɗora min ita a goshi suna cewa na faɗa musu me na bawa Noor tasha ta mutu.

Hawaye ya sakko min zirrr, na É—ago kai na sauke kallona akansa, sai naga shima ni É—in yake kallo kuma haÉ—a idon da muka yi sai kawai ya É—auke nasa ya basar irin ma bai san da ni a wajen ba.
[2/2, 07:48] Hlm: *B3ƘR08FT5*
Na aje wayar saman fuskata ina faman fitar da murmushi kamar sauna, sai daga bisani kuma naji raina ya ɓaci na kama jin haushin kaina, sai kace wata shashasha ma a soyayyar, ina neman zaƙewa daga ance ana sona sau ɗaya, to shi dama haka ma yake no text no call? Soyayyar ce bai iya ba ko kuma salon tasa kulawar kenan? Ko kuma ya gamata akan matarsa ta farko? Rashin nemana da bai yi ba fa tun zuwan farkonsa ya bani haushi sosai, don har ce nayi yana da girman kai, yana nufin kenan ma ba zan ja ajina ba tunda ni ba budurwa ba ce, sai yanzu da wani karkataccen bakinsa zai kira ni yana Baby, a'a Bebo.

To ni ina son miji me raha da zamu zama abokai bana son me ɗagawa, in ma zai sauke abinda ke kansa ya sauke, idan ba zai sauke ba yaje can ya nemi ƴar uwarsa ƙabila ko wadda zata iya da halinsa, Numbernsa na ƙara kalla da kyau don ko ya kira ba zan ƙara ɗagawa ba ehe, kar yaga ya kira ina ta wani zumuɗi ya zaci sonsa na ke yi.
Ummani tace,"To ke ya kike ganin za'ai da waɗannan kuɗin? Dukka lefen miliyan ɗaya da rabi za'a haɗa miki? Ni fa kawai nayi shiru ne gudun faɗan Abbaanku, shi yana batun gwara ayi miki kaya na gani na faɗa kar su ce sun bada kuɗi masu yawa an riƙe. amma ai kuɗin ne sun yi yawa, a dai haɗa ko na miliyan guda ne, ke ni miliyan ɗin ma a wajena tayi yawa wanne sutturu za'a siya har na miliyan, ba gwara a raba biyu sauran a haɗa da wancan a bawa Sale kafinta yay miki kaya masu kyau".

"Kawai ma da zai dawo ya karɓi kuɗinsa da yafi". Na faɗa cikin muryar da ke shaida faɗa faɗa, ina ta gungunin masifa na ƙorafin yanda ma ya raina ni.
Ta ce,"Uhmmm daga baya kenan, ni bana son gulma".

Sai na sami kaina da ɗagowa in kalleta, na buɗi ba ki nace,"To Ummani sai ka kama auren wanda bai san kulawa ba balle haƙƙinta, kuma ba zai ke nuna maka da gaske yana sonka ba saboda yana ji da kansa". Harar da ta galla min yasa na sauke kai ƙasa ina ci gaba da masifata ƙasa ƙasa.
Lokacin Maman Yasmin ta shigo tana tsokana na da,"Amarsu".

Gaisheta kawai nayi ban ko ɗaga kai ba, Ummani tace,"Ƙyaleta". Suka shiga gaisawa Maman Yasmin ɗin na cewa,"Abban Yasmin yace min kina nema mana".

Ummani tace,"Ehh dama ce nayi ke da Nafisa ku zo ku shiga kasuwa ku haÉ—o kayan lefen nan, kunga wata guda kamar yau ne gwara ayi abu a tsanaki, gata nan ita É—in kuma idan zata biku to".

Maman Yasmin tace da Ummani,"Tom shikenan, amma kinga ko za'a yiwa Mrs Arab magana a faɗa mata ga na iya adadin kuɗin da ake so ta haɗa, mu bar mata zaɓi nan da kwana uku za kiga ta haɗo su har akwatuna, kuma wallahi tayi masifar sanin makamar iya haɗa lefe, mayan bikin nan da ake duk ita ake bawa kwangila".

Ummani tace,"To idan kin san dai babu wata matsala ai sai ayi mata maganar ko".

"To shikenan bari a kirata ma yanzu, ke Sa'ida rubuta lambar wayata babu kuÉ—i, ai shegun kaya zata haÉ—a miki, da muka je bikin Surayya duk shegun less É—in da kika ga tana sakawa ai ita ta haÉ—a lefen".

A ƙasan raina na ce ehh fa shigar Amaryar tayi kyau babu ƙarya. Na ɗau wayata ina,"Karanto lambar". "Oak, 07037599677". Ina gama dialling nayi saving da Mrs Arab Kano.
Kiran lambar ya tafi na miƙa mata ina tashi na fita, ruwan wanka na ɗora kana na koma ɗaki na ɗakko wani ɗinki da zan ƙarasa haɗawa, masu shi na ta kirana na gagara ƙarasa musu.

Ƙarfe uku na fito a shirye don tafiya wurin aiki, tun uku saura na ke ta ganin kiran Salim na shigowa nayi biris naƙi ɗagawa, har aikowa yayi nayi saurin kora ɗan aiken kar ma Ummani taji. Na shiga ɗaki na yiwa Ummani sallama bayan ta min adu'a na fito, da zuwana soro kiran Maman Khairi ya shigo tana tambayana su siya min jugs ɗin tangaran yafi yawa ko kuwa? Nace ni na bar musu zaɓi kawai, tun ɗazu ta zo suka fita ita da Maman Yasmin yo siyayyan kayan kitchen lefen kuma kamar yadda ta faɗa ne sun gama magana da Mrs Arab zata haɗo komai ta kawo, ina jin Maman Yasmin na faɗin don Allah ta haɗa akwatu set uku, ni dai kam mun yi dacen sirikai don Matan Yayyuna kamar ciki guda muka fito, yanda Ummani ke yabon su haka suma suke yabonta ko ina suka shiga sai sun ce su kuwa babu abinda zasu ce da Allah sai godiya domin ya basu suruka ta ƙwarai wadda ta ɗauke su babu banbanci da abinda ta haifa, kuma babu takurawa sam a al'amuranta, to nima dai bana kukan rashin Yayyu mata don sun maye min gurbinsu, sai dai nayi kukan rashin ƙanne mata kawai.
Chapter 81 · 0% Book details